Shiri domin gamuwa da Allah (3)
Kwanaki kadan da suka gabata, mun soma bincike a kan yadda za mu zama a shirye yayin da muke jiran lokacin da za mu gamu da Shi Mahaliccinmu wata rana. Na lura mutane da yawa suna ganin kamar akwai sauran lokaci gare su, suna ganin kamar ba da gaske ne wannan duniya za ta kare […]
Kwanaki kadan da suka gabata, mun soma bincike a kan yadda za mu zama a shirye yayin da muke jiran lokacin da za mu gamu da Shi Mahaliccinmu wata rana. Na lura mutane da yawa suna ganin kamar akwai sauran lokaci gare su, suna ganin kamar ba da gaske ne wannan duniya za ta kare ba; wannan abin tsoro ne kwarai da gaske, bari in sake nanatawa cewa wannan duniya; ba za ta dauwama ba za ta shude. Babu wani mutum da zai dauwama cikin wannan duniya, rana tana zuwa wadda ko ka so ko ka ki dole za ka fuskanci Allah Mahaliccin kowa da komai. A wancan lokacin kuwa babu boye-boye ko kadan. Za ka bayyana a gaban Ubangiji Allah; kai da kanka za ka ba da lissafin kanka a gaban Kursiyyin Shari’ar Allah. Ba za ka iya guje wa fuskar Ubangiji ba, wannan ne dalilin da ya kamata ka yi tunani a kan irin shirin da kake yi domin gamuwa da Allah. A cikin koyarwarmu ta karshe, na ce, idan Allah Ya yarda, za mu yi koyarwa daga inda muka karanta, bari mu sake karanta su da wasu wurare daga cikin Littafi Mai tsarki. A cikin Littafin Ruya ta Yohanna sura ashirin, aya goma sha daya zuwa goma sha biyar (20: 11-15), maganr Allah na cewa; “Na ga kuma babban farin Kursiyyi, da wanda ke zaune a bisansa, wanda duniya da sama suka guje ma fuskatasa; ba a kuwa samu masu wuri ba. Na ga matattu kuma, kanana da manya, suna tsaye a gaban Kursiyyin, aka bude littattafai: aka bude wani littafi kuma, littafin rai ke nan: aka yi ma matattu shari’a kuma bisa ga abin da aka rubuta cikin littattafai, gwargwadon ayyukansu. Teku kuma ya ba da matattun da ke cikinsa, mutuwa da hades kuma suka ba da matattun da suke cikinsu, aka yi musu shari’a kuma, kowane mutum gwargwadon ayyukansa. Kuma aka jefar da mutuwa da Hades cikin korama ta wuta. Mutuwa ta biyu ke nan, wato korama ta wuta. Kuma wanda aka iske ba a rubuta shi cikin littafin rai ba, aka jefar da shi cikin korama korama ta wuta.”
Bari mu dubi wani wuri kuma kafin mu soma yin nazari, a cikin Littafin Mai Wa’azi (12 :14), maganar Allah na cewa “Gama Allah za ya kawo kowane aiki cikin shari’a, da dukan asirin rai, domin Ya raba, ko nagari ko mugu.”
Bayyana a gaban Kursiyyin Shari’ar Allah ba sai ka zaba ba ne, a’a dole ne za ka samu kanka a wurin. Hanyar zuwa wurin kuwa ita ce: ko mutuwa, ko kuwa lokacin da Allah Ya ga cewa yanzu ya kamata in shar’anta wannan duniya, wato duniya ta kare ke nan. Allah da kanSa za ka fuskance Shi Wanda Ya san dukan irin rayuwar da ka yi yayin da kake duniya. Mu lura fa; Allah cikin alherinSa Ya ba mu alamun karshen wannan zamani domin mu zama a fadake, kada ranar zuwansa ta zo babu shiri, mu sake duba Littafin Matta 24 : 1 – 14; maganar Allah na cewa, “Yesu ya fita haikali, yana cikin tafiya, sai almajiransa suka zo wurinsa domin su gwada masa gine-gine na haikali. Amma ya amsa ya ce musu, ba ku ga wannan abu duka ba? Hakika ina ce muku, ba za a rage wani dutse bisa wani ba, da ba za a rushe ba. Yana nan yana zaune bisa dutsen Zaitun, sai almajiran suka zo wurinsa waje daya, suka ce, ka fada mana yaushe wadannan abubuwa za su faru, mene ne kuma alamar zuwanka da cikar zamani? Yesu ya amsa, ya ce, ku yi lura kada kowa ya bashe ku. Gama mutane da yawa za su zo cikin sunana, su ce, Ni Kiristi ne, za su kuwa badda mutane da yawa. Kuma za ku ji labarin yakukuwa da zizar yaki! Ku yi lura kada hankalinku ya tashi, gama wadannan al’amura dole za su faru, amma matuka ba ta yi ba tukunna. Gama al’umma za ta tasa wa al’umma, mulki kuma zai tasa wa mulki: za a yi yunwa da raye-rayen duniya wurare daban- daban. Amma dukkan wadannan al’amura mafarin wahala ne. Sa’an nan za a mika ku ga kunci, za su kashe kuma: za ku zama abin ki ga dukkan al’ummomi saboda sunana. Sa’annan mutane da yawa za su yi tuntube, za su ba da juna, za su ki juna kuma, kuma masu karyar annabci da yawa za su tashi, su bad da mutane da yawa. Saboda yawaita da mugunta za ta yi kuma, kaunar yawancin mutane za ta yi sanyi. Amma wanda ya jure har matuka, shi zai tsira. Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukkan al’ummomi; sa’annan matuka za ta zo.”
Sai mu lura sosai da abin da Yesu Kiristi ya ce, a cikin dukkan abin ya ce, abu daya ne kawai ya saura, wato wa’azin wannan Bishara ga dukan al’umma, kuma ba mu san lokacin da mutum zai ji wannan bisharar ba. Idan maganar yaki ne ya zama kamar ruwan dare gama duniya. Idan maganar annabawan karya a wannan zamani kuwa, ba abin nema ba ne ko kadan, suna nan da yawa, suna kiran kansu Annabi wane da Annabi wane. Ba su san Yesu Kiristi ba kodayake suna yin wa’azi da sauran ayyukan al’ajabi. Idan kuwa kisan masu bin Yesu Kiristi ne, wannan shi ma ba bakon abu ba ne ko kadan; kauna ta riga ta zama da sanyi sosai, yau kowa ta kansa yake yi. Shin mene ne ya sa har yanzu ba mu kula da cewa lokacin dawowarsa ta yi kusa ba?
’Yan uwana, sai mu yi hankali da yadda muke rayuwa a yau, domin a ranar da za ka tsaya a gaban Allah, duk yadda ka yi rayuwa, zai zamo a fili. Mutane da yawa za su sha kunya domin sun yi tsammanin sun yi shi a boye babu wanda ya sani; amma idan da kunya ne kawai babu damuwa ko kadan domin za ka iya share fuska kawai ka ci gaba da rayuwarka; wannan bayan ka sha kunya, hakan nan rabonka shi ne korama ta wuta. Mutuwa ta biyu ke nan. Allah zai bude littattafai inda aka rubuta dukkan abin da ka yi; ko nagari ko mugu, a wancan lokaci ne kowane asiri zai tonu. Wace irin rayuwa kake yi yanzu? Wadda za ta gamshi Allah ne ko kuwa? Mene ne ka iya yi a boye kana gani kamar babu wanda ya sani? Ka sani fa Allah Yana gani kuma zai shar’anta ka.
Abu mafi tsoro shi ne Littafi na biyu wanda maganar Allah ta ambata a cikin aya ta goma sha biyu cikin Ruya ta Yohanna sura ashirin; wadda tana cewa, “Na ga matattu kuma, kanana da manya suna tsaye a gaban Kursiyyin, aka bude littattafai: aka bude wani littafi kuma, littafin rai ke nan…… (19) kuma wanda aka iske ba a rubuta shi cikin littafin rai ba, aka jefar da shi cikin korama ta wuta.” Tambaya mai muhimmanci a nan ita ce; ko sunanka ya samu shiga cikin wannan littafi na rai? Idan sunanka ba rubuce yake cikin wannan littafi ba, rayuwarka ta zama abin tausayi sosai abin kaito kuma. Akwai zarafi har yanzu idan kana son sunanka ya samu shiga cikin littafin rai. Za mu ga abin da ya kamata ka yi har sunanka ya samu shiga. Ubangiji Allah Ya taimake mu.
Mu ci gaba da addu’a domin kasarmu da shugabanninmu; Allah kuma Ya ba mu zaman lafiya.