Shiri don gamuwa da Allah (12)
Jama’ar Ubangiji Allah barkanmu da warhaka, barkanmu kuma da sake saduwa cikin binciken da muke yi tare a kan Shiri domin Gamuwa da Allah- a yau muna kashi na goma sha biyu daidai. Idan mun tuna mun tsaya ne a inda muka yi karatu daga cikin Littafin Yohanna 3: 17 – 21 inda yake cewa […]
Jama’ar Ubangiji Allah barkanmu da warhaka, barkanmu kuma da sake saduwa cikin binciken da muke yi tare a kan Shiri domin Gamuwa da Allah- a yau muna kashi na goma sha biyu daidai. Idan mun tuna mun tsaya ne a inda muka yi karatu daga cikin Littafin Yohanna 3: 17 – 21 inda yake cewa “Gama Allah Ya aiko dan cikin duniya ba domin ya yi wa duniya shari’a ba, amma domin duniya ta tsira ta wurinsa. Wanda yana ba da gaskiya gare shi ba a yi masa shari’a ba, wanda ba ya ba da gaskiya ba, an riga an yi masa shari’a, domin ba ya ba da gaskiya ga sunan da haifaffe kadai na Allah ba. Shari’a fa ke nan, haske ya zo cikin duniya; amma mutane suka fi son duhu da haske; domin ayyukansu miyagu ne. Gama ko wane ne wanda yake aikata mugunta; kin haske yake yi, kuma ba shi zuwa wurin haske; domin kada ayyukansa su tonu. Amma wanda yake aikin gaskiya yana zuwa wurin haske, domin a bayyana ayyukansa, a cikin Allah an yi su.”
Za mu ci gaba ne da duban abin da ya sa dukkan wanda bai dauki Yesu Kiristi a matsayin mai ceto ba yana karkashin la’ana wadda babu mai taimakonsa a lokacin da zai fuskanci Ubangiji Allah a Ranar karshe. Wani irin hadari ne yake kan mutumuin da ya sa Allah da kansa ya yi hanya domin mutum ya samu tsira? Amsar daya ce kawai ZUNUBI! Zunubi yana da hadari sosai a kan dan Adam. Maganar Allah ta ce mana ‘ hakkin zunubi mutuwa ne….’ Ba nufin Ubangiji Allah ba ne ya ga cewa mutum ya mutu cikin zunubi, ainihin mutuwa ba kawai rabuwar ruhin mutum da gangar jikinsa ba ne, eh, lallai ita ma mutuwa ce, amma akwai mutuwa ta biyu wadda ta shafi dukkan wanda bai karbi Yesu Kiristi a matsayin mai cetonsa ba; wannan irin mutuwa ita ta fi muni – domin irin wadannan sun rabu da Allah ke nan har abada; wannan abin tsoro ne sosai; mu sani fa wuta wanda Allah Ya shirya; bai shirya ta domin mutum ba tun daga farko; mutum ya kawo kansa ne ciki lokacin da ya ki bin umurnin Allah; ya zabi ya yi biyayya ga ra’ayin da Shaidan ya shuka a cikin zuciyarsa, daga lokacin ne mutum ya zabi ya tafi tare da Iblis ko Shaidan cikin korama ta wuta, ko wutar Jahannama. Idan har mutum ya yarda ya kai wajen kuwa; sai ya sani; sai ta sani cewa babu tuba a wurin, babu mutuwa, abin da kawai akwai shi ne wahala da kuka da kunar wuta irin ta Jahannama, babu ruwa can, kuma haka za ka kasance har abada, ba za ka iya kidaya shekarun da za ka yi a wajen ba, bayan ka yi shekara biliyan sau biliyan sai a ce yanzu ne ka soma; ’yan uwana maza da mata, wannan ba tatsuniya ba ce, wannan tabbas ne zai faru, wannan alkawarin Allah ne. Dalilin da Yesu Kiristi ya shigo duniya ke nan – ya bude wa mutum wanda Allah da kanSa Ya halitta, hanya ta tsira ko kubuta daga wannan mutuwa ta biyu. Mutane da yawa sun yi watsi da wannan shiri na Allah; amma lokaci na zuwa da za su yi da-na- sani, kada ka yarda ka kai wancan lokaci na da-na-sani. Akwai mutane da dama da suka san gaskiyar nan; amma tsoron idanun mutane ya hana su karbar Yesu Kiristi a matsayin mai cetonsu kuma ubangijinsu; sai mu tuna cewa, a ranar da za mu gamu da Allah a gaban Kursiyyin Shari’arsa, daidai ne za mu bayyana; ba mutum da abokinsa ko mutum da dansa ba, kowa ta kansa zai yi, kai kadai za ka ba da lissafin kanka da kuma dukkan abin da ka aikata yayin da kake raye a cikin wannan duniya. Sai ka yi tunani. Hanyar tsira daya ce kawai kamar yadda Littafi Mai tsarki ke koya mana – Yesu ya ce masa, “Ni ne HANYA, Ni ne GASKIYA; Ni ne RAI; ba mai zuwa wurin Uban sai ta wurina.” (Yohanna 14 : 6)
Idan har da gaske mutum yana so ya sadu da Allah cikin salama, babu wata hanya kuma wadda zai samu biyan bukata fiye da shiriya tsakaninka da Allah ta wurin ba da gaskiya ga Yesu Kiristi ubangijinmu.
A cikin aya 18 ta Yohanna sura uku, maganar Allah ta ce “Wanda yana ba da gaskiya gare shi ba a yi masa shari’a ba, wanda ba ya ba da gaskiya ba, an rigaya an yi masa shari’a, domin ba ya ba da gaskiya ga sunan da haifaffe na Allah ba.” Shari’ar nan ita ce rabuwa da Allah na har abada domin zunubi; wannan hukuncin Allah ne, babu wani alkalin da zai iya tsayawa a madadinka. Mutum ba ya da hujja kuma a gaban Allah domin shi Allah, Ya rigaya Ya sanar da mu game da abin da zai faru da kowane mutum wanda ba ya ba da gaskiya ga sunan da haifaffe na Allah. Zabi ya rage ne a gare ka ko a gare ki.
A kowane lokaci idan maganar Allah ta yi magana a kan haske da kuma duhu, sai mu sani cewa HASKE -Tsarki ne cikin rayuwa, adalci ne cikin dukkan abin da muke yi wanda a bayyane suke a fuskar jama’a, babu boye-boye ko kadan, DUHU kuwa, yana nufin zunubi, ayyukan mugunta, mutane ba sa yin su a fili yawancin lokaci; da dama ba su son wasu ma su sani domin suna ganin kamar za su sha kunya a gaban wadanda suka san su. Akwai mutane da yawa da za ka yi tsammani mutanen kirki ne amma a boye cike suke da mugunta har irin ta kin karawa. Bari mu ga irin wadannan mutane da ayyukansu:- A cikin Littafin Ruya ta Yohanna 21 : 8. Maganar Allah tana cewa “Amma ga matsorata da marasa ban gaskiya da masu kazanta da masu kisan kai da fasikai da masu sihiri da masu bautan gumaka, da dukan makaryata; rabonsu yana cikin korama mai konewa da wuta da kibiritu; mutuwa ta biyu ke nan.” Haka nan a cikin Littafin Galatiyawa 5:19-21; maganar Allah na fadakar da mu a kan irin wannan; “Ayyukan jiki fa a bayyane suke, fasikanci ke nan, kazanta, lalata, bautar gumaka, sihiri, magabtaka, husuma, kashe-kashe, hasala, tsattsaguwa, rabuwa, hamiyya, hassada, maye, nishadai da irin wadannan; ina kuwa fadakar da ku, kamar yadda na rigaya na fadakar da ku, su wadanda ke aikata wadannan al’amurra, ba za su gaji mulkin Allah ba.”
Ina so ka binciki kanka, ina son ke ma ki binciki kanki, wace irin tafiya ce muke yi a gaban Allah? Ka binciki zuciyarka ka kuma gaya wa kanka gaskiya – shin wane ne Yesu Kiristi a gare ka? Wane ne Yesu Kiristi a gare ki? Idan har ba shi ba ne ubangiji da mai cetonka ba; idan ba shi ba ne ubangiji da mai cetonki ba, gaskiya kana cikin hadari mai tsanani, hakan nan ke ma kina cikin hadari mai tsanani. Allah cikin alherinSa Ya ba ka zarafi yau, Ya ba ki zabi a yau domin ka sami ceto; kada ka yi watsi da wannan kyakkyawan zarafi. Sai mu tuna, ba mu san yaushe ne kwananmu zai kare a wannan duniya ba; zai dace matuka mu shirya tsakaninmu da Allah tun akwai sauran lokaci, yau ne namu; gobe ba namu ba. Ubangiji Allah Ya taimake mu. Amin.