Shiri don gamuwa da Allah (13)
Ina so kowane mai karatu ya gode wa Allah domin alherin Sa zuwa gare mu; alherin Sa ne ya sa muke cikin masu rai a yau. Idan mun duba a hankali; za mu ga cewa akwai mutane da yawa da suka yi niyyar yin abubuwa masu kyau a yau amma da suka kwanta jiya da […]
Ina so kowane mai karatu ya gode wa Allah domin alherin Sa zuwa gare mu; alherin Sa ne ya sa muke cikin masu rai a yau. Idan mun duba a hankali; za mu ga cewa akwai mutane da yawa da suka yi niyyar yin abubuwa masu kyau a yau amma da suka kwanta jiya da dare, ba su farka ba daga barcin, sai kawai suka iske kansu a gaban Allah wanda Ya haliche su. Kai Allah Ya sa ka tashi daga barci lafiya kana kan kafafunka, babu damuwa ko kadan. Bari in tambaye ka, nawa ne ka ba Ubangiji Allah domin Ya bar ka da rai a yau? Babu abin da mutum zai iya baAllah domin Ya bar shi ya ci gaba da rayuwa; alherinSa ne kawai muke mora.
A cikin koyarwarmu na makon jiya, mun soma magana ne a kan wadanda ba su san Yesu Kiristi a matsayin mai cetonsu ba. Wane irin shiri ne ya kamata su yi? Ubangiji Allah bai bar mu a cikin duhu ba ko kadan, zunubi yakan kawo hallaka ga kowane mutum. Wannan kuwa ba abin wasa ba ne. Shi mutum na farko bai yi tsammani zai rabu da ganin Allah ba idan ya ci daga itacen da Allah Ya hane shi cewa kada ya ci daga ciki; da ya kuskura ya dauka ya ci kuwa, idanunsa da na matarsa suka budu, suka ga cewa sun zama tsirara, su da kansu suka guje wa fuskar Allah suka buya cikin itatuwa, ba sa son Ubangiji Allah Ya gansu – zunubi ke nan, yakan sa mutum ya guji fuskar Allah.
Kyakkyawan shiri ga mutanen da ba su riga sun karbi kyautar nan da Allah da kanSa Ya bayar domin dukkan duniya ta samu tsira ba; ita ce karbar Yesu Kiristi a cikin zuciyarsu ta wurin ban gaskiya. Muddin mutum bai yi imani da Yesu Kiristi a matsayin mai cetonsa ba, ba shi da rabo cikin mulkin sama. Wani babban malami mai suna Nikodimu, ya zo wurin Yesu Kiristi a wani dare domin su tattauna da shi, bari mu ga abin da ya faru tsakaninsu su biyun: A cikin Littafin Yohanna 3:1-15, maganar Allah tana cewa: “Wani mutum yana nan na wajen Farisawa, sunansa Nikodimu, wani basaraucen Yahudawa, wannan ya zo wurinsa da dare, ya ce masa, Rabbi, mun sani malami ne kai daga wurin Allah ka zo, gama ba mai yin wadannan alamun da kake yi, sai ko Allah Yana tare da shi.Yesu ya amsa, ya ce masa: “Hakika, hakika ina ce maka, in ba a haifi mutum daga bisa ba, ba ya da ikon shiga mulkin Allah.” Nikodimu ya ce masa: “Yaya zai yiwu a haifi mutum sa’adda ya rigaya ya tsufa? Ya iya sake shiga a cikin cikin uwatasa a haife shi kuma? Yesu ya amsa ya ce: “Hakika, hakika, ina ce maka, in ba a haifi mutum daga cikin ruwa da ruhu kuma ba, ba ya da ikon ya shiga cikin mulkin Allah. Abin da aka haifa daga nama, nama ne, abin da an haifa daga cikin ruhu, ruhu ne, kada ka yi mamaki da na ce maka, dole a haife ku daga bisa. Iska takan hura wajen da take nufa, kana jin motsinta kuma, amma ba ka san wajen da take fitowa da inda za ta ba, haka nan ne dukkan wanda aka haife shi daga cikin ruhu. Nikodimu ya amsa, ya ce masa, wadannan abubuwa yaya za su yiwu? Yesu ya amsa: “Ya ce masa, kai mai koya wa Isra’ila ne, ba ka fahimci wadannan abubuwa ba? Hakika, hakika ina ce maka, muna fadin abin da muka sani, muna shaida abin da muka gani, ba ku karbi shaidarmu ba. idan na fada muku zancen duniya, ba ku gaskanta ba, yaya za ku gaskanta idan na fada muku zancen sama? Kuma ba wanda ya taba hawa zuwa cikin sama, sai shi wanda ya sauko daga cikin sama, wato dan mutum wanda ke cikin sama. Kuma kamar yadda Musa ya tada maciji bisa cikin daji, haka nan kuma dole za a tada dan mutum bisa; domin dukkan wanda yana ba da gaskiya ya samu rai na har abada.”
Shirin da yake da muhimmanci shi ne daidaita tsakanin mutum da Allah. Hanyar yin wannan kuwa daya ce kawai. Ubnagiji Yesu Kristi ya ce a cikin maganarsa a Littafin Yohanna 14:6, “Yesu ya ce masa: Ni ne hanya, Ni ne gaskiya, Ni ne rai, ba mai zuwa wurin Uban sai ta wurina.” Yesu Kiristi ya ce “Ni ne hanya.” Sulhu tsakanin mutum da Allah ba zai taba aukuwa ba sai ta wurin gicciyen Yesu Kiristi kadai. Idan muka ba da gaskiya ga abin da Allah da kanSa Ya shirya, za mu samu wannan rai na har abada. Idan kuwa muka yi watsi da wannan shiri na Allah domin cetonmu, gaskiyar ita ce akwai lokacin da za ka ce DA-NA-SANI. Ba na so ka kai wancan lokaci, wuta wadda Allah ya shirya ba dominka ba ne amma domin Shaidan ne da dukkan masu binsa, musammam dukkan aljanu da suke tare da tun daga farko; wato mala’ikun nan na Allah wadanda suka bijire. Abu daya ne kawai zai hana mutum shiga cikin wannan wuta mai kuna ta har abada – wannan kuwa shi ne, barin Yesu Kiristi ya shigo cikin zuciyarmu ta wurin ban gaskiya ba ayyuka ba; domin babu wani abin kirki da mutum zai iya ya yi wanda zai ba shi wuri a cikin mulkin Allah. akwai babban hadari a kan dukkan wanda bai ba da gaskiya ga Yesu Kiristi; a matsayin Ubangijinsa da mai cetonsa ba.
A cikin Littafin Galatiyawa 5:19 -21 maganar Allah na cewa, “Ayyukan jiki fa a bayyane suke, fasikanci ke nan, kazanta, lalata, bautar gumaka, sihiri, magabtaka, husuma, kashe-kashe, hasala, tsattsaguwa, rabuwa, hamiya, hassada, maye, nishadi da irin wadannan, ina kuwa fadakar da ku, kamar yadda na rigaya na fadakar da ku, wadanda ke aikata wadannan al’amura ba za su gaji mulkin Allah ba.” Haka nan cikin Littafin Ruya ta Yohanna 21:8; maganar Allah na cewa “Amma ga matsorata da masu kazanta da masu kisan kai da fasikai da masu sihiri da masu bautar gumaka da dukkan makaryata, rabon su yana cikin korama mai konewa da wuta da kibiritu, mutuwa ta biyu ke nan. Haka nan a cikin aya goma sha biyar na Ruya ta Yohanna sura ashirin, maganar Allah ta sake cewa: “Kuma wanda aka iske ba a rubuta shi cikin Littafin Rai ba, aka jefar da shi cikin korama ta wuta.” A karshe ina so ne mu san cewa a ranar gobe ba ka da wata hujja ta rashin samun ceto daga cikin zunubi domin ka iya bauta wa Allah da dukkan zuciyarka. Karbar Yesu Kiristi a matsayin mai cetonka ba ta da wahala ko kadan. Romawa 10: 9 – 10 tana cewa: “Gama idan ka shaida da bakinka Yesu Ubangiji ne, ka kuma ba da gaskiya cikin zuciyarka Allah Ya tashe shi daga matattu za ka tsira, gama da zuciya mutum yake ba da gaskiya zuwa adalci da baki kuma ake shaida zuwan ceto.”
Zabi ya rage a gare ka. Maganar Allah ta ce mana: “Gama hakkin zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai na har abada ne cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.” kofar samun ceto a bude take, za ka iya wannan addu’a a cikin dakinka kawai, kuma Allah zai ziyarce ka. Ubangiji Allah Ya taimake mu a cikin alherinSa, amin.