Shirin Allah domin fansar dan Adam
Babi na Goma Sha Hudu: I’itikafi a cikin watan Shawwal:496. An karbo daga Muhammad ya ce: “Muhammad dan Fudail dan Ghazwan ya ba mu labari daga Yahya dan Sa’id daga Amrata ’yar Abdurrahman daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya kasance yana I’itikafi a kowane watan Ramadan, kuma ya […]
Babi na Goma Sha Hudu: I’itikafi a cikin watan Shawwal:
496. An karbo daga Muhammad ya ce: “Muhammad dan Fudail dan Ghazwan ya ba mu labari daga Yahya dan Sa’id daga Amrata ’yar Abdurrahman daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya kasance yana I’itikafi a kowane watan Ramadan, kuma ya zamo idan ya yi Sallar Asuba sai ya koma zuwa ga inda ke zaman I’itikafinsa. Ya ce, “Sai A’isha ta nemi izininsa domin I’itikafi ya yi mata izini, sai ta kafa karamar rumfa (lema). Sai Hafsa ta ji haka ta kafa tata rumfar. Zainab ma ta ji haka sai ta kafa wata rumfar. Lokacin da Manzon Allah (SAW) ya juya daga Sallar Asuba, sai ya ga rumfuna hudu, ya ce, “Mene ne wannan? Sai aka ba shi labarinsu ya ce, “Me ya sanya su aikata haka? Shin biyayya suke nufi? Ku tumbuke su ban son ganinsu, sai aka cire. Bai yi I’itikafin ba cikin Ramadan face ya yi I’itikafin a goma na karshen Shawwal.”
Babi na Goma sha Biyar: Wanda bai ganin wajabcin yin I’itikafi da azumi:
497. An karbo daga Isma’il dan Abdullahi ya ce: “Daga dan uwansa daga Sulaiman daga Ubaidullahi dan Umar daga Nafi’u daga Abdullahi dan Umar daga Umar dan Khaddab (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai shi ya ce, ya Manzon Allah! Hakika ni, na yi alwashin zan yi I’itikafi a Masallacin Harami a (zamanin) Jahiliyya. Sai Annabi (SAW) ya fadi masa cewa: “Ka cika alwashinka, sai ya yi I’itikafi na dare daya.”
Babi na Goma sha Shida: Idan mutum ya yi alwashi a Jahiliyya zai yi I’itikafi, sa’an nan ya musulunta:
498. An karbo daga Ubaid dan Isma’il ya ce: “Abu Usama ya ba mu labari daga Ubaidullahi daga Nafi’u daga dan Umar cewa: “Lallai Umar (Allah Ya yarda da shi) ya yi alwashin zai yi I’itikafi a Masallacin Harami lokacin Jahiliyya, ya ce, ina tsammaninsa ya ce, “Dare daya,” sai Manzon Allah (SAW) ya ce, masa: “Ka cika alwashinka.”
Babi na Goma sha Bakwai: I’itikafi a cikin goma na tsakiyar watan Ramadan:
499. An karbo daga Ubaidulllah dan Abu Shaiba ya ce: “Abubakar ya ba mu labari daga Hafsi daga Abu Hasin daga Abu Salih daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce, “Annabi (SAW) ya kasance yana I’itikafin kwana goma a cikin kowane watan Ramadan. A shekarar da ya rasu sai ya yi I’itikafin yini ashirin.”
Babi na Goma sha Takwas: Wanda ya yi nufin I’itikafi sa’an nan ya bayyana masa ya bari (fita):
500. An karbo daga Muhammad dan Mukatil Abul Hassan ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, A’uza’iy ya ba mu labari, ya ce, “Yahya dan Sa’id ya ba ni labari, ya ce, Amrata ’yar Abdurrahman ta ba ni labari daga A’isha (Allah Ya yarda da ita) cewa: “Hakika Manzon Allah (SAW) ya ambaci zai yi I’itikafi a goma na karshen Ramadan. Sai A’isha ta nemi izininsa ya yi mata izini. Hafsat ita ma ta roki A’isha da ta neman mata izini, ta aikata haka. Lokacin da Zainab ’yar Jahash ta ga haka sai ta umurta da a yi mata tanti (rumfa) na I’itikafi kamar na (su). (A’isha) ta ce, “Manzon Allah (SAW) ya kasance idan ya juya daga Sallar Asuba sai ya koma zuwa ga tantinsa, sai ya ga rumfuna uku ya ce, “Mene ne wannan? Sai suka ce, “Rumfar A’isha ce da Hafsat da Zainab.” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Biyayya suke nufi da aikata haka? To ni ba zan yi I’itikafin ba, sai ya koma gida. Lokacin da ya yi sallar Azumi, sai ya yi I’itikafi a goma ga Shawwal.”