Shirin APPEALS ya horar da manoman citta a Kudancin Kaduna
A kokarin da take yi don kare manoman citta daga yin hasara a Najeriya, Shirin Bunkasa Aikin Gona da Inganta Sarrafa Kayan Gona da ake kira APPEALS ya shirya wa manoman citta da ke Kudancin Kaduna bita kan yadda za su kare kansu daga yin hasara bayan gama duk wahalhalun noma. Bitar wadda aka shirya ta […]
A kokarin da take yi don kare manoman citta daga yin hasara a Najeriya, Shirin Bunkasa Aikin Gona da Inganta Sarrafa Kayan Gona da ake kira APPEALS ya shirya wa manoman citta da ke Kudancin Kaduna bita kan yadda za su kare kansu daga yin hasara bayan gama duk wahalhalun noma.
Bitar wadda aka shirya ta kwana uku an gudanar da ita ce a kananan hukumomin Jama’a da Jaba da Kagarko da ke yankin. Kuma an samu jawabai daga masana daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da kuma gwaje-gwajen na’urorin zamani da ke gyara citta da yankawa da kuma busarwa.
Lokacin da yake gabatar da jawabi, shugaban Shirin APPEALS na Jihar Kaduna Dokta Yahaya Aminu ya bayyana na’urorin a matsayin ci gaban fasaha da kere-keren zamani da za su saukaka wa manoma wasu wahalhalu tare da bunkasa adadin cittar da za a rika samarwa da rage yawan hasarar da manoman kan fuskanta da adadi mai yawan gaske.
Baya ga jan hankalin manoman da ya yi kan mayar da hankali kan horon da suka samu don cin gajiyarsa, Dokta Yahaya ya ce abin takaici ne duk da kasancewar Kudancin Kaduna ne ya fi ko’ina noman citta a Afirka kuma wanda aka yi amanna tana daya daga cikin citta mafi kyau da daraja a duniya amma har yanzu sun gaza samar da abin da duniyar ke bukata saboda rashin bin hanyoyi da dabarun zamani.
Daga karshe ya yi wa manoman albishir kan shirin da Gwamnatin Jihar Kaduna da hadin gwiwar Kamfanin OCP da ke kasar Moroko ke yi don auna irin kasar da kowace karamar hukuma da yanki ke da shi don manoman su rika dubawa don sanin duk irin nau’in sinadaran da kasarsu ke da shi da wadanda suke bukata don tantance nau’i da adadin takin da za su yi amfani da shi a gonakinsu.
Yayin da yake gabatar da mukala, Injiniya Abdulhakeem Lawal daga Jami’ar Ahmadu Bello, da ke Zariya ya bayyana hasarar da ake yi wajen noman citta da ke farowa tun daga girbi har zuwa sauran dawainiyar da ake yi mata. Ya ce hakan ya kan shafi inganci da yawan abin da ake nomawa maimakon bayar da shawarar diban kasar zuwa dakunan gwaje-gwaje da suka yi karanci a Najeriya, kuma hakan ke shafar noma a Najeriya.
Shi kuwa Dokta Musa Jaliya daga Jami’ar ABU, ya yi bayani a kan nau’o’in cututtukan da kan addabi citta tun daga kan nomawa har zuwa lokacin cirewa da kuma yadda za a magance su.
Sannan ya bayyana abubuwa da yawa da manoman za su iya sarrafa cittarsu da shi don amfanin cikin gida domin sayarwa.
Masana daban-daban sun gabatar da kasidu masu matukar amfani kan abin da ya shafi noman citta tun daga kan iri zuwa tazarar da ake bukata a tsakani; yayin shukawa da tazarar kunya zuwa kunya da irin karfin zafi ko sanyin da ake bukata da adadi da irin takin da take so, har zuwa nomewa da wankewa da yankawa da kuma irin magungunan feshin da za a yi amfani da su tun daga shuka har zuwa durawa a cikin buhu don samar da citta mai kyau da inganci da karuwarta a cikin gona.
Mutum goma-goma ne daga kungiyoyin manoma daban-daban da ke kananan hukumomin Kudancin Kaduna suka halarci taron bitar.
Christy Yakubu da Monday Jonah da suka halarci bitar sun bayyana wa Aminiya gamsuwarsu da irin bitar da aka gudanar inda suka sha alwashin inganta noman cittar da kuma tsabtace ta don samun abin da ake bukata.