…Shirin bai wa dalibai abinci zai taimaka wajen bunkasa ilimi – Sale Baba

Sakataren Ilimi na karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna Alhaji Sale Baba Muhammad ya bayyana cewa shirin bai wa daliban makarantun firamare abinci da gwamnatin Jihar Kaduna ta kirkiro zai taimaka wajen bunkasa ilimi a jihar. Alhaji Sale Baba Muhammad ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Saminaka, inda ya […]

…Shirin bai wa dalibai abinci zai taimaka wajen bunkasa ilimi – Sale Baba
…Shirin bai wa dalibai abinci zai taimaka wajen bunkasa ilimi – Sale Baba

Sakataren Ilimi na karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna Alhaji Sale Baba Muhammad ya bayyana cewa shirin bai wa daliban makarantun firamare abinci da gwamnatin Jihar Kaduna ta kirkiro zai taimaka wajen bunkasa ilimi a jihar.
Alhaji Sale Baba Muhammad ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Saminaka, inda ya ce babu shakka idan jama’a suka bai wa shiri goyon baya da hadin kai za a samu babbar nasara.
Ya ce a karamar hukumar Lere shirin yana tafiya kamar yadda aka tsara shi a dukkan makarantun firamaren yankin.
Alhaji Sale Baba ya yi bayanin cewa baya ga daliban da ake bai wa abincin, akwai mutane da dama da suka fara amfana da shirin da suka hada da masu sayar da kayan abinci da masu dafa abincin da masu yi musu aiki da sauransu da dama.
Shugaban kwamitin gudanar da shirin bai wa daliban firamare a binci na karamar Hukumar Lere Alhaji Hassan Malami ya shaida wa wakilinmu cewa akalla sun dauki masu dafa abinci sama da 1500 ne suke cin gajiyar shirin a karamar hukumar.
Ya ce shirin yana tasiri kwarai da gaske domin a yanzu masu dafa abincin da aka dauka sun samu aikin yi.
Ya ce suna gyare-gyare kan ’yan matsalolin da aka samu, don haka ya yi kira ga iyayen yara su bai wa shirin goyan baya da hadin kai ta hanyar tura ’ya’yansu zuwa makaranta a kan lokaci.