Shirin ‘‘BARKA DA HANTSI’’ ya shekara uku Allah Ya maimaita mana

Mai karatu ina bude makalar yau da yi wa juna murnar ganin shigowar sabuwar shekarar Musulunci ta Hijirah 1436, wadda ta fara a Juma’ar da ta gabata wato, wa 1 ga watan Muharram 1436, bayan Hiijirar fiyayyyen halitta Annabi Muhammadu SAW daga Makkah zuwa Madinah. Irin wannan lokaci ba na bukukuwa ba ne, illah dai […]

Shirin ‘‘BARKA DA HANTSI’’ ya shekara uku Allah Ya maimaita mana
Shirin ‘‘BARKA DA HANTSI’’ ya shekara uku Allah Ya maimaita mana

Mai karatu ina bude makalar yau da yi wa juna murnar ganin shigowar sabuwar shekarar Musulunci ta Hijirah 1436, wadda ta fara a Juma’ar da ta gabata wato, wa 1 ga watan Muharram 1436, bayan Hiijirar fiyayyyen halitta Annabi Muhammadu SAW daga Makkah zuwa Madinah. Irin wannan lokaci ba na bukukuwa ba ne, illah dai lokaci ne na yi wa kai hisabi dangane da yin waiwayen shekarar da ta gabata wadanne ayyukan alheri mutum ya aikata, don ya gode wa Allah bisa ga wannan baiwa da kuma duba irin wadanne ayyukan ba daidai ba ya aikata, ya kuma roki Allah da ya gafarta masa, sannan kuma ya yi damara a wannan sabuwar shekara zai dukufa wajen ayyuka na gari da kauce wa miyagu. Allah SWT muna rokonka da ka canja mana mawuyacin halin da muke ciki a kasar nan na rashin tsaro da kwanciyar hankali da fatara da mayatar rayuwa. Ka ba mu ikon zaben shugabanni na gari a babban zaben kasa da za a yi a cikin wannan shekara ta 1436.

Ko da wai, makalar tawa ta yau, ba batun sabuwar shekarar Musuluncin za ta mayar da hankali akai ba, a`a, za ta mayar da hankali ne akan wani shirin gidan Radiyo da nike gabatarwa mai suna BARKA DA HANTSI a tashar gidan Radiyon FREEDOM mai taken MURYAR JAMA`A da ke Kano da masu saurare kan kama akan mita 99.5, a zangon FM. Tashar Radiyon da a watan Disamban nan mai zuwa in Allah Ya kaimu take cika shekaru 11, da kafuwa, wanda kuma shi ne gidan Radiyo mai zaman kansa na farko a Arewa, da aka fara jin amonsa a cikin watan Disamban 2003, daga rukunin masana`antu na daya da ke Sharada a birnin Kano.
Allah Ya sani Jama`a ma sun sani, cewa shi wannan gidan Radiyo na FREEDOM, tun da aka kafa shi, Allah Ya ke kama masa, ta yadda ya zama gidan Radiyon da yake kan gaba wajen gabatar da shirye-shirye masu matukar kayatarwa da ilmantarwa da fadakarwa da nishadantarwa ga masu saurarensa na cikin Jihar Kano da wasu sassa na jihohin makwabta irinsu Katsina da Jigawa da Bauchi da Kaduna. Tsohon Manajin Daraktar tashar, Malam Faruk dalhatu, bayan yanke hukuncin Hukumar gudanarwa da ta Daraktocin gidan Radiyon, shi ya gayyace ni a cikin watan Satumban 2011, inda ya nemi alfarmar in rinka shigowa don in taimaka musu bisa ga tunanin da suka yi na cewa zan iya bada tawa gudummuwar wajen kara daga likkafar gidan Radiyon.
Bayan mun tattauna da shi na amince, sai ya kira Malam Abbas Dalhatu, wanda a yau yake mai rikon mikamin Manajin Daraktan Radiyon, a lokacin yana Babban Darakta mai kula da Harkokin kasuwanci, ya sanar da shi amincewata. Ya kuma sake kirawo Malam Musa Mamman, Manajan tashar, shi ma ya sanar da shi amincewata, wanda shi kuma ya hada ni da Malam Adamu Isma`ila Garki, wanda ke Manajan shirye-shirye. Da Malam Adamu muka zauna muka tsara yadda shirin zai kasance kamar yadda ake jinsa yanzu, wato daukar sakonni da tambihi da hira da baki da ake yi. Duk wannan abu da ake yi Janar Manajan tashar Malam Umar Sa`idu Tudun Wada yana can cikin Gwamnatin Kwankwaso, amma kuma yana sane da shirye-shiryen da ake yi. Bayan an tsayar da ranar fara aiki sai na zabi yin aiki da Malam Ahmed Rufa`i Bello, wanda da ma shi ma`aikacin gidan Radiyon ne.
Allah cikin ikonSa ranar 24 ga Oktoban 2014, na zuwa muka fara da Ahmed Rufa`i Bello, amma tafiya ba ta yi nisa da shi ba saboda ya fara karatu ke nan a Jami`ar Bayero, don haka sai aka canja shi da Tijjani Ado Ahmed, daga baya kuma aka karo ma`aikata irinsu Abubakar Mohammad Janar da Salisu Baffayo. Babban makasudin bullo da shirin bai wuce laluben da aka saba yi ba wajen ganin an ci gaba da bullo da kayatattun shirye-shiye da za su dace da yanayin mulkin dimokuradiyya da ake ciki a kasar nan, musamman wajen ganin masu mulki suna sanar da wadanda suke mulki inda tafiyar da mulki ya kwana, da kuma sanar da masu mulkin irin yadda talakawa ke kallon mulkin nasu.
A takaice dai shiri ne da bayan wannan aniya yake kuma duba al`amurran da suka jibanci harkokin zamantakewa da na tattalin arziki da na addini da siyasar kanta, inda ake gayyato jami`an gwamnatoci da na `yan Majalisun Dokoki na jihohi da na kasa da na kungiyoyin jama`a maza da mata da matasa da `yan kasuwa da manoma da masana ilmim zamani da makamantansu da sukan shigo su baje kolinsu akan abin da suka sani. Alhamdulillah karbuwar shirin ya sanya tun tuni wasu tashoshin gidajen Radiyo na Kano da na wasu garuruwa suka fara kwaikwayar shirin na BARKA DA HANTSI da wani sunan. A takaice, shiri ne ga mai abin cewa akan yadda zai kara wa masu saurare haske wala-alla akan amanar da suka ba shi ko kuma wani batu na kasa da ya shige masu duhu akan harkokin yau da kullum.
Allah Ya sani ko kusa ban taba tsammamin shirin zai samu karbuwar da ya samu ba, ta yadda ya kai matsayin shirin da masu saurare daga inda duk suke, suke jinjina masa. Kai karewa ma da karau an fada mani cewa marigayi Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero (Allah Ya gafarta masa) mai sauraren shirin ne, kar ka yi batun Gwamnan Jihar Dokta Rabi`u Musa Kwankwaso da makarraban gwamnatinsa, an ce har daukar masu shirin ke yi. Daga mutanen gari maza da mata, kama ya zuwa ga `yan boko da suka hada da malaman Jami`o`i da na sauran manyan makarantu, musamman masu koyar da aikin jarida da tsofaffin `yan jaridar, yabo da godiyarsu ba ta misaltuwa kan shirin. Ba aniyar wannan makalar ba ce ta tabo irin kalubalen da shirin yake fuskanta wala-alla a ciki da waje ba, ba don komai ba sai don babu bukatar yin hakan daga gare ni, kuma ina tsammamin mai karatu ya san cewa idan da dan Adam zai iya rayuwa shi kadai, to, kuwa da rayuwarsa za ta zama cike da kalubale, bare kuma aikin jama`a irin na yada labarai.
Alhamdulillah! Ya zama wajibi in kara gode wa Allah (SWT) da yake kara ba mu fasaha da hikima da saita harsunan mu wajen fadin daidai, da har masu saurare suke cewa shirin yana da dadin saurare. Haka godiya ga Hukumar gudanarwa da ta duba yadda aiki ke gudana (akan aikin jarida) da ta Daraktoci da ke karkashin jagoranci Air bice Marshal Muktari Mohammad (mai ritaya) da Manajoji da dukkan abokan aiki musamman Ahmed Rufa`i Bello da muka fara shirin da shi da wadanda muke gabatar da shirin da su a halin yanzu, da uwa-uba masu saurare bisa ga irin hadin kai da goyon baya da hakuri da suke da ni na yau da kullum. Ina rokon Allah (SWT) ya ci gaba da yi mana jagora, ya ba mu lafiya da zaman lafiya, Ya kuma yi mana kyakykyawan karshe. Alhamdulillah shirin BARKA DA HANTSI na RADIYO FREEDOM na Kano ya cika shekaru uku Allah maimaita mana.