Shirin da ’yan sanda suka yi wa zaben kanan hukumomin Bauchi

’Yan Sanda a Jihar Bauchi sun sha alwashin hukunta masu neman kawo matsala a zaben kananan hukumomin jihar da zai gudana ranar Asabar. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Lawal Jimeta ya ce rundunar ta kammala shiri domin ganin jam’iyyu da masu zabe sun samu aminci a lokacin zaben. Buhari ya taya Sarkin Bauchi murnar cika shekara […]

Shirin da ’yan sanda suka yi wa zaben kanan hukumomin Bauchi

’Yan Sanda a Jihar Bauchi sun sha alwashin hukunta masu neman kawo matsala a zaben kananan hukumomin jihar da zai gudana ranar Asabar.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Lawal Jimeta ya ce rundunar ta kammala shiri domin ganin jam’iyyu da masu zabe sun samu aminci a lokacin zaben.

Ya ce rundunar ba za ta raga wa duk dan bangar ziyasa ko dan daban da ta kama yana kokarin tayar da rikici ba.

Sanarwar ta kuma ce wajibi ne a kiyaye dukkannin matakan kariyar COVID-19 a tsawon lokacin zaben.

Lawal Jimeta ya kuma sanar da hana zirga-zirgar ababen hawa daga karfe 12 dare na ranar Juma’a zuwa karfe 2 na ranar Asabar.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram

Tags