Shirin fim: Pete Edochie ya dawo ruwa da karfinsa
A shekarun baya, idan ana batun komai da ruwanka a farfajiyar shirya fina-finan Turanci a Kudancin Najeriya, idan aka yi batun Pete Edochie, shi ke nan. Yakan fito cikin fina-finai babu kaukautawa, wadanda suka shafi gargajiya ko na sarauta da sauransu. A kan haka kawai sai aka fara ganin yana baya-baya, har ta kai ga […]

A shekarun baya, idan ana batun komai da ruwanka a farfajiyar shirya fina-finan Turanci a Kudancin Najeriya, idan aka yi batun Pete Edochie, shi ke nan. Yakan fito cikin fina-finai babu kaukautawa, wadanda suka shafi gargajiya ko na sarauta da sauransu. A kan haka kawai sai aka fara ganin yana baya-baya, har ta kai ga ma an fara mantawa da fina-finansa a wannan lokacin. A batun da ake yanzu, dan wasan ya dawo ruwa.
Pete, wanda ya kware wajen iya sarrafa kalamai, wanda kuma yake amfani da karin maganganu masu kama zuciyar dan kallo, a kwannan nan ne aka gano shi yana shirya sabon fim da ake wa lakabi da ‘The Godfather.’
An same shi tare da ’yar wasa Adaora Ukoh, suna daukar wani sashi na fim din, wanda ake ganin da shi zai kaddamar da dawowarsa ruwa da karfinsa, musamman ta fuskar fitowa cikin fina-finan zamani.
Da take nuna farincikinta game da aiki tare da Pete Edochie, ’yar fim Adaora, ta lika hotonta tare da shi a shafinta na intanet, na Instagram, sannan ta furta cewa: “Na ji dadi matuka da na samu kaina cikin aikin fim tare da shi. Rabona da in shirya fim da shi, tun fim din ‘The Four Sisters.” Inji ta.
Da wannan ne ake ganin cewa lallai tsoho ya dawo ruwa, kuma za a sake fafatawa da shi, kamar yadda ya saba a baya.