Shirin gasar fitar da zakarun jima’i a Sweden ya tarwatse
Shi jima’i ko an kayar da kai za ka amfana da gamsuwar da ake samu.
Shirin mayar da jima’i wasan motsa jiki da kuma gudanar da gasar farko na fitar da gwani na gwanaye ya ruguje.
Hakan ya biyo bayan wucewar ranar 8 ga watan Yuni wacce aka sa domin soma gasar, kamar yadda wanda ya ayyana shirin Dragan Bratych da kuma daukar gabarinsa a kasar Sweden, amma kuma ba a gudanar ba.
Sai dai bayan gazawar fara gasar da kuma aninyar shugaban shiryawa, cikakkun bayanai sun fito karara na yadda aka haihu a ragaya tun farko.
A wani rahoto da jaridar Gotenborg-posten wacce ake bugawa a garin Gothenburg ta kasar ta ce, Hukumar Kula da Wasanni ta kasar Sweden wadda ke da alhakin kula da wasanni da habaka su, a cikin watan Janairun wannan shekarar ta karbi takardar Dragan kan wannan bukata ta mayar da jima’i wasan mosta jiki.
Hujjarsa ita ce shi ma yana kara lafiyar jiki da na kwakwalwa, baya ga sa nishadi da walwala kamar sauran wasanni mosta jiki irin su dambe da kokawa da wasan kwallo da sauransu.
Ya kara da ikirarin cewa, jima’i ya fi so saboda ko an kayar da kai za ka amfana da gamsuwar da ake samu.
Ashe tun watan Afrilu hukumar ta yi fatali da wannan bukata ta neman sahlewarta.
Tabbacin watsi da takardun neman izinin ya fito ne daga bakin shugaban hukumar Mista Bjorn Erikson, inda ya ce sun ki amincewa da bukatar ce bisa hujjar cewar bai cika wasu ka’idojin hukumar ba.
Sai dai yadda labari ya yadu na cewa kasar ta amince da bukatar Mista Dragan har an sa ranar soma kasar, ya daure wa mutanen duniya kai, tare da rikitar da duk wani mai hankali da kuma yakinin cewa hakika duniya ta zo karshe.
Daga baya dai ta tabbata cewa, ashe Bera ne yake neman masu taya shi bari.
Domin Mista Dragan shi ne mamallakin gidajen rawa masu tarin yawa da ake yin tsirara a kasar ta Sweden.