Shirin gurfanar da Bazoum a Nijar ya fusata Amurka
Amurka ta ce shirin sojojin na gurfanar da Bazoum zai rura wutar fargabar da ake ciki
Amurka ta bayyana fushinta kan barazanar da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar suka yi ta gurfanar da shugaban kasar Mohamed Bazoum, tana mai cewa wannan matakin zai rura wutar fargabar da ake ciki.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, Vedant Patel ya shaida wa manema labarai cewa, sun kadu da rahoton cewa, tsare shugaba Bazoum ya tsallaka zuwa wani mataki na gaba.
- CBN ya sha alwashin farfado da darajar naira a kasuwar canji
- Sojojin Nijar Za Su Gurfanar Da Bazoum Kan Zargin Cin Amanar Ƙasa
“Wannan matakin ya saba wa ka’ida baki daya kuma rashin adalci ne kuma a gaskiya, ba zai taimaka ba a yunkurin magance rikicin kasar cikin ruwan sanyi,” Inji Patel
Wannan na zuwa ne bayan sojojin sun bayyana aniyarsu ta gurfanar da shugaban a gaban kotu dangane da batutuwan da suka shafi cin amanar kasa da kuma barazanar kai mata harin sojin kungiyar Ecowas a cewarsu.
Bayan wani zaman taron da gwamnatin sojin ta gudanar a ranar Lahadin, sun bayyana cewa, suna da cikakkun shaidun da za su gabatar wa kotunan kasar da na duniya da ke nuna cewa, hambararen shugaban kasar da makarraban siyasarsa na ciki da waje, sun aikata miyagun laifukan cin amanar kasar, kamar yadda Kanar-Manjo Amadou Abdramane, daya daga cikin mambobin sojojin da ke mulki, ya bayyana ta kafar talabijin din gwamnatin kasar.