Shirin Ilimi Kyauta kuma Tilas a Jihar Kano: Sai kowa ya ba da goyon baya
Masu iya magana kan ce ilimi gishirin zaman duniya, wadansu kuma su ce ilimi hasken rayuwa. Kowace karin magana ka dauka daga wadannan biyu da na kawo da wadanda ban kawo wa ba, za ka ga ta yi daidai da abin da Bahaushe ke nufi ko yake son jan hankali kan muhimmancin a nemi ilimi. […]
Masu iya magana kan ce ilimi gishirin zaman duniya, wadansu kuma su ce ilimi hasken rayuwa. Kowace karin magana ka dauka daga wadannan biyu da na kawo da wadanda ban kawo wa ba, za ka ga ta yi daidai da abin da Bahaushe ke nufi ko yake son jan hankali kan muhimmancin a nemi ilimi. Karewa ma farkon surar da Allah Ya aiko ga ManzonSa (SAW) a cikin Alkur’ani Mai girma ita ce Suratul Alak, (96: 1-5). Surar daga farkonta zuwa aya ta 5, umarni take yi kan a yi karatu da hikimar Ubangiji Allah (SWT) a kan halitta da yadda zai sanar da mutum ilimin da karamcinSa a kan bayinSa. Sai dai kuma kash! Duk da wannan bayani na Alkur’ani, har yau akasarin Hausawan Arewa sun ki yarda da ilimin balle su rungumi fannonin ilimin ka’in-da-na’in kamar yadda ya kamata.
A duk lokacin da ka yi maganar ilimi ga Bahaushen Arewa, kuma Musulmi, to, maganar tsarin ilimi iri biyu zai fara kawo hankalinsa a kansu kake magana, wato na sanin Allah da addininSa da Ya aiko ManzonSa Annabi Muhammadu (SAW) da shi, da kuma na boko da Turawa ’yan mulkin mallaka suka shigo mana da shi, tsarin ilimin da wadansu kuma kan ce da shi na sana’a, saboda aikin albashi da ake yi da ilimin bokon. Amma dukkan fannonin wadannan ilimi biyu, in ka duba sai ka ga a yau da muke cikin karni na 21, ba fannin da mafi yawan Hausawa suke ba muhimmiyar kulawar da ta kamata, kamar yadda sauran abokan zaman Hausawan, irin kabilun Ibo da Yarbawa ke yi, kai hatta kananan kabilun Arewa sun fi Bahaushe kula da dawainiyar ilimin ’ya’yansu.
Mai karatu, bari in waiwayi yadda wadansu Hausawa ba sa bada kulawar da ta kamata a kan ilimin ’ya’yansu a kan ilimin addinin Musulunci da suka yi imani da shi ba malamin Makarantar Allo na unguwarsu kudin Laraba. Kada ka yi batun biyan kudin wata-wata ko na zangon karatu a makarantun Islamiyya da wasu kan kama daga Naira dubu daya a wata da akan ba da zabin biya kan wata-wata ko a zango daya a biya Naira dubu uku. Wadansu kuma da sukan kai ’ya’yansu tun suna kanana makarantun Allo a wata uwa duniya, ji suke burinsu ya cika a rayuwa na sun dora dansu a kan neman karatun Alkur’ani da zai cece su gobe Kiyama. Duk da wannan imani da irin falalar da ake samu, amma akasarin irin wadancan iyaye za ka tarar ba su kulawa a kan cin yau balle na gobe na ’ya’yan nasu, balle sutura ko sabulun wanka ko na wanki, kada ka yi batun dan abin da irin wadannan iyaye za su ba malami. Shi ma malamin bai damu ba don yana jin aikin Allah yake yi.
Hakan da makamantan halaye na nuna halin ko’in kula da Bahaushe yake nunawa a kan fannonin ilimin biyu.
Idan ka dawo kan karatun boko nan wadansu Hausawa ke nuna matukar gazawarsu, a kan su ma yarda su sanya ’ya’yansu a makarankun boko na gwamnatoci inda ba a matsawa a kan biyan kudin makaranta, sannan karatun kyauta ne musamman na ilimin firamare zuwa aji uku na karamar sakandare, balle kuma su iya sayen littattafan koyon karatu da rubutu ga ’ya’yan nasu. Kada ka yi batun Bahaushen da yake da kudi, amma ya rika ganin tamkar asara ce ya sa ’ya’yansa makarantun kudi inda zai rika fitar da akalla Naira dubu 15 a kowane zangon karatu (bayan wata uku-uku), sannan ya rika sayen tarin littattafan karatu da rubutu duk shekara, bayan kulawa da dawainiyar da makarantun kan bijiro da su daga lokaci zuwa lokaci.
Alhali yana ganin mace kabila mai sana’ar tuyar kosai ko gasa masara a kan titin unguwarsu, ba ta ma yarda ta kai ’ya’yanta makarantun gwamnati ba, ta gwammace da wannan sana’ar ta rika jalautawa tana biyan abin da ma ya fi Naira 15 din, ’ya’yan nata su yi ilimin, mai yiwuwa don sun fi mu sanin muhimmancin ilimin. Sai ka rasa inda wannan sakaci na kin tallafa wa abin da zai taimaki rayuwarsa na Bahaushe ya dauko asali. Idan ya ki dawainiyar karatun boko bisa kiyayyar bambancin addini tsakaninsa da Nasara da ya kawo karatun boko, to me ya sa ba ya tallafa wa karatun Allo ko na Islamiyya? Babban amsa dai ba na ce jahilci ba, illa dai in ce sakaci!
A yunkurin Gwamnatin Jihar Kano na ceto fannonin ilimin biyu ya sanya a makon jiya Gwamnan Jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da sabon shirin Gwamnatin Jihar na Ilimi Kyauta a dukkan makarantun firamare da sakandaren jihar kuma tilas da kuma shirin cusa koyar da darussan karatun boko a cikin manhajar makarantun Islamiyya da na Allo, makarantun da suke dauke da dalibai sama da miliyan biyu, sabanin na boko da suke da dalibai sama da dubu 800. A karkashin sabon shirin Gwamnatin Jihar Kano, bayan niyyarta ta bayar da ilimi kyauta, gwamnatin kuma ta sha alwashin za ta rika dinka kayan makaranta ga daliban makarantun, tare da ba da cikakkiyar kula ga makarantun Allo da na Islamiyya masu dauke da dalibai sama da miliyan biyu da rabi, sabanin dalibai sama da dubu 800 da take da su a makarantun firamarenta.
Shirin Bayar da Ilimi Kyauta kuma a zaman na tilas da kuma yunkurin da ake yi na tallafar ilimin makarantun Islamiyya da na Allo a wannan lokaci da harkokin karatun boko suka tabarbare, musamman a jihohin Arewa, ba karamin kalubale ba ne ga gwamnatin da ta ce za ta yi shi. Bisa la’akari da ta ina za ta fara. Gyaran makarantun da suka lalace? Ko samar da kujerun zama ga mafi yawan daliban da suke daukar darussa a kasa? Ko kuma samar da sauran kayayyakin ayyukan koyo da koyarwa? Akwai kuma matsalolin samar da wadatattu kuma kwararrun malamai da kuma tabbatar da kyautata jin dadinsu ta karin girma da biyansu hakkokinsu da horar da su a kai-a kai.
Ga iyaye da kungiyoyin tsofaffin dalibai da su kansu malamai, akwai bukatar su daura damara wajen ganin sun ninka gudummawar da suke bayarwa don ci gaban ilimi a yankunansu da jiha da kasa baki daya. Ga gwamnatocin jihohin Arewa da suka yi hobbasan ganin ci gaban ilimin a yanzu irin su Yobe da Gombe da Kano da sauransu, ya kamata su sani kuma su kudirce cewa nasara da rashin nasarar shirin ya dogara ne a kansu kacokan. Don haka suna bukatar su nuna wa ’yan kasa da gaske suke cikin dukkan abin da za su yi cikin aiwatar da shirin.
Ga malaman makarantun Allo, ya kamata su bada cikakken hadin kai wajen koyar da darussan boko ga dalibansu, kada su zauna a kan koyarwar magabata ta kyamar karatun boko ko su rika zuba idanu sai an ba su kudi kana za su bada hadin kai. An dai ce kishin baki sai taro, don haka sai kowa ya kama za a kai ga nasara. Yanzu kuma shi ne lokacin.