Shirin Kiwon Lafiya na Dogara: Likitoci sun raba jariran da aka haifa manne a Bauchi

Allah Ya yi wa mahaifan wadansu jariran da suka haifa manne da juna gyadar dogo inda likitoci suka raba ’ya’yan nasu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi a karkashin shirin kiwon lafiya ga mutum dubu 50 kyauta da Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya dauki nauyi a Bauchi. Aikin kula […]

Shirin Kiwon Lafiya na Dogara: Likitoci sun raba jariran da aka haifa manne a Bauchi

Allah Ya yi wa mahaifan wadansu jariran da suka haifa manne da juna gyadar dogo inda likitoci suka raba ’ya’yan nasu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi a karkashin shirin kiwon lafiya ga mutum dubu 50 kyauta da Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya dauki nauyi a Bauchi.

Aikin kula da marasa lafiya da Yakubu Dogara ke yi a kowace shekara shi ne karo na uku a cikin shekara biyu da kaddamar da shi a Bauchi, kuma marasa lafiya daga jihohin Bauchi da Gombe da Filato da Yobe da Adamawa da Kano da Jigawa ne ke amfana da shi.

Mahaifiyar jariran mai shekara 20 mai suna Ikilima Shu’aibu ta ce ta haifi jariran ne a garin Chanka da ke karamar Hukumar Alkaleri da ke Jihar Bauchi a watan Disamban bara amma daya daga cikin tagwayen wacce kanta ya shige cikin dayar ta rasu kwanaki kadan bayan ta haife su dayar kuma tana raye kuma wadda take rayen sai aka rada mata suna Ikilima.

Rayayyiyar ce likitocin da Dogara ya tura suka yi wa aiki inda suka raba ta da dayar da ta rasu domin ceto rayuwarta.

Mahaifiyar jariran wadda take cikin damuwa ta ce ta haifi ’ya’yanta da kanta ba tare da likitoci sun yi mata aiki ba, kuma bayan ta haife su ne aka gan su manne da juna aka turo su Asibitin Koyarwa da ke Bauchi inda suka shafe wata biyu suna jinya har zuwa lokacin da likitoci suka suka yi musu aiki.

Ikilima ta ce wannan ne haihuwarta ta uku, a baya ta haifi ’ya’ya biyu lafiya, kuma tun lokacin da ta samu cikin wadannan komai nata lafiya sai dai ta taba fama da ciwon ciki aka yi mata jinya a Asibitin Gar.

Ikilima wadda ta ce an yi mata aure tun tana da shekara 13, ta ce ta taba zuwa awo sau biyu ne kawai kuma ba ta taba daukan hoton cikinta ba balle ta ga abin da ke ciki.

Jagoran likitocin da suka gudanar da aikin Dokta Joseph Kigbu ya ce sun yi kokarin raba yaran ne domin a ceci rayuwar dayar tunda ’yar uwarta da kanta ke like a cikin ’yar uwar ta rasu. Kuma sun nemi taimakon addu’a domin samun nasara kuma Allah Ya taimake su sun samu nasarar raba su.

Likitoci da ma’aikatan jinya da masu kula da gwaje-gwaje suna ci gaba da duba marasa lafiya kyauta na tsawon mako daya a karkashin shirin na Dogara.

Daga cikin ayyukan da suke gudanarwa akwai duba lafiyar mutane da ba su magunguna da yin gwaje gwaje da yin tiyata da duba masu ciwon suga da ciwon hawan jini da tarin fuka da cutar kyanda da zazzabin Lassa da bayar da shawarwari kan tsabta da kula da lafiya da kuma matsalolin mata masu juna biyu.