Shirin ko-ta-kwana domin dorewar canji a Najeriya

A wannan mako mun bayar da aron wannan shafi ne ga fitaccen dan gwagwarmayar kare hakkin jama’ar nan dan kasuwa kuma dan siyasa Alhaji Abdulkarim daiyabu, inda ya yi tsokaci kan halin da ake ciki a kasar nan kamar haka: Abin tsoro ne har wadansu su fara tunanin PDP za ta iya kwace mulki daga […]

Shirin ko-ta-kwana domin dorewar canji a Najeriya
Shirin ko-ta-kwana domin dorewar canji a Najeriya

A wannan mako mun bayar da aron wannan shafi ne ga fitaccen dan gwagwarmayar kare hakkin jama’ar nan dan kasuwa kuma dan siyasa Alhaji Abdulkarim daiyabu, inda ya yi tsokaci kan halin da ake ciki a kasar nan kamar haka:

Abin tsoro ne har wadansu su fara tunanin PDP za ta iya kwace mulki daga APC, kada Allah Ya ba su sa’a. Mene ma ya jawo har wadansu suka fara wannan mummunan tunani shekara daya da fara mulki? Wadansu na hangen rikicin ’yan Majalisar Tarayya da jagororin Jam’iyyar APC zai iya zama sanadiyyar rushewar gwamnatin.
A gefe guda tsofaffin shugabannin da suka jefa kasar cikin bala’i da masifa, suka rabe arzikin kasar a tsakanin junansu, suka bar talakawa cikin yunwa da talauci da cututtuka. Suka komo suna amfani da wadansu wajen yi wa gwamnati zagon-kasa, ta hanyar ba da shawara an kara kudin man fetur da kananzir, a dada rusa darajar Naira. Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da jihohi da yawa ba sa iya biyan ma’aikata albashi, sannan mafi yawan mutane ba su ma da aiki ko sana’a. barayin shugabanni ke sam musu dan abin bukata na wuni daya su la’anci gwamnati da Shugaban kasa. Da ma Malam Aminu Kano ya gaya mana “Duk wanda zai yi rigima a kan talaka, ya yi shirin rigima biyu, yayin da ya fara yin rigima da wadanda suke zaluntar talakawan, azzaluman za su zuga wadansu talakawa su yi rigima da shi.”  
Ga shi dai duk shugabannin da suka rage masu rai su takwas, Buhari ne kadai aka yarda ba barawo ba, hatta wadanda Buhari ya amince su taya shi aiki, ba a samu irin Buhari ba, wannan shi ne babbar matsalar. Har shi Buhari da kansa ya koka a kan ana matsa masa ya rusa darajar Naira ya kara kudin mai, ya shiga tsaka mai wuya, ba shi kadai yake yin mulkin ba. Ana ta kururuwa, an fara kwato miliyoyin Dala da biliyoyin Naira, amma talakwa suna dada shiga matsi. Babu wutar lantarki, babu ruwan famfo, bayan hauhawar farashi da rashin hanyar samun abin da rayuwa za ta dore. (impossible to get but necessary to spend).
Mataki na farko shi ne yadda za a kwaci Buhari daga hannun miyagun mutane da suka kewaye shi, har ya shiga tsaka-mai-wuya. Kada mu sake PDP ta samu damar komawa mulki. Idan har abubuwa suka kasa gyaruwa a APC, gara asamar da wata jam’iyyar da za ta kunshi tsantsar mutanen da aka zalunta da masu tausaya mana, adalai. A taru a murkushe PDP da duk wadansu azzalumai, a kwato duk abin da suka sata, a hukunta su a bainar jama’a. Idan ma akwai wadanda suka buya a APC, suka labe a bayan Buhari, duk a zakulo su a hada da su a yi musu hukunci bai-daya. Kamar yadda Annabi Muhammadu (SAW) ya ce: “Koda ’yarsa ce ta yi sata, zai sa a yanke mata hannu.” Maganar dan wane ko abokin wane, dan jam’iyya mai mulki ko dan jam’iyyar adawa, Basarake ko Attajiri ko Malamin addini, koma wane ne da wace ce ta kare, tun da mun san barayin da suka rusa mana kasa, suka jefa mu a halin da muke ciki yanzu. An yi walkiya mun ga tsirarar kowa. Babu wata magana sai adalci, adalci sak.
Idan ’yan majalisa sun kasa gyarawa sai mu yi musu garambawul, a canja na canjawa, yadda za a samu masu tsarki su gyara mana dokokin kasar, yadda ba za su yi karo da dokokin Allah ba. Har a kai ga tsarkake alkalai da jami’an tsaro da masu mulki da ma’aikata baki daya. A tsarkake kowace irin mu’amala a  tsakanin al’umma. Rayuka da lafiya da arziki da mutunci da addini na kowa su tabbata an tsare. A bai wa kowa hakkinsa, daidai-wa-daida. Babu cuta, babu cutarwa!
Duk wadanda aka zalunta, aka kashe wa ’yan uwa, aka yi wa sata, aka kwace wa fili a Abuja ko a kowace jiha ko karamar hukuma, ko aka rushe wa muhalli (gida) ba a biya shi diyya ba a saurare su. Haka wadanda suka rasa aiki ko sana’a sakamakon rufe masana’antu da kamfanoni ko kashe noma da kiwo da sana’o’in hannu da kasuwanci da fatauci. Haka rashin wutar lantarki da ruwan famfo da hanyoyi masu inganci, tsaron rayuka, kiwon lafiya, ilimi da sauransu duk a gyara su. Kada su yaudaru da barayin shugabanni da suka fara jefa mu a cikin wannan matsala su ne abin zargi, ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba. Su ne suka dasa masa wadanda suke ba shi gurguwar shawara don bukatarsu, su ne suka rabe duk arzikin kasar a tsakanin junansu, ba sa so a kwace, a ba mu hakkinmu. Su ne suka fara mallaka wa kansu rijiyoyin mai suka kashe matatun mai, suka mallaki jiragen dakon mai da motocin dakon mai da gidajen mai da matatun mai a wasu kasashe, suka kara farashin man fetur da kananzir da dizal, suka rusa darajar Naira, suka kashe bankuna, suka saye masana’antu da kamfanonin gwamnati, har da gidaje da sauran kadarorin gwamnati. Shi ya sa suke yi wa gwamnatin Buhari kafar ungulu, kada asirinsu ya tonu a kwace duk abin da suka mallaka, a harbe su ko a rataye su ko a daure su rai-da-rai. Ni kuma ina ganin gudu suke yi, ba wurin buya, balle su tsira. Saboda haka kowa ya kwana cikin shiri, idan suka rusa APC sai wata jam’iyyar, ba dai PDP ba. Ko sun biyo mu, sai mun ware su daga cikinmu sun fuskanci hukunci na adalci (su dawo da kayan jama’a da suka sace). Tinkahonsu bangarorin da suka hadu suka yi APC, kowane bangare suna da wakilai masu yi musu biyayya ta karshe fiye da bin Allah, kamar yadda suka fara a 1999, wato ci gaba da abin da suka fara tunda aka yi wa Buhari juyin mulki a 1985. Suka rusa duk ginin da aka faro tun zamanin Turawa da Jamhuriya ta Farko. Idan ba a manta ba har Majalisar Koli ta Soja sai da aka rusa kimarta, sai Shugaban kasa shi kadai, ya yi  duk abin da ya ga dama, shi ne abin da ya kawo halin da muka tsinci kanmu, saboda sakacinmu da lalacewar manyan cikinmu, masu kwadayi da tsoro. To yanzu kanmu ya waye, ba ma kwadayin dukiyar sata, sai dai a kwato mana kayanmu baki daya, a bai wa kowa hakkinsa, a hukunta duk wanda ya yi kowane irin laifi, hukunci mai tsanani a bainar jama’a.
Tunda aka sanar da mu, akwai mutum 3,127, wadanda kudin da suka sace mana, idan aka kwato, sun isa a yi kasafin kudi na shekara 11, ba tare da kudin mai ko haraji ba, tilas a kwato su, tunda aka fara sai an kammala, babu tsimbire. Mun gama da PDP har abada insha Allah. Sai dai wata ba ita ba. Gaskiya da adalci su ne suke tabbata ba zalunci ba.
Burin barayin shugabannin kasar nan da suka daddasa wakilansu, suke ba da muguwar shawara, ba su da mu kowa ma ya mutu ba, idan ba haka ba, yaya za a ba da shawara a kara farashin mai, a rage darajar Naira, a ki fara yi wa talakawa tallafi da kudin da aka fara kwatowa? Kamar a ce mutane su yi ta azumi ne babu ci, babu sha, dare da rana har kwana talatin, a ce sai ranar Sallar Idi za a yi musu liyafa? Idan suka mutu kafin sallar wa za a yi wa liyafar? Irin wannan shawara ba abar karba ba ce, balle a yi aiki da ita.
Alhaji Abdulkarim daiyabu
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya, Tsohon Shugaban Jam’iyyar AD na kasa,   Tsohon Shugaban Kungiyar ‘Yan Kasuwa da Masu Masana’antu, Da Ma’adanai da Harkokin Noma ta Jihar Kano (KACCIMA). 08060116666, 08023106666.