…Shirin ‘Lale Kati’ ya sanya ni a tsaka mai wuya a tsakanin Santsi da tabo – Ishak Hadeja

Alhaji Ishak Hadeja, tsohon dan jarida ne da ya shafe shekaru a gidajen talabijin na NTb (NTA), kuma da shi aka yi fafutikar kafa gidan talabijin na Jihar Kano, (CTb 67), kuma shi ne ya kirkiro shirin ‘Lale Kati’ da ya shahara a Jamhuriyya ta Biyu. Aminiya ta gana da shi inda ya yi bayani […]

…Shirin ‘Lale Kati’ ya sanya ni a tsaka mai wuya a tsakanin Santsi da tabo – Ishak Hadeja
…Shirin ‘Lale Kati’ ya sanya ni a tsaka mai wuya a tsakanin Santsi da tabo – Ishak Hadeja

Alhaji Ishak Hadeja, tsohon dan jarida ne da ya shafe shekaru a gidajen talabijin na NTb (NTA), kuma da shi aka yi fafutikar kafa gidan talabijin na Jihar Kano, (CTb 67), kuma shi ne ya kirkiro shirin ‘Lale Kati’ da ya shahara a Jamhuriyya ta Biyu. Aminiya ta gana da shi inda ya yi bayani kan gwagwarmayarsa ta aiki da siyasa da sauransu:

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinka?
Ishak Hadeja: Shekaruna dai yanzu sun kai 60 da wani abu. Na fara karatu a firamaren Abdulkadir da ke Hadeja, sai aka dauke mu a Kwalejin Gwamnati da ke Keffi, bayan na gama kwalejin da na dawo Kano, lokacin an kirkiro jiha a 1969, a 1970 sai na fara aiki da Ma’aikatar Labarai ta jihar. Bayan shekara biyu sai na samu gurbin zuwa karanta aikin jarida, a Kwalejin Koyon Aikin Jarida ta Landan da ke Fleet Street. To, ina gama wannan kwas sai na ji Gwamna Audu Bako yana niyyar kafa talabijin a Jihar Kano, na nema aka ba ni kwas din talabijin a Landan din. Bayan na gama ina can ma aka ba ni aiki, muka fara kafa talabijin na Kano. Kafin mu kafa mun je mun zauna a tashar talabijin ta kasa, wato NTb Kaduna; akwai ma’aikatanmu da ba su san aiki ba, muka dan gwada musu, bayan an yi wasan al’adu na kasa a 1977, (FESTAC), sai muka dawo Kano a 1977 na fara aikin talabijin.
Aminiya: Wacce gwagwarmaya ka yi a aikin?
Ishak Hadeja: Gwagwarmayar tana da yawa, duk da cewa mun samu horo, kafa talabijin bai zama wahala a gare mu ba, amma akwai wadanda muke tare da su, ba su san aikin ba, su muka koyar. Saboda haka kullum in na shiga gidan nan karfe takwas, wani lokacin sai 11 dare zan fita. Haka dai ayyuka da yawa muka rika yi; ni ne wajen shirye-shirye da bayar da umarni, har muka gina gidan. Da tafiya ta yi nisa Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ya ce zai kafa talabijin, kuma dama mu mun fara gajiya da ita NTb din a lokacin. Saboda wadanda suke yin aikin ba su ake yi wa abubuwan da suka kamata ba, irin su bayar da gidaje da rancen sayen mota, wadansu ake ba. Kuma koda na bar NTb na je wajen Alhaji Abubakar Rimi, wato tukwici ne na yi, saboda a lokacin da nake neman aikin in samu kwas din talabijin din nan, Alhaji Abubakar Rimi yana daga cikin wadanda suka taimaka aka kara mini shekara biyu. Saboda haka zuwa wurinsa ba wani abin damuwa ba ne. To, amma inda muka samu kalubale ba irin kafa talabijin ta CTb.
Saboda lokacin siyasa ne, mutane da dama sai muka bar NTb zuwa sabon gidan talabijin, sai da muka yi wajen shekara guda muna zaune, aka rika bayani kayya-kayya Rimi ya yaudare ku. Ya kawo talabijin din ma ba kafawa za a yi ba da saurans. Duk muka jure wadannan maganganu, da aka zo aka tura wajen mutum 24 Amurka suka samu horo suka dawo. Mu kuma manyan ma’aikata muka tafi muka yi wata uku a New York da Los Angeles muka samo horo. Shi ne lokacin da muka dawo, gwagwarmayar siyasa ta yi yawa, don ba irin maganganun da ba mu ji ba.
Da aka zo aka kafa talabijin na CTb 678, neman wurin da za a kafa ma sai ya zama hayaniya. Saboda a lokacin a cikin tsananin gaba da hassada tsakanin banagaren santsi da tabo. Santsi na su Abubakar Rimi, tabo na su Sabo Bakin Zuwo. Saboda haka wannan lokacin muka shiga tsaka-mai-wuya. Kafin ma a zo wannan, mun nemi lasisin shigo da kayan aikin da za a kafa gidan talabijin din ta yadda za a sayo na’urori da sauransu. Kuma a wancan zamanin Ministan da ke kula da wannan wurin dan Kano ne, sai siyasa ta sake shigowa aka hana mu, muka yi ta tafiya Legas aka tura Kwamishinoni aka yi ta zuwa, aka hana mu. Wadanda suka nema a bayanmu irin su Jihar Imo aka ba su, amma Kano sai aka hana mu don siyasa. Ba a ba mu lasisin nan ba, sai a watan shida, kuma a lokacin mun dauki alkawarin za mu kafa talabijin din ranar 1 ga Oktoba, wato wata hudu. To, tsakanin wata hudun nan gaya min yadda za a yi mu shigo da kayan nan, a yarda mu gama shigo da su a kan idon jami’an Gwamnatin Tarayya. Wannan babban kalubale ne, amma da yake muna da shugabanni da suke da hangen nesa, lokacin da za mu kafa talabijin din nan har kayan sun shigo ta cikin kayan NTb, kuma Gwmanatin Tarayya ba ta san sun shigo ba. Saboda Gwamna Muhammadu Abubakar Rimi da mukarrabansa sun yi amfani da alakarsu da wasu mutane kan haka. Kuma wani abin mamaki da aka kawo kayan daga ruwa a cikin motar NTb aka zubo kayan aka kawo mana har gidan gwamnatin Kano.
Kai don mu samu lasisin nan, idan ka je gidan waya na Kano, akwai wani gini da aka yi za a sanya Hukumar Sadarwa (NITEL) a ciki, to, a gabansa akwai wani lambu, wallahi gwamnatin Kano ta bayar da wannan lambu aka ba ta lasisin shigo da kayayyaki. Duk irin wadannan abubuwa muka yi ta shiga, amma 1 ga wata (Oktoba) ba mu fara watsa shirye-shiryenmu ba, saboda wata ’yar matsala ta sarrafa na’urorin sadarwa, amma 6 ga wata muka fara watsa shirye-shiryenmu. Kowa ya yi mamaki, su kansu ’yan NPN sun yi mamaki. Sai dai wannan jajircewa ta Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi da mu da muka dauki alkawarin da yaran da muka horar da yin wannan aiki. A haka muka kafa talabijin, aka zo aka fara shirye-shirye, kuma shirye-shiryen da suka dauke hankalin masu kallo a Jihar Kano, ba tare da la’akari da jam’iyya ba.
A lokacin ne na bullo da shirin ‘Lale Kati’. Kuma shirin babu zancen dan santsi ko dan tabo ko dan NPN; mutanen Abubakar Rimi da na NPN da na UPN kowa yana shiga talabijin din nan. Misalin da zan bayar shi ne, ni na zo nan Kwanar Sabo, har gidan Marigayi Alhaji Sabo Bakin Zuwo na dauki bayanansa. Saboda ya ce in kuka je kuka sanya wannan shirin na tabbata Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi zai kore ku. Abin da na gaya wa Alhaji Sabo Bakin Zuwo shi ne, za mu sanya shirin nan, amma don Allah don Annabi ban da zage-zage a ciki; in kuma ka yi zagi sai na ciccire wuraren. Harkarku ta ’yan siyasa ka je ka yi, ban damu ba, muka dauki shirin, ka san wani abin mamaki sai na dauki waya na buga wa Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi, na ce ranka ya dade yau kana da babban bako a filinmu na talabijin, ya ce wane ne, na ce Sabo Bakin Zuwo ne. Sai ya ce, a’a da kuwa na yi niyyar fita, amma na fasa sai na zauna na kalli shirin.
A gaya min a Najeriya, ana cin zafin adawar nan, ai Gwamnan ma na iya cewa don me kuka dauki shirin, amma Muhammadu Abubakar Rimi cewa ya yi bari ya zo ya zauna ya kalla. Mun taba gayyato Aminu Wali har cikin gidan Gwmanati muka je muka dauki hirar da aka yi da shi. Babu kuma zance labarai na PRP, idan dai labarai na PRP ne, santsi ko tabo za mu sanya shi. Har ma su kansu ’yan santsin sukan ce mu ba mu yarda ba, an zo an kawo mana ’yan tabo a cikin talabijin din. Duk irin wadannan maganganun babu irin wadanda ba mu ji ba, amma mun toshe kunnuwanmu.
Aminiya: Shin kai ne ka kirkiro da shirin ‘Lale Kati’ ko hukumar talabijin din?
Ishak Hadeja: Ni Ishak Hadeja na duba na gani na kirkiro shi. Da farko akwai wata hira da aka yi da Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi, inda ya ce to, bana za a lale kati; ku kun yi shekara hudu, mu ma mun yi shekara hudu, a zo a gaya wa jama’a abin da aka yi. Kuma manufar shirin lale kati ita ce, duk mutanen Kano suna jin ana hawa duro a yi lacca, to ba su taba ganinsa ba, sai dai su ji. Saboda haka muka ce to, lale kati zai kai musu har gidajensu irin wadannan laccocin da ake yi a kan duro. Wannan ita ce manufar lale kati. Duk inda aka yi laccar siyasa, ta Rimi ce, ta wani ce haka muka yi ta sanya ta. Allah sai Ya sa aka dace, a lokacin akwai mutanen da ke hamayya da juna a cikin harkar siyasa. A gefe daya, akwai Alhaji Muihammadu Abubakar Rimi da Sabo Bakin Zuwo ga Mahmud Usman ga Lawan Dambazau, ga su nan dai irin su Lawan Narogo din nan. Don haka sai ya zama tamkar wasan kwaikwayo ake yi. Yau Rimi zai fito ya fada, gobe kuma ka ji Alhaji Sabo Bakin Zuwo ya fito, wannan ya sanya mutane suke sha’awar su kalli ‘Lale Kati’. Saboda ba mutum daya ba ne, ba kuma bangare daya ba ne. Kuma ka sanya Abubakar Rimi a cikin talabijin ya ce maka “Da aka yi Shehu na kwarai, yanzu kuma mun zo an kawo mana wani Shehu Shawaraki.” Ko kuma ka ji Alhaji Sabo Bakin Zuwo yana cewa, ka san shi Rimi wawa ne, idan ka ce je ka zagi wane, shi ke nan sai ya sanya falmaran dinsa, ya je ya zage shi, da safe ya zo ya ce, yaya na burge? Duk irin wadannan abubuwan muke ta sakawa, muka yi ta fadakar da mutane kan yadda ake tafiyar al’amuran siyasa yadda ya kamata. Idan Rimi aka soka za mu sanya; idan ya yi martani za mu sanya. Domin mun taba zuwa Sakkwato, akwai NTb Sakkwato, aka yi hira da Muhammadu Abubakar Rimi, wadda ta yi hira da shi, ta ce, wai ka ce kai da Nwobodo ku kuka fi kowa kyau a cikin gwamnoni, wai dole a zabe ku? Sai ya kale ta, ya ce da ita, yanzu tsakaninki da Allah, tsakanina da Garba Nadama wa za ki dauka? Sai ta rasa abin da za ta ce. Wallahi saboda wannan hirar da ta yi sai da aka kore ta daga aiki, muka zo kuma Kano muka ba ta aiki.
Cigaba a shafi na 37

Irin wadannan abubuwa da muka rika sanyawa a ‘Lale Kati’ fisabilillahi ko’ina ka je, mutane suna so su zauna su gani. In dai lokacin ya yi, wato 8:58 zan kada gangar ‘Lale Kati’, babu mai zuwa kallon labaran kasa na NTA.
Kai akwai wani babban dan siyasa a garin nan da ya ce shi ba zai iya kallon shirin Network News ba, saboda bai san abin da za a fada a ‘Lale Kati’ ba. Saboda farin jininsa a wancan lokacin, ka ga Gwamnan Jigawa Sule Lamido, in ya zo gaida Gwamna, sai ya zo ofishina. Shi da kansa yake neman mu yi masa kaza, mu yi masa kaza. Ya ce idan ba a sa shi a ‘Lale Kati’ babu wanda zai san ma yana siyasa. Irin wadannan mutane suna da yawa. Shaharar da ‘Lale Kati’ ya yi ta kai ga mutane suna so su ji abin da aka ce, ko kuma a sanya su a shirin. NPN ta yi matukar jin kunyar wannan abin da dan jam’iyyarta ya fada. Kuma lokacin da Shagari ya zo aka tarbo shi daga Daura, aka zo dambatta, aka zo Gwauron Dutse. Duk sai da ‘Lale Kati’ ya dauki al’amuran da suka wakana. Muka sanya shirin na tsawon minti 45. ’Yan NPN suka yi ta ihu ai dole, Shugaba mai cikakken iko ya shigo gari. Sai mu kuma muka ce lokacin da Shagari yake garin nan, to Dodon NPN yana Sakkwato; muka dauko Muhammadu Abubakar Rimi, inda yake cewa, tunda ake haihuwa a Sakkwato birnin Shehu, wa ya taba haihuwar dansa aka zo aka sanya masa Akinloye, aka ce babu, amma wai su zo, su ce wai jam’iyyarmu ta kafirai ce. Rimi ya zo ya yi fatattaka. To haka ake so, idan kai bai wa wadannan dama, wadancan ma sai ka ba su. Haka muka yi ta yi, shirin ‘Lale Kati’ ya shahara, shi kansa Alhaji Muhammadu abubakar Rimi har tambaya ya rika yi, wai me aka yi jiya a shirin ‘Lale Kati?’ Yakan yi irin wannan tambayar in baya nan, saboda mutane na yi masa waya su ce kaza da kaza aka ce, ai mu jiya an burge mu.
Akwai lokacin da Cif Obafemi Awolowo ya yi kwana uku, kuma duk inda ya je da Kachako da ina ne, duk muka sanya shi a shirinmu. Wallahi da kansa Awolowo ya ce a je, a kirawo ni duk inda nake. Ya miko mini hannu muka gaisa, ya ce ya gode abin da aka yi masa. Mun yi matukar kokari wajen bai wa kowa dama, amma ka san dole wanda yake daukar nauyinka dole ka ba shi kaso mafi tsoka.
Akwai wani dan siyasa na NPN da ya je nan Ladin-Makole ya yi lacca, kuma cikin sa’ar Ubangiji mu kadai ne kyamararmu take wurin. Ya zo ya yi balbalin bala’insa,. Ya ce su fa ’yan NPN Mujahiddin ne, idan aka nada wani arne a matsayin Shugaban kasa za a zub da jini, za a zub da jini? Aka kawo mini kaset din na ce Alhamdulillahi. Na rike kaset din nan ban sanya shi ba, sai ranar da Shagari ya zo garin nan a 1983. Muka zo muka sanya a ‘Lale Kati’, muka ce da dai taken NPN shi ne ‘kasa daya al’umma daya,” amma yanzu ga wani sabon tsari ya fito daga bakin wannan jami’i, ya rasu shi ya sa ba zan fadi sunansa ba. Muna harba wannan kaset din gaba daya ’yan NPN a garin nan suka rikice. Washegari aka juya aka ce an dakatar da shi na tsawon wata shida. To, irin wadannan shirye-shirye muke ta sakawa, kuma daukacin jihohin da ake da akidar sauyin ci gaba mun aika musu da wannan kaset din.
Aminiya: Wane irin kalubale ka fuskanta game da shirin ‘Lale Kati?’Ishak Hadeja: Za ka yi mamakin cewa a lokacin akwai jami’in tsaro da ke zuwa ya zauna, har ma muka zama abokai. In ya zo ya tambaye ni, sai in ce me kuke so, in ya ce kaza muka gani, sai in dauko kaset din in sanya masa ya gani. Haka muka kasance tare da jami’an tsaro. Ni yanzu ban ma san inda mutumin yake ba, wani kato ne Bakatsine. kalubalen da muka fuskanta shi ne, akwai ’yan santsi da ke ganin bai dace ba mu rika sanya ’yan tabo da ’yan NPN a talabijin, sannan akwai wasu ma’aikata a gidan CTb. Sai dai shi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ya ce ya kafa talabijin din ne don a rika ganin ayyukansa, amma bai hana a sanya wani ba; dama shi damuwarsa idan ka buda tashar NTb babu abin da za ka ji sai Shagari. Duk da wadannan masu nuna rashin amincewar Rimi ya ba mu wuka da nama, mu ma sai muka yi kokarin kiyayewa, wajen ganin ba mu sa abubuwan da ba su kamata ba. Sai dai munafukan gidan sun damu da cewa babu maganar da ake sai ‘Lale Kati’, sai Ishak Hadeja. Haka suka yi ta munafunci da sun samu labari sai su je su sanar da NPN. Ka ji fa, mutumin da aka dauko ka aka kara maka matakin albashi ga kudin haya, amma ka ji abin da suka rika yi. Mun dai zama abokan gabar wadanda suka zo CTb don neman abin duniya, sabanin mu da muka yi alkawarin gina tashar talabijin din. Kusan duk abin da za mu yi, sai sun yi mana zagon kasa. Mu abin da muke alfahari da shi, shi Rimi ya sani ba mu sa kwadayin abin duniya ba. Haka muka zauna da shi lafiya. Ni dai na gode wa Allah saboda ‘Lale Kati’ ya fito da CTb, ya fito da Ishak Hadeja.
Wadannan munafukan ana cewa an samu sauyin gwmanati sai suka koma gindin ’yan NPN. Kuma babu wanda ya taba tunani ni Ishak Hadeja zan kara kwana daya a gidan CTb bayan Sabo Bakin Zuwo ya hau. Sai muka jera kwana 90, a karshen makon da ake tunanin za a kore mu, sai Allah Ya kawo soja.
Aminiya: Da sojoji suka karbi mulki ko an ci gaba da ‘Lale Kati?’
Ishak Hadeja: Sojoji sun shigo babu zancen ‘Lale Kati’. Da gwamnati ta zo, sai aka je aka debo wata gayya, wadanda suke zaginmu cewa mun baro NTb, mun dawo nan. Sai aka wayigari wurin da muka kafa, iyayen gidansu sun kawo su CTb. Wadannan mutane da manajojin daraktoci ne a gidan rediyo da talabijin na NTb, kuma da shigowarsu sai suka ce, to, mu fa duk wanda ya shafi Rimi idan ya daga mana hanci za mu kore shi. Dole dai suka zauna da mu, domin su iyayen gidansu ne suka turo su, mu kuma mu muka san aikin. A lokacin Hamza Abdullahi ne. Muka ci gaba da aikin talabijin, amma dai wadannan munafukan suna nan tare da mu. Bayan na bar CTb, na koma Jihar Jigawa, sai aka zo aka yi wani taro, aka ce wai ba ni ne na yi ‘Lale Kati ba. Ni kuwa na ce alhamdulillahi, domin gaskiya daya ce kowa ya santa.
Aminiya: Yaya za ka kwatanta aikin jaridar da kuka yi da wanda ake yi yanzu?
Ishak Hadeja: Fisabilillahi da an yi aiki gwargwadon iko da karfi mutum yake yi, amma yanzu an samu ci gaba wajen na’urori da harkokin sadarwa, wadanda suka hada da waya da kwamfuta da sauransu, an dan takaita maka wahalar da za ka sha da na tafiye-tafiye, wajen tabbatar da sahihancin labari. Gwargwadon iko lokacin da muke NTb Kano kafin mu dawo CTb a kan kamatanta gaskiya. Da wuya ka ga an sanya labari in ba a tabbatar da shi ba. Ba zan ce ba a yi a yanzu ba, amma gasar da ake yi tsakanin gidajen rediyoyi da talabijin kan sanya wasu su sassauta don jawo hankalin jama’a. Mu yanzu alhamdulillahi a Arewa jaridar Daily Trust ita muke ganin take kokarin kwatanta gaskiya a tsakanin Kudu da Arewa wajen bayar da sahihan labarai don kare mutuncin al’umma. Kuma har yanzu muna da karancin gidajen talabijin masu zaman kansu. Don haka na so a ce yadda aka samu yawaitar gidajen rediyo, haka muke da talabijin masu zaman kansu a Kano. Kai na tabbatar da a ce zan zo in kafa gidan talabijin mai zaman kanta, to da NTA da CTb duk sai na danne su, sun yi kasa, duk da cewa shekaru sun ja.
Aminiya: Ganin ka yi shirin siyasa yaya za ka kwatanta siyasar wancan zamani da ta yanzu?
Ishak Hadeja: A da akwai akida tsantsa mai zafi, wato babu sassauci; ni dan tabo ne, ba ruwana da dan santsi ko dan NPN. Uba da da ko wa da kane ba a gaisawa, an bata saboda akidar siyasa. Yanzu an samu saukin wannan, sai dai illar da ake fama da ita a yanzu ita ce neman kudi. Abin takaici abin dariya, mafi yawan ’yan siyasa neman kudi suke yi. Na kalubalanci duk wani dan siyasa a halin yanzu ya fada in ba ta kudi ake yi ba. Ai ina daga cikin wadanda suka je taron fitar da gwani na Jam’iyyar APC a Legas.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya