Shirin noman rani na biliyoyin Naira a dam din Gurara ya zama shifcin gizo – Manoma
Shirin zai iya samar da tan 100,000 na kayan abinci sau uku a shekara idan aka yi shi yadda ya dace
Shirin noman rani na madatsar ruwa ta Gurara da ke Jere a karamar Hukumar Kagarko da ke Jihar Kaduna, nada nisan kilomita kadan ne daga Babban Birnin Tarayya, Abuja, kuma an tsara shi ne don taimaka wa wajen farfadowa da da bunkasa noma a yankin don tashi daga noman da aka saba zuwa zuwa na samar da masana’antu na zamani da ake sa ran fitar da tan 4,500 na shinkafa da tan 6,700 na masara da tan 11,000 na kankana da kuma tan 18,000 na sauran kayan marmari, kamar yadda tsohuwar Ministar Albarkatun Ruwa, Misis Sarah Ochekpe ta bayyana.
Shirin zai iya samar da tan 100,000 na kayayyakin abinci sau uku a shekara idan aka yi shi yadda ya dace.
A shekarar 2001 ce Gwamnatin Tarayya ta bayar da kwangilar aikin fadada dam din Gurara da zai samar da ruwan sha da kuma noman rani a kan Naira biliyan 15.1 inda za a rika tuwa ruwa daga dam din na Gurara zuwa dam din Usuma da ke ba Abuja ruwa, daga baya an kara kudin zuwa Naira biliyan 38.5 sannan aka sake karawa zuwa Naira biliyan 54.3 a shekarar 2007 bayan kara wasu ayyuka da suka hada da noman rani, aikin da aka bai wa wasu kamfanoni biyu da suka hada da Kamfanin Salini da aka bai wa hekta 2,000 da Kamfanin SCC da aka bai wa aikin hekta 4,000.
Idan aka kammala aikin wanda ya kai hekta dubu 12 zai ba da dama ga kananan manoma da masu noman kasuwanci su gudanar da harkokinsu a yankin.
Aikin da aka bai wa Kamfanin SCC Nigeria Limited shi ne lura da rarraba hanyoyin ruwa da za su shafi hekta 4,000 da sanya bututun ruwa na tsawon kilomita 29 da kuma manyan randar adana ruwa mai girman murabba’in milimita dubu 100.
An tsara za a rika gudanar da noman rani har nau’o’i biyar da suka hada da na gwaji da manyan gonakin noman rani da sauransu. Lokacin da wakilinmu ya ziyarci yankin a ranar Asabar da ta gabata ya ga abubuwan da suka durkushe.
Babu kyakkyawan hanyar da za ta sadar da mutum zuwa wajen, sannan motocin da suke wurin ma kwata-kwata ba sa aiki.
Shirin ya gaza cim ma abubuwan da ake tsara tun farko kuma mafi yawan manoman da suka koma wajen don yin noman ranin tuni sun bar wurin saboda dimbin matsaloli da suke gwada yadda hatta Gwamnatin Tarayya ta tafka asarar kudaden da ta zuba a wurin.
Matsalolin da suke dada korar manoma
Gazawar Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Tarayya wajen magance matsalar wahalhalun da ake fuskanta da suka dakatar da shirin na daya daga cikin matsalolin.
Sace wasu kayayyakin aiki a cibiyar noman gwaji da sauransu ya sa galibin tsarin ba ya gudana.
Ga wasu manoman da har yanzu suke noman kayan abinci da sauransu sun ce tsadar noman da suke yi tana faruwa ne saboda kuskuren wajen tone kasar wurin ta yadda aka kwashe kasa mai rai da za ta amfani shukarsu aka bar su da kasa marar taki da za ta inganta abin da suka shuka lokacin gina dam din.
Kuma sakamakon rashin yabanya saboda rashin kasa mai taki akwai bukatar manoman su yi amfani da dimbin takin zamani don ganin sun samu albarka a gonakinsu, wanda hakan ya sa manoma da dama suka hakura da yin noman bayan sun yi noman na shekara daya ko biyu.
Bayanan da jaridar Aminiya ta samu sun ce kafin a fara aikin Kamfanin SCC wanda ya gina dam din a farko ya samar da tsaro ga wurin amma daga baya ya janye bayan da Ma’aikatar Ruwa ta Tarayya ta amshi ragamar aikin. Haka wurin ya ci gaba da kasancewa tun shekarar 2014 da gwamnati ta karba.
Tsarin da aka yi tanada na bayar da hekta dubu daya don noman kasuwanci ba a aiwatar da shi yadda ya kamata ba, sannan Gwamnatin Tarayya ta umarci manoman su tashi daga wajen. An sanya aikin a cikin tsarin ayyukan hadin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu (PPP) a shekarar 2016/2017 da Hukumar ICRC ta yi.
Yarjejeniyar ta bukaci sarrafawa da kuma lura da wurin noman rani mai girman hekta 1000 a Dam din Gurara 1 a tsakanin Azara-Jere da ke Jihar Kaduna don bayar da jinginar kayayyakin da Gwamnatin Tarayya ta samar ga masu zuba jari don amfani da su yadda ya kamata a kan Naira biliyan 2.1.
Tun lokacin da Ma’aikatar Ruwa ta Tarayya da aikin ke karkashinta ta dakatar da manoma yin noma a wurin saboda shirinta na sauya mika harkar ga ’yan kasuwa da za su gudanar da aikin yadda ya kamata, babu abin da aka gudanar a aikace inda yanzu haka ciyayi suka mamaye wurin.
Gazawar gwamnati wajen kula da kayayyakin yana ba kananan manoman yankin kunya.
Wani mazaunin garin Jere mai suna Abdullahi Sani ya ce asalin shirin zai bai wa mazauna wurin damar mallakar wasu sassa na shirin noman ranin amma babu ko daya da ya yiwu.
Ya ce a kakar noma ta shekarar 2014/2015 manoma da dama da suka hada da manya da matsakaita daga cikinsu da suka saba noman kayan lambu da masara sun je sun duba wuraren amma aka dakatar da ayyukansu.
Gwamnati na yawan maganar fadada hanyoyin noma da rage zaman banza wanda da a ce tun farko an aiwatar da abin da ya dace da an samar wa mutane da dama ayyukan yi da kuma ciyar da mutanen Abuja.
Ya ce da an yi abin da ya dace tuntuni da mafi yawan matasan da ke Abuja sun tafi yankin kuma da tuni wajen ya bunkasa da harkokin noma gadangadan a wurin da kewayensa.
Dan Auta wani matashi mai aikin lambu kusa da dam din ya ce Hausawa da yawa da suka saba da harkar noman rani za su iya baro inda suke zaune a Abuja su tare a nan domin su yi noman masara amma hakan ba zai yiwu ba.
Ya ce kalilan din mazauna yankin da suke noma galibi sun fi noman damina ba su cika noman rani ba.