Shirin raba taki ta waya bai da amfani – Sarkin Noma

Sarkin Noman karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano kuma Ma’ajin kungiyar Manoman Najeriya (AFAN) Alhaji Muhammad Yaro Sale ya ce shirin raba taki ga manoma ta wayar salula bai dace da manoman Arewa ba wadanda ke da karancin fahimtar shirin.Alhaji Muhammadu Yaro Sale ya bayyana haka ne yayin da ya tattauna da manema labarai a […]

Shirin raba taki ta waya bai da amfani – Sarkin Noma
Shirin raba taki ta waya bai da amfani – Sarkin Noma

Sarkin Noman karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano kuma Ma’ajin kungiyar Manoman Najeriya (AFAN) Alhaji Muhammad Yaro Sale ya ce shirin raba taki ga manoma ta wayar salula bai dace da manoman Arewa ba wadanda ke da karancin fahimtar shirin.
Alhaji Muhammadu Yaro Sale ya bayyana haka ne yayin da ya tattauna da manema labarai a Kano, inda ya ce shirin ko ba zai magance matsalar da manoma ke ciki ba ta fuskar samar da takin zamani.
Alhaji Yaro Sale ya ce tunda Gwamnatin Tarayya ta bullo da shirin manoman da suka fito daga Arewa da ba su da zurfin ilimin zamani suke fuskantar rashin tabbas na samun taki daga gwamnati.
Ya ce sauran matsalolin da shirin ya kawo sun hada da yadda manoma ke shan wahala kafin su je inda aka tura su, su dauki takin in sun yi nasara, ga matsalar rashin kyan hanyar sadarwa, sannan wasu ba su san bayanan da ake tura musu ba.
Sarkin Noman ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta sake tsarin ba manoma taki bisa la’akari da irin fahimtar kowane sashi na kasar nan ta yadda za ta gamsar da manoman  kasar nan.
Alhaji Yaro Sale ya nuna rashin jin dadi kan yadda manoma ke shan wahala idan suna neman rancen kudin noma daga bankuna da sauran cibiyoyin kudi da ake da su a kasar nan.
Ya roki wadannan cibiyoyi da bankuna su sassauta ka’idojin da suke gidayawa ga manoma ta yadda za su rika samun rance don bunkasa harkokin noma, kuma ya nemi manoman su rika mayar da kudin da suka ranta domin wasu su amfana.