Shirye-shiryen Sallah: ’Yan kasuwar Kano na kokawa da karancin ciniki

Kasuwar kayan yara da ke Nassarawa ta kasance tamkar kufai sabanin yadda aka san ta…

Shirye-shiryen Sallah: ’Yan kasuwar Kano na kokawa da karancin ciniki

Yayin da watan azumin Ramadan ke wa al’ummar Musulmi bankwana aka tunkari bukukuwan Karamar Sallah, ’yan kasuwa a Jihar Kano na cikin mawuyacin hali a saboda karancin ciniki.

Bisa al’ada, ranakun goman karshe na watan Ramadan lokaci ne da hadahadar kasuwanci ke da matukar tasiri a wajen ’yan kasuwa saboda tururuwar da mutane suke yi zuwa kasuwanni domin sayen kayan ado da bikin Sallah.

Aminiya ta kai ziyarar gani da ido zuwa wasu kasuwannin Kano inda ta gano yadda take kayawa tsakanin ’yan kasuwa da kayan da suka kasa da kuma masu saye.

Sabanin kowace shekara, bana ta zo da sauyi saboda rashin ciniki da ’yan kasuwa ke fuskanta wanda suka alakanta da rashin kudi a hannun jama’a.

Kasuwar kayan yara

Kasuwar kayan yara da ke yankin Nassarawa, daura da Asibitin Kwararru na Abdullahi Wase sanannen wuri ne idan ana maganar nau’ikan kayan yara na alfarma da na kwalliya.

Amma Aminiya ta iske kasuwar tamkar kufai sabanin yadda aka san ta da cinkoso a irin wannan lokaci na jajibirin Sallah.

Da yake magana, wani dattijon dan kasuwa, wanda ya ce ya shafe sama da shekara 1o a kasuwar, ya alakanta yanayin da take ciki a wannan shekara da kunci.

“Babu abin da za mu ce sai godiya ga Allah, amma gaskiya ana cikin wani hali. 

“Yanayin rashin kudi da ke addabar al’ummar kasar nan ya yi kamarin da ba iya jin shi ake yi ba, har gani ana yi.

“A daidai wannan lokaci, goman karshe, abin mamaki ne ka zo kasuwar nan ka samu wajen ajiye mota ma, shaguna kuwa har cinkoso ake.

“Yau ka duba ka gani, ga mu nan a zaune kawai; zuwa dan anjima ni ma kwanciya zan yi na huta. 

“Maganar gaskiya babu ciniki, kuma ga kayan nan,” inji dattijon.

Shi ma wani dan kasuwa da wakilinmu ya yi kicibus da shi da yaransa su uku suna barci yayin da shi kuma yake karatun Al-Kur’ani, Suleiman Mu’awiyya, ya tofa albarkacin bakinsa:

“Gaskiya ana cikin wani hali, kasuwa dai babu ita kuma ga shi kaya sun yi tsada ta yadda ’yan mutanen da suke iya shigowa kasuwar ma ba sa iya saye.

“Idan ka duba za ka ga ko su ma masu kudin ba kamar yadda aka saba ba.”

Suleiman ya kara da cewa duk da cewa wata ya zo karshe, ma’aikata za su samu albashi, ya tabbata ba za su saki jikinsu wajen kashe kudi a kasuwanni ba, saboda yara suna dab da komawa makaranta, yayin da kuma yawanci kayan abinci sun kare.

Kasuwar Sabon Gari

A kasuwar Sabon Gari Layin ’Yan Takalma kuwa, zancen gizon dai ba ya wuce na koki a inda galibi daga cikin ilahirin shaguna kaya ne kawai da masu kayan ke zaune kurum. 

Wadansunsu kuma na fama da daidaikun jama’a masu nuna sha’awar siyan takalma.

Bello Muhammad shi ma dattijo ne a wannan kasuwa kuma ya bayyana cewa halin da aka tsinci kai suma a wannan sashe lamari ne da sai addu’a.

“Ba sa iya saye gaskiya, saboda kayan sun yi tsada kuma ga shi babu kudi a hannun mutane. 

“Kayan da kake gani yawancinsu ma tsohuwar ajiya ce; ba mu taba fuskantar yanayi irin wannan ba. 

“Yadda mutane ke wuce wurin nan a irin wannan lokacin, idan ka zo ka ga ni yanzu ka san akwai matsala.

“Kwalin takalmin yara da zaka siyo a Naira dubu saba’in, yanzu ya kai dubu dari da ashirin.”

’Yan Kaji

Kamar takwarorinta, ita ma kasuwar kayan abinci da naman tsuntsaye irin su kaji ba a bar ta a baya ba, yayin da bangaren masu sayar da kaji su ma suke kokawa da rashin cinikin.

Abdullahi Haruna, matashi mai sana’ar sayar da kaji, ya ce, “Ya bayyana irin matsaloli da harkar ke fuskanta sakamakon tsadar da kajin suka yi.”

Layin ’Yan Figa

A akasarin layikan da ke kasuwar, ’yan kasuwa ne kawai zaune a ciki ko wajensu, suna jiran masu sayen kaya.

Layin ’yan figa waje ne da ya yi suna saboda irin yawan kajin da ake gyarawa a kowane lokaci. 

Aminiya ta same su, sama da mutum goma, suna ta sharar barci da tsakar rana cikin ginin kwatar da ke wannan bangare.

A zantawarmu da wakilan wurin, sun bayyana kokensu kan yadda harkokin nasu suka ja baya.

“A baya, a kullum muna gyara sama da kaji dubu biyu, amma yanzu ko dari biyar ba ma iya gyarawa.

“A yau, kajin da muka gyara ba su wuce dari biyu ba,” a cewar daya daga cikinsu.

Ya ce, “A baya a irin wannan lokacin ba za ka iya shigowa wajen nan ba, amma yanzu ka ga dukkanmu barci muke yi, babu kasuwa gaskiya.