Shirin zaune ya fi na tsaye
Nan da ‘yan kwanaki kadan ‘yan Najeriya za su yi tururuwa zuwa tashoshin jefa kuri’a a unguwanninsu, kuma kamar yadda aka saba za a ci karo da wasu matsaloli irin na al’ada da aka saba da su a ranakun zabe. Daga cikin wadannan matsalolin wadanda suka fi addabar jama’a guda biyu ne: dogon jinkirin da […]
Nan da ‘yan kwanaki kadan ‘yan Najeriya za su yi tururuwa zuwa tashoshin jefa kuri’a a unguwanninsu, kuma kamar yadda aka saba za a ci karo da wasu matsaloli irin na al’ada da aka saba da su a ranakun zabe. Daga cikin wadannan matsalolin wadanda suka fi addabar jama’a guda biyu ne: dogon jinkirin da ake samu kafin isowar kayayyakin zabe domin kuwa a wani lokacin, kuma a wasu wurare sai a kai har bayan azahar ba a fara gudanar da zabe ba, saboda rashin kayayyaki. daya gagarumar matsalar da ke ci wa jama’a tuwo a kwarya a ranakun zabe ita ce ta rashin samar da isassun kayyyaki ga dukkan tashoshin jefa kuri’a. Sau da yawa sai ka ga an wadata wasu wuraren da dukkan muhimman kayayyakin da ake bukata, wasu kuma an yi musu kwauron irin wadannan kayayyakin, musamman ma wasu takardun da idan babu su zaben ba zai yiwu ba, ko kuma ba zai yi armashi ba sabo da rashin su.
Sau da yawa akan zargi jami’an hukumar zabe da ke jihohi tare da manyan jami’an da za su gudanar da zabe game da hadin baki da Gwamnonin jihohi don aikewa da kayayyakin zabe akan kari zuwa wuraren da aka san cewa jam’iyyar gwamnati na da magoya baya da yawa, kuma a kan kari, sa’annan kuma a hana wuraren da aka san akwai ‘ya’yan jam’iyyar da ke adawa ne da ta gwamnati muhimman kayayyakin da za su ba su damar sauke nauyin da ke bisa wuyansu.
Wannan babban al’amari ne, kuma ba sabon abu ne ba, domin kuwa ya zama jiki a harkokin zabe a kasar nan. Abin takaici game da haka, shi ne an san da haka, ana kuma kuka dangane da aukuwarsa a kowane lokaci, amma sai daga karshe a kasa daukar wani matakin magance matsalolin da hakan ke haddasawa, hasali ma sai ka ji ana cewa, ai zaben ya yi armashi ainun. Baicin haka nan kuma babu wanda ya taba kalubalantar wadannan al’amuran a kotu, kuma ko ma an yi hakan sai kotunan su yi watsi da karar, su ce ai wannan karamar matsala ce da bai kamata a bata lokaci a kanta ba. To amma duk da cewa jama’a na korafi game da haka, mutane da yawa sun tabbatar cewa ba makawa sai irin haka ta sake faruwa a wannan karon domin kuwa mai hali bai barin halinsa.
Hukumar zabe ta sha cewa a shirye take, ta kuma yi dukkan abubuwan da ya kamata a jajibirin kowane zabe, amma idan lokacin zaben ya zo sai a ga wallenta. Fatanmu a nan shi ne, a wannan karon hukumar zaben da shugabanninta za su ba mara da kunya, su wanke kawunansu daga zarge-zargen da aka yi musu a zaben da ya gabata.
A yanzu dai ga shi nan wadanda suka amfana daga kura-kurai da matsalolin da suka wakana a zaben 2011, suka yi ta yabawa, kamar za su goya Farfesa Attahiru Jega a baya, su ne kuma a halin yanzu suke sukar lamirinsa, suna neman a tsire shi, ko kuma a wancakalar da shi don kada ya gudanar da zabe mai zuwa. A takaice dai Farfesa Jegan da suka mayar tamkar wani waliyyi, sai ga shi nan suna daukar sa daidai da wani shaidani a halin yanzu.
Ba wani abu ba ne kuwa ya hadasa haka, illa yadda Farfesan ya tsaya kai da fata cewa sai an dauki matakan tottoshe duk wata ‘yar kafar da za ta bayar da damar tafka magudi irin wanda aka saba. Jam’iyyar PDP da iyayen gidanta sun hanga, sun gano cewa karshen su ya zo, kuma tsarin da hukumar zabe ta yi don yin amfani da na’urar tantance masu jefa kuri’a ba za ta bari su dukufa kan dabi’arsu ba, shi ya sa suka nemi lallai, ala-kulli halin, sai an yi watsi da wadancan na’rorin. Ganin yadda Farfesa Jega da abokan aikinsa suka dage lallai sai an yi amfani da wadancan na’urorin a bana, bayan jama’a sun gamsu da ingancinsu, sa’ilin da aka yi gwajin su a jihohi 12 a fadin tarayyar kasar nan a kwanakin baya, sai suka dauki karan tsana, suka dora masa, suka yi ta yin zanga-zangar da ba ta da wani ma’ana a garuruwan Kudanci don bakanta Shugaban hukumar Zaben a idanun jama’a.
Irin wannan zanga-zangar ta kin-jinin Attahiru Jega da kuma na’urar tantance masu zabe ta kafu ne bisa kabilanci da bangaranci, domin kuwa wadanda suka fi kowa zakewa dangane da haka su ne mutanen Kudu-maso-Gabas, wadanda ko ruwa mutumin Arewa ya fada ciki za su ce ya tayar da kura. Su ne wadanda suka nuna rashin amincewarsu da kasancewa cikin tarayyar jamhuriyar Najeriya, amma kuma sai ga shi nan sun fi kowa tsoma baki cikin al’amuran da daukacin jama’an Najeria suka raja’a akai, suka kuma yi amanna da su. Ba domin komai suke yin haka ba sai don su yi wa zabe mai zuwa kafar ungulu ne ganin cewa nasara ba ta a gare su, ba kuma za su ci gaba da gallaza wa jama’ar kasar nan ba, ko kuma su yi ta takura musu don bin tsari da manufofinsu.
A yanzu ma saboda a daure wa karya gindi, Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kawar da kansa daga irin izgili da rashin mutuncin da ‘yan MOSSOB da kuma ta OPC ke yi, ya kuma ci gaba da daukar matakan kara takura Farfesa Jega, domin kuwa ya kira shi don jin ko shirin da ya yi na zabe zai dace da manufa da burinsa na murdiya, ko kuwa za a ci gaba da yadda Farfesan ya tsara ne na hana magudi, ta hanyar yin amfani da na’urar tantance sahihancin katuna da kuma cancantar mai rike da shi?
A yanzu dai Farfesa Jega aka sanya a gaba saboda ya tsaya bisa kan gaskiya, ya ki amincewa da matsin da ake yi masa na sauka daga mukaminsa don ya bari a yi sama-da-fadi. Yanzu tun da dai Jega ya dage sai ya yi zabe da kuma na’urar da ke ba azzalumai tsoro, sai shi ma ya tabbatar hukumarsa ta tsaya kan gaskiya yadda zai kamanta adalci, a tabbatar kayayyakin zabe sun isa ko ina akan kari, don ya fita daga dukkan munanan zarge-zargen da ake yi masa.