Shirin zaune ya fi na tsaye(9)

Samar da makarantun almajirai da gwamnatocin da suka shude suka yi alkawarin gigginawa zai hana yara,  almajirai kusan miliyan uku da ke walagigi bisa karauka a Jihohin Arewacin kasar nan, suna barace-barace cikin halin rayuwa mara tabbas, a wuraren da ba su kamata ba, ko kuma suna yin aikace-aikacen wulakanci domin mutane marasa mutunci, wadanda […]

Shirin zaune ya fi na tsaye(9)
Shirin zaune ya fi na tsaye(9)

Samar da makarantun almajirai da gwamnatocin da suka shude suka yi alkawarin gigginawa zai hana yara,  almajirai kusan miliyan uku da ke walagigi bisa karauka a Jihohin Arewacin kasar nan, suna barace-barace cikin halin rayuwa mara tabbas, a wuraren da ba su kamata ba, ko kuma suna yin aikace-aikacen wulakanci domin mutane marasa mutunci, wadanda ba za su taimaka musu da komai ba, sai ma su kara bata masu tarbiyya da tsoma su cikin halin rayuwar da za ta kai su ga galabaita. Haka nan suke ta yawo kwararo-kwararo, babu masu tausaya musu, suna kwalama da rubibi, ko daka-wawa, yayin da aka ba su abincin da ba zai warke musu matsalar su ba, ba kuma zai sa su hakura da bara ba, ko wata wahalar neman abinci.
 Samar da  makarantun da za a tsugunar da almajirai, a dinga koya musu ilimin addini da na zamani a lokaci guda  shi ne mafi a’ala, domin kuwa almajiran za su samu ilimi mai amfani da zai agaza musu wajen bayar da tasu gudummawa, don ciyar da kasa gaba nan gaba. A bisa gaskiya ko ma a ce kawai masu da’awar giggina makarantun tsugunar da almajirai ke yi, sun san cewa  ba za su cika alkawari ba, wani sabon jidali ne kawai suke takalowa.  Dalili kuwa, shi ne, ba su yi wani cikakken shirin tallafar tsarin ba, suna so ne kawai su kai ga cikar wata boyayyiyar manufar siyasa da suke tsarawa, musaman don tozarta  Arewa, da kuma shafa wa jama’arta bakin fenti, don idan an kasa samun nasarar shirin a ci gaba da ganinsu a matsayin masu kyamar ilimin zamani, wadanda ke gwammacewa bin tafarkin haifar da tashin-tashina da kyankyashe ‘yan ta’addan da ke tayar da zaune tsaye a kasar nan.
Jama’a dai ba su gasgata gwamnatoci ba game da wannan manufa, domin kuwa suna sane da yadda tsarin bai wa ‘ya’yan makiyaya ilimi a fadin tarayyar kasar nan, da aka bullo da shi sherkara aru-aru, ya ci tura duk kuwa da wata hukuma sukutum da gwamnatin tarayya ta kafa don kula da shirin, da kuma  makudan kudin da aka narkar game da haka suka bi ruwa a banza, a wofi. Ba wani abu ba ne kuwa ya jawo haka illa hassada da ganin kyashin da ‘yan Kudu suke nunawa don yawancin wadanda za su ci gajiyar tsarin duk ‘yan Arewa ne.
A yanzu ma ba ta sake zani ba, ‘yan Kudu sun fara fitar da wukar su, domin sukan lamirin shirin ilimantar da almajiran Arewa, suna masu cewa da bai kamata ba a zaftare kudin su ba, domin agaza wa wata hukuma ba can daban, sa’annan kuma suna ta cewa, bai dace ba gwamnati ta ware wasu makarantu don koyar da ilimin da ya jibanci wani addini.
A yanzu dai ya kamata a ce gwamnati ta fi kowa sanin cewa jama’ar Arewacin Najeriya ba su kyamar ilimin boko, sun farka, sun kuma rungumi ilmin zamani, sa’annan kuma a wannan marrar babu wani lungun da babu makarantun boko irin ta zamani, hatta ma wanda ke can cikin kauyen kayau akwai,  jama’a kuma na tuttura ‘ya’yansu  zuwa manya da kananan makarantun da ke yankunansu. A yanzu idan da za a yi kididdiga sahihiya, za a gane cewa tazarar da jihohin Kudanci suka yi wa na Arewaci ‘yar kadan ce a yawan makarantun gwamnati, duk kuwa da cewa, ilimin boko ya bayyana a Kudancin kasar fiye da shekaru saba’in kafin isowarsa Arewaci.
Babu irin darussan da ba a koyarwa a dubban makarantun Arewa, tun daga kan na bokon zamani ya zuwa na Muhammadiyya da na koyon sana’o’in da suka jibanci fasaha da kimiyya. Saboda haka nan ana iya cewa, iyayen yara sun komo daga rakiyar makarantun tsangaya, ‘yan kadan ne daga cikin su ke tura ‘ya’yansu makarantun allo. Idan kuwa haka ne ana iya cewa, yawan almajiran da ake gani suna bulayi da tangaririya kan tituna ba, domin iyayensu ba su sha’awarsu da karatun boko ne ba, sai dai don wadansu dalilai can na daban.
Kamar yadda aka tabbatar yawancin almajiran da ke gantalewa kan karauka daga shiyyar Arewa-maso-Yamma suka firfito, inda wasu mutane ke gwada dabi’ar kyuya ko sakaci wajen rainon ‘ya’yan da suka haifa, suka fi gwammacewa su bayar da su ga malaman da ke shiga uwa duniya don su huta da wahalarsu, daga nan ba a sake jin duriyarsu. Haka nan su ma malaman da akan sadaukar musu da wadannan yara gaba take kai su, domin idan sun tafi wani gari almajiran ne za su yi ta dawainiyar ciyar da malamin, su kuma yi kwadago ko aikatau don  samun kudin da za su ba shi don ya ji dadin zaman gari.
Tun da yanzu makarantun Islamiyya da ke kurkusa da gidajen iyayen yara sun wadatu a dukkan manya da kananan garuruwan kasar nan, suna kuma maye guraban makarantun allo, ko na tsangaya, cikin sauki, babu wani dalilin da zai hana ba za a raja’a kan irin wadannan makarantun ba, a kuma tabbatar da cewa iyaye ba su kai ‘ya’yansu nesa ba don neman ilmin addini, suna kai su ta Islamiyyar da ke kurkusa. Ana iya fadada irin wadanan makarantun har ya zuwa jami’a, inda za a  koyar da dukkan darussan kimiyya da na fasaha, irin na makarantun boko a cikinsu, kuma cikin harsunan  Turanci da na Larabci.
Sake tsarin bayar da ilmi don biyan bukatun dukkan sassan kasar nan ne kawai zai magance matsalolin da ke sa ana samun almajirai bila-adadin suna gararamba, ba tare da zuwa makaranta ba, maimakon matakan yaudarar jama’a da gwamnatoci ke dauka don neman suna. dorewar sabon salon koyar da almajiran makarantun allo ya dogara ne bisa tsarin wadatar da isassun kudin yin haka, ba wai a yi ta kame-kame, ko hankoron neman karo-karo don yin haka ba. Kar dai a ce ragon azanci ne gwamnatoci ke yi. Idan kuwa haka ne, to ya kamata su sake dabara, su tabbatar sun bi ingantaccen tsarin da zai biya dukkan bukatun al’umma, domin shirin zaune ya fi na tsaye.