Shirin zuwa Hajji da Gwamnan Osun ke yi ya ta da ƙura kan addininsa

Har yau an kasa gano ainihin addinin da Gwamnan Jihar Osun yake. Hakan ya biyo bayan yawan ganin Gwamnan ne a masallaci da coci yana bauta.

Shirin zuwa Hajji da Gwamnan Osun ke yi ya ta da ƙura kan addininsa

Gwamna Adeleke sanye da kayan coci, a gefe kuma tare da Musulmi lokacin Sallar Idi

Har zuwa yau al’ummomin Jihar Osun sun kasa gano ainihin addinin da Gwamnan Jihar, Mista Ademola Nurudeen Jackson Adeleke yake bi.

Hakan ya biyo bayan yawan ganin Gwamnan ne a masallaci da coci yana bauta kamar yadda mabiya addinin Musulunci da Kiristanci suke yi wanda hakan ke ci-gaba da janyo cece-ku ce a cike da wajen jihar.

Da yake yi wa Aminiya ƙarin haske a kan sanayyarsa da Gwamna Ademola Adeleke, Sarkin Hausawan garin Ede mahaifar Gwamnan, Alhaji Gambo Ibrahim, wanda aka haife a garin Ede, ya ce ya daɗe da sanin cewa Gwamna Ademola Adeleke ya fito ne daga zuriyar wani babban gida a Masarautar Ede inda Fadar Timi na Ede ta naɗa mahaifinsa marigayi Cif Adeleke a matsayin Balogun na Masarautar Ede.

“Mahaifiyar Gwamnan ’yar ƙabilar Ibo ce da take bin addinin Kirista. Kuma kafin rasuwar mahaifinsa Cif Adeleke ya riƙe matsayin Sanata a Majalisar Dattawa a matsayinsa na mabiyin addinin Musulunci, inda ya yi fice wajen ɗaukaka kalmar Allah a Masarautar Ede da jihohi 6 na Kudu maso Yamma” in ji shi.

Dangane da batun cewa ba a san ainihin addinin da Gwamna Ademola Adeleke yake bi ba, Sarkin Hausawan Ede kuma Sakataren Majalisar Sarakunan Hausawa a Jihar Osun ya ce, “Duk wanda yake zaune a garin Ede ya san cewa Gwamna Ademola Adeleke da babban yayansa tsohon Gwamnan Jihar Osun marigayi Isyaka Adeleke da sauran ’yan uwansu an haife su ne a Musulunci.

“Kuma mu da muke zaune a gari ɗaya da su, mun isa mu zama shaidar cewa Addinin Musulunci suke yi domin tare da su muke yin Sallah a masallaci.

“A bana ma tare da shi muka yi Sallar Idi a babban Filin Idi na garin Ede.

“Kuma ya yi niyyar tafiya ƙasar Saudiyya don yin Umara amma Allah bai nufa ba.

“Sai dai muna sa ran za a yi aikin Hajjin bana da shi da yardar Allah,” in ji shi.

A kan jita-jitar cewa Gwamna Ademola Nurudeen Adeleke ya fice daga Musulunci ya koma addinin Kirista har an canza masa suna zuwa Jackson, sai Sarkin Hausawan ya ce hakan ba zai rasa asali da mahaifiyar Gwamnan ba wacce Kirista ce da tun yana yaro ta raɗa masa sunan Jackson.

“Abin da ya faru shi ne, ka san cewa a nan ƙasar Yarbawa yadda uba ya ke da iko a kan ɗansa, haka ma uwa tana da irin wannan iko.

“Saboda haka mahaifiyar Gwamnan a matsayinta na mai bin addinin Kirista ita ce ta raɗa masa sunan Jackson kuma take kiransa tun yana yaro.

“Shi ne dalilin da ya sa wasu suke danganta shi da addinin Kirista. Amma ni ban san lokacin da ya fice daga addinin Musulunci ba,” in ji shi.

Aminiya ta tuntuɓi mai bai wa Gwamnan Shawara kan Al’amuran ’Yan Arewa mazauna Jihar Osun, Alhaji Isma’il Sani Muhammed a kan wannan lamari inda ya tabbatar masa da cewa Gwamnan Musulmi ne ta hanyar mahaifinsa wanda ya raɗa masa suna na Musulunci.

“Mu dai mun san cewa Mai girma Gwamna Musulmi ne da iyayensa suka raɗa masa sunan Nurudeen a Musulunce.

“A kan batun cewa ya koma addinin Kirista kuwa, ina tabbatar maka wannan jita-jita ce da har yanzu bai fito da bakinsa ya bayyana ba.

“Ganin da ake yi wa Gwamna a cikin coci ba zai rasa nasaba da rayuwar mabiya addinai a wannan sashe na ƙasa ba inda kusan kowane gida ake samun zuriya mabiya addinai daban -daban.

“Kuma yana shiga coci ne domin halartar bukukuwan aure da makamantansu da addu’o’in samun mafita a kan matsalolin jihar da ƙasa baki ɗaya,” in ji shi.

Daga ƙarshe ya ƙarƙare da cewa, zargin cewa wasu ’yan siyasa ne suke yin amfani da wannan dama wajen ɓata sunan Gwamna musamman a Jihar Osun da Musulmi suke da rinjaye a kan sauran addinai.

Ya yi kira ga ’yan Arewa mazauna Jihar su yi watsi da irin wannan jita-jita da ake watsawa domin raba kan al’ummomin jihar.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja