Shirinmu na tabbatar da ingancin zabe ya samu matsala – Dokta Gumi

Shaikh Ahmad Gumi daya ne daga cikin manyan malamai a kasar nan, kuma shi ne shugaban wata gidauniya mai suna “ My Choice, my Pride,” wadda ke kokarin ganin an yi zabe mai inganci a kasar nan. A wannan tattaunawa da Aminiya: Watannin baya ka fito da wani tsari kan yadda za a tara kudi […]

Shirinmu na tabbatar da ingancin zabe ya samu matsala – Dokta Gumi
Shirinmu na tabbatar da ingancin zabe ya samu matsala – Dokta Gumi

Shaikh Ahmad Gumi daya ne daga cikin manyan malamai a kasar nan, kuma shi ne shugaban wata gidauniya mai suna “ My Choice, my Pride,” wadda ke kokarin ganin an yi zabe mai inganci a kasar nan. A wannan tattaunawa da

Aminiya: Watannin baya ka fito da wani tsari kan yadda za a tara kudi domin a tabbatar da zabe mai inganci a kasa. Ga shi yanzu kwanaki kadan suka rage a yi zabe, saboda haka muke son sanin inda aka kwana da wannan shiri naka?
Sheikh Ahmad Gumi: Da farko dai ina godiya ga Allah da ya ba ni damar fito da wani tsari, wanda idan har mutane za su ba da cikakken hadin kai kwarai da gaske zai kawo mana saukin magudin zabe. Ba kuma wani abu ba ne illa yin amfani da intanet, wanda ya shafi duniya baki daya. Mun kuma kare tsarin domin tun a watan ramadan muke yunkuri.
Saboda a yau ba ka iya yin wani abu sai ka yi rajista. Mun yi ta jeka dawo domin ganin mun yi rajista na yin wannan aiki. Kasan yadda halin Najeriya yake, sunan da muke so ba mu same shi a haka ba. Da farko mun so “my bote, my pride,” amma sai suka ce ba za mu samu hakan ba wai sai dai mu saka “ my choice, my pride”. Sai muka ce hakan ma ya yi daidai.
Daga nan muka amsa rajistar mu da wannan sabon suna. Koda shaidar izinin amincewa da kungiyar mu ta fito Hukumar Zabe ta rigaya ta kulle amsar takardun masu neman lura da zabe, wato “Obserbers” dama aikin mu, ai ba mu ne za mu je wajen zaben ba. Shi mai katin kuri’a, ma’ana mai zabe shi ne zai tsaya a kidaya kuri’un da suka kada, daga nan sai ya aiko mana da sakamakon a ta intanet.
Bayan kuma ya yi rajista da mu, ba wai haka kawai za ka je ka aiko mana da bayani ba. Saboda haka rashin samun damar kasancewa daga cikin kungiyoyin da aka baiwa damar lura da zabe ba zai hana mu aikin mu ba. Domin ko a zaben da aka yi a Jihar Osun sai da muka gwada musu zabe a can, domin ganin yiwuwar lamarin.
Muka aika sakonnin tes ga mutanen da suke Jihar Osun, domin sanar da su manufarmu. Cewa duk wanda ke son taimakawa wajen ganin an yi zabe mai kyau ya ziyarci shafinmu da ke intanet, domin ya ga yadda zai iya aiko mana da sakamakon zaben mazabarsa, sannan kuma ya yi rajista da mu.
Muka aika, muka saka a intanet duk aikin nan da muka yi sai muka samu mutum 15 kacal da suka yi rajista da mu. Daga nan muke ta magana da su ta waya har lokacin zabe ya zo. Abin da ya faru shi ne wasu daga cikinsu kafin a fadi zaben sun yi gaba abinsu. Wasu kuma ba su tsaya ba domin abin ya yi dare, wasu kuma sun saya har aka fadi sakamakon, amma abin mamaki sai suka kasa aiko mana da sakamakon.
Daga karshe dai mutum daya ne da ya kasa aiko da sakamakon sai ya aiko mana da sakon tes, cewa, jam’iyya kaza ta samu sakamako kaza, wata kuma ta samu kaza. Daga nan ne muka lura ba za mu iya dogara ga mutane kawai ba. Koda kana da mutane sama da dubu 130 a kowace mazaba ba za su iya aiko da sakon ba. Dole sai ka karantar ko koya wa wani mutum yadda ake aiko da sakamakon.
Abu ne mai sauki, amma sai ka koyar da mutane. Wadanda suka yi rajista da mu a yanzu sun kai dubu daya alhalin kuwa akwai akwatunan zabe dubu 130, amma mutum dubu daya ne suka yi rajista tun ma kafin a fitar da ’yan takara. Saboda rashin wayewa da fahimta na jama’armu sai muka ce akwai bukatar mu koma wajen ’yan takarar, domin su kawo mana mutanen da za mu iya koya wa wannan aiki.
Sai muka buga a intanet da jaridar Daily Trust, muka kuma buga wasiku muka aika wa ’yan takarar duka, amma ban da na Yamma maso Gabas da kuma Kudu maso Yamma. Muka nemi cewa kowane dan takara ya kawo mana wakilinsa mu koya musu, su kuma su koya wa sauran mutane, domin idan ba a koya musu ba, ka da a zo a lokacin zabe mutane su kasa aikowa da sakamako.
Domin wannan aikin ilimi ne, amma kasan halin dan Najeria har yanzun nan da muke magana da kai babu wanda ya aiko. Gwamnoni da sanatoci da sauransu. Wato abin yana da daure kai, domin mun gane cewa mutane hayaniyarsu ta fi yawa akan aiki. Sannan kuma ’yan siyasar nan a kasa kansu daya domin ciniki suke yi da juna.
Yanzu abu ya rage mako daya da wani abu ina za a samu mutum 130 da za su rika kawo maka bayanai. Wanda inda a yanzu za mu same su za a iya yi, to amma babu mutanen. Mutumin gari kuwa duk yadda kake ganin yana da basira sai ka ga ba zai iya ba.
Aminiya: Me ya hanaku yin amfani da dalibai wadanda akasarinsu suna amfani da intanet domin su rika aiko muku da wadannan bayanai a lokacin zabe?
Sheikh Ahmad Gumi: Yaran da aka ce suna amfani da intanet a Najeriya, an ce sun kai kusan miliyan 20. Sun iya zage-zage da hira, amma ba su san abin da zai amfane su ba. Sannan kuma wannan abu an buga shi a intanet kuma an fada a radio babu wanda bai sani ba. Tun ma kafin ’yan takarar su fito.
Kuma wannan abu da muke babu ruwansa da wani dan siyasa ko kungiya. Kuma shi wannan sakamakon zaben da aka fitar daga wannan mazaba shi za mu dauko hotonsa mu saka a intanet, saboda haka mu babu ruwanmu da wa ya ci, ko waye bai ci ba. Kuma kai da ka aiko da hoton idan ka shiga cikin shafin za ka ga abin da ka aiko, idan kuwa aka canza maka kana iya yin kara a kai.
Mu babu ruwanmu da wata APC ko PDP, mu dai kawai a yi gaskiya a zaben, kuma duk wanda ya ci a ba shi abinsa.
Aminiya: Tunda abin ya zama haka yanzu ina mafita?
Sheikh Ahmad Gumi: Mafita ita ce, su ’yan siyasar ne ya kamata su yi gaggawar kawo sunayen wakilansu, domin a koya musu hanyar da za su bi wajen aiko da sakamakon zabe. Kowace mazaba a kalla a samu wakilai biyu.
Aminiya: Ko kun sake tuntubar ’yan siyasar abin da ya hana su turo da wakilansu ko maido da amsar takardun da kuka aika musu?
’Yan kadan ne suka maido da amsa. Wani daga Yobe da Bauchi da sauransu. Dukkansu da suka maido da takardun ba su fi mutum shida ba. Akwai wani da ke neman majalisar tarayya bayan an zauna da shi da aka bukaci ya turo wakilansa tun da ya tafi bai sake dawowa ba. Akwai masu takarar gwamna da sanatoci duk an aika musu da wasiku, amma babu bayani.
Mun dai zama kamar bani Isra’ila Musa suke fada wa ‘ je ga ubangijinka ko yi jihadi, mu muna nan muna jiranku. Wato Allah ya je da Musa su yi musu jihadi. Babu mai son ya motsa ko taimakawa sai dai su yi zagi da hayaniya. To, an taba mulkin mutane babu ilmi ba halaye na kwarai. Ba a mulkin mutane da rashin ilmi ko da fushi, sai da basira da wayo ake mulki, amma duk ba mu gane ba.
Saboda haka sai dai kudi ya yi aiki. Ma’ana masu zaben an saye su, masu lura da zaben su ma an saye su. Duk da haka wannan lasisi da aka ba mu ba zai kare a banza ba. Za mu daure mu yi abin da za mu iya yi. Sai dai kai mai mutum dubu daya ya zaka yi da mazabu dubu dari da talatin.
Kai kasan cikin mazabu dubu 100 da wani abu kai mai dubu daya kasan dai babu abin da za a iya yi. Amma dai muna duba yara masu tasowa nan gaba, domin a koya musu yadda za su rika kare ’yancinsu nan gaba. Yadda za su rika zabar mutanen da suka dace domin ita siyasa da dila ake yinta.
A koya wa mutane yadda ake kare siyasa ba tare da zagi ko cin mutuncin mutane ba. Domin me muke yin wannan abin sai don masu biyowa daga baya. Ai duk muna da zuri’a, saboda haka ba za mu barsu da karnuka suna cizonsu ba. Idan muka samu rashin nasara a yanzu sai mu koma mu sake lale, domin gano inda aka yi kuskure da kuma yadda za a kare aukuwar haka nan gaba.
Amma dai yadda zaben nan mai zuwa kaima ka gani. Tun watan Ramadan ake ta kokarin nan wanda kuma kaima ka gani.
Aminiya: Ko masu bada taimakon sun ci gaba da tara kudin kuwa?
Sheikh Ahmad Gumi: Tun da aka yi zaben fitar da ’yan takara mutane suka tsaya.
Aminiya: Ke nan suna ganin babu bukatar wannan shiri ke nan ko?
A’a, ai su ba su sani ba, cewa kungiyoyin siyasa duk wanda ke ciki shi ma kura ne, wannan kudi da ake tara yana son ya ji dadinshi. Wai dan mutum na kungiyarku ba shi ke nuna yana tare da ku ba. Shin ’yan Najeriya na da tsoron Allah ne, ba su tsoron Allah. To, amma an zo da tsarin da kowa zai ga gaskiyar da aka yi ba kuma cewa muke yi muna ra’ayin wani ba ne. A’a, muna cewa ne hoton zaben da aka yi a Enugu da shi nan,
Amma mutane ba su da basirar su gane, kuma da suna da basira da nan za su kawo kudin, inda za a kare hakkinsu. Saboda kungiyoyin siyasa duk wanda ya shiga, ya shiga ne saboda ya samu kuma a yaushe yake samu sai a lokacin zabe.
Aminiya: Wato dai yanzu za ku yi abin da za ku iya ne kawai?
Sheikh Ahmad Gumi:kwarai kuwa za mu yi abin da kawai za mu iya ne. Shi ma din taimako ne saboda gaba. Domin na Osun ya nuna mana kada mu dogara da mutanen gari, saboda mutumin gari ana cikin zaben ma yana iya barin wajen. Domin na Osun akwai wanda da muka yi magana da shi sai ya ce wai ya kai matarsa asibiti saboda tana nakuda. Wato zaben ma ya bar shi, wani kuma cewa ya yi wai wata harka ta kai shi Legas.
Saboda haka duk yadda kake tsammanin dan Adam sai dai kawai ka yi hakuri da shi.
Saboda haka yanzu muna dogara ne akan ’yan siyasa. Shi yasa muke son za mu kai ’yan jaridu wajen domin mu nuna muku irin shirin da muke yi. A yanzu haka dai mun shirya tsaf.
Aminiya: Wane jan hankali za ka yi ga mutane su gane cewa wannan shiri na ku fa don su ake yi, ba don wata manufa ba.
Sheikh Ahmad Gumi: Wannan abu fa kamar a gina asibiti ne, an gina da wane ne? Don mutane ko ba wai dan PDP ko APC ba. Ko an yi hanya mai kyau, an yi don wane nme? Don jama’a ne. Saboda haka wannan abu Allah ne ya kawo shi, cewa ga yadda za ku yi ba za a sake cutarku ba a lokacin zabe. Zai taimaki kowa.
Shi magudin zabe abin da mutane ba su gane ba, shi ne, idan kai yau a garinku kuna APC, wani fa a garinsu PDP suke yi. Kamar yadda PDP ke tsoron APC haka APC ke tsoron PDP a wani wajen. Kuma magudin nan dukkan biyun suna yinsa. Amma mu abin da muke yi ba ruwanmu da ko’ina a dai ga sakamakon na gasken. Taimakon jama’a ne gaba daya ba wani bangare ba.