Shirmen Shoridon Na’ibin-bawa
Ezegareb! Ezegareb!! Ezegareb!!!Jim! Jim!! Jim!!!Gare-gare, gare-gare!Jim! Jim!! Jim!!Rake-rake, rake-rake!!Jim! Jim!! Jim!!! ’Yan makaranta sai mu karkade na-mujiyarmu don jin yadda na shiga kurikuridon Shirum daga turakun turke ababen balaguro da ke unguwar Na’ibin-bawa don shararar hanya daga birnin Dabo zuwa Haurbja, amma ta ajiye ni a bayan kada, inda na shiga cikin wata kwaramniya. Wannan […]
Ezegareb! Ezegareb!! Ezegareb!!!
Jim! Jim!! Jim!!!
Gare-gare, gare-gare!
Jim! Jim!! Jim!!
Rake-rake, rake-rake!!
Jim! Jim!! Jim!!!
’Yan makaranta sai mu karkade na-mujiyarmu don jin yadda na shiga kurikuridon Shirum daga turakun turke ababen balaguro da ke unguwar Na’ibin-bawa don shararar hanya daga birnin Dabo zuwa Haurbja, amma ta ajiye ni a bayan kada, inda na shiga cikin wata kwaramniya. Wannan al’amari da ya auku da ni da wani abokin balagurona, sai muka rika ganinsa lamarin tamkar majigi.
A rana ta sili da manuniyar sama ga watan Farim-biri na shekara ta dubu karamin lauje da sili da tsayuwa bisa kafa daya, da la’asariya sakaliya, na nufi turakun ababen hawa da ke Na’ibin-bawa a cikin birnin Dabo, amma sai aka yi mini dabo, tunda mai jan linzami bai kai mu Haurubja ba; da guntuwar shoridonsa mai suna shirum ta samu matsala sai ya wancakalar da mu a bayan-kada.
Daga Bayan-Kada zuwa Haurubja, an yi zagarabtu da rarake-rarake da gare-gare da ni a cikin wata ’yar karamar kurkurido, inda muka shafe kimanin sa’o’i kofar hanci muna walagigi da yi wa birnin Haurubja shataletale.
Shorido ta samu matsalar bulewar bututun kwararar na kwadi, amma saboda shirme irin na mai jan linzamin guntuwar ‘shirum’ shoridon Na’ibin-bawa, sai kawai ya yi wasu ’yan like-like, duk da haka na kwadi dai ya ci gaba da kwarara, don haka shorido ta ja daga ta tsaya cak!
Ganin matsalar shoridon shirum ta ta’azzara, sai muka yanke cewa ya kaimu turakun turke ababen hawa na Kawon Bayan-Kada, inda ya nemo mana wata ’yar karamar kurkuridon gwalonfo. Sannan ya ce mana ba shi da ko asi, don haka mu za mu bayar da Hauron da za a kai mu Haurubja, duk da cewa mun cake masa daminsa cas, tun a turakun turke ababen hawa na Na’ibin-bawa da ke birnin Dabo. Yana furta wadannan kalamai, sai wata yarinya a cikinmu, wadda daukacin kalamanta murguda baki ne tamkar tana cin kilishi, ta yi ta yaren Ingilishi, amma da aka ce ‘za ki biya Hauro dubu da rabi a kai ki Haurubja,’ sai kawai ta fara furta kamalamai a cikin yaren Hauhau wajen hawan-sa ba tare sa-in-sa ba. “Wallahi ni ba ni da Hauro dubu da rabi.,” injita. Jin haka a raina na ce ashe ta iya yaren Hawan-sa. To kun ji!
Daga bisani aka karkare a kan kowanenmu ya bayar da Hauro dubu sili-sili, inda wani jami’in ma’aikatar Shari’a a Haurubja ya cika mana rabi-rabi, aka yi yarjejeniya, kan cewa mai jan linzami da ya dauko mu daga turakun ababen hawa na Na-ibin-bawa zai biya mu Hauronmu, kuma za a saka wa kowa ’yan matsabansa asusu-asusun ajiya da ke kasar Haurbiya.
Mai jan linzamin kurkurido da ya dauko mu daga Bayan-Kada da karfe sili da sili na dare, ya yi ta raraka gudu da mu cikin dare., sannan ya sanya mana wani faifan wakar raka-rakar Turawan Ingilishi, babu abin kake ji sai surkullen karfkiyar kade-kade da jinjina da kalamai kalallamu masu karo da juna, kamar yadda na jero muku a farkon wannan darasin.
Duk inda mai jan linzamin kurkurido ya tsahirta a shingen binciken Baraden burgar gadi ko na ’ya’yan mai dan taku da kulki, sai kaga an kyale shi ya wuce ba tare da wani cikakken bincike ba, kai hasali ma a wasu wuraren har dakarun tsaro cewa suke yi ya burge su. Domin zan iya tunawa tun a Bayan-Kada, a wani shinge na Baraden Burgar Gadi da suka saurari rugugin “Ezegareb! Ezegareb!! Ezegareb!!! Sai kawai wani barde ya ce, “Babana yayi daidai,” Da jin haka sai wani daga cikin abokan balagurona, mai suna Alhaji Datti, ya ce, “Ka ji, har ka samu da,” ni kuwa n ace masa, “ai wannan shi ne amfanin bugu.”
Mun isowa cikin Haurubja, sai aka sauke wata yarinya da muke tare da ita a gari mai kama da sunan Kububuwa, bayan an ci gaba da luluwa, Aka kara dire wani a kofar shiga garin ‘Gwaram-fa. Saura ni da Alhaji Datti, watakila ko ba mu yi sa’a ba ne, domin za mu shiga cikin Hausawam-fa, sai kawai mai jan linzami ya yi ta raruka gudu da mu, ashe bai san inda zai sauke mu ba. Mun dai kulla yarjejeniya das hi kan zai sauke mu a turakun turke kurkurido da shorido-shorido ta Jabbi da ke garin Tako-tako, amma sai kawai ya yi sabi zarce da mu.
Tashin farko sai ga mu a gari mai kama da kukan jariri Inya-inya, nan fa muka nusar da mai jan linzami cewa ka saki hanya, amma sai nuna mana cewa, ai yasan wurin tun dadadewa, domin da ai gadar sama za a yi a wurin. “Kuma da Malam Nasara el-Rusau ya ci gaba da zama Magajin gari, ai da an rushe wancan katafaren gidan,” a cewarsa lokacin da ya yi mana nuni da wani makeken matsugunni al’umma na alfarma. Sai muka ja bakinmu muka tsuke, shi kuwa ya ci gaba da raraka gudu, har ya kai muku wata unguwa da wani kataon shataletale da aci-balbal tana walwalin waliyo, sannan ga rundunar Baragen Burgar gadi na kewaye da shi.
Baraden Burgar gadi suka yi batutuwa da mai jan linzamin kurkuridonmu, inda daga bisani suka kyale shi ya ci gaba da waligigi da mu, har ya kai mu cikin wani kwari, inda muka rika hango babbar mafuskantar alkiblar kadaita Mahalicci da ibada ta kasa da ke Haurubja daura da Babbanr Cibiyar Addu’a da Gicciye ta kasar Haurobiya. Sai mai jan linzami ya fita daga kurkuridonsa, ya je ya tambayi wani mutum, don ya nuna masa hanya, amma cikin rashin sa’a, sai mutumin ya ce shi ma bako ne, kuma hira ta kawo shi. Nan dai muka yi kasada muka haura zuwa saman gada, nan da nan muka fasko inda muke, muka kuma yi kokarin nusar da shi hanya, har ya kai kowa inda zai sauka, muka yi sallama da shi babu sauran salallami.
Wannan walagigi da halin ha’ula’i da muka shiga, duk na dora laifin a kan uwar kungiyar Na-tuwo, wato masu lalube na tuwo a jikin kurkurido da shorido da ake turkewa a turakun Na’ibin-bawa. Lallai lokaci ya yi da za su yi tanadi ga fasinjojin kurkurido da shirum- shirum. Idan ahr mahukuntan turakun Na’ibin-bawa ba su duba wannan matsala da auku a kanmu ba, to za mu kai kuka wurin Hukuma Karo-karon-titi ta hukuntasu. Kuma akwai yiwuwar mu yi nesa da wannan turakun. Domin an taba kwata irin wannan da ni a shekara ta dubu karamin lauje da manuniyar kasa, inda wani mai jan linzami da ya dauko ni daga turakun turke ababen hawa ta bargar abin da Babban mutum mai rawani ke hawa, ya kuma arce da ni zuwa gari mai sunan shayin ’yan dugwi-dugwi, tun daga wancan lokaci nake takatsantsan wajen zuwa turakun bargar abin hawan babban mutum mai rawani. Jami’an kungiyar Na-tuwo da ke Na’ibin-bawa sai a yi hattara.