Shiryen-shiryen watan Ramadan ga ma’aurata

Murna da gabatowar Ramadan kyakkyawar Sunnah ce da ya kamata ma’aurata su dabbaka.

Shiryen-shiryen watan Ramadan ga ma’aurata

ma’aurata

Assalamu alaikum. Barkan mu da sake haduwa a cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.

Ga bayanin shirye-shiryen da suka kamata ma’aurata su gabatar don tarbar watan Ramadan mai cike da alheri.

1. Hada-kai don dacewa da alheran Ramadan: A wani ingantaccen Hadisi, Manzon Allah (SAW) ya kwadaitar da mu irin ninkin-baninkin ladan da muminai suke samu a cikin wannan wata mai albarka, inda ya ce duk wanda ya yi wani aikin nafila, to za a ba shi lada kamar ya yi aikin farilla a cikin wani lokaci da ba na Ramadan ba.

Kuma duk wanda ya yi aikin farilla, to za a ba shi lada kamar ya yi aikin farilla sau saba’in a wani lokaci da ba na Ramadan ba.

Don haka Ramadan babbar dama ce gare ku ma’aurata da za ku yi amfani da shi wajen hada kai da taimakon juna wajen ibada da karfafa imani.

Idan kuka hada kanku wajen yin bautar Allah (SWT) tare da taimakon juna wajen karfafa imani da inganta ibada, ko shakka babu wannan zai kara karfin so da kaunar da ke tsakaninku, inda ake sa ran Allah zai ninninka muku sakamakonsu.

Don haka sababbi da tsofaffin ma’aurata a dage, a tarbi watan Ramadan da himma.

2. Dagewa da addu’a: Yana daga cikin sunnonin tarbar watan Ramadan, yin addu’a ga Allah don dacewa da kuma aikata kyawawan ayyuka a cikinsa.

Don haka ma’aurata a fara dagewa da yin addu’ar dacewa da Ramadan. Sannan ’yan uwa ma’aurata su fahimce cewa, wannan wata da zai bakunce su wata ne na amsar addu’a da karbar tuba.

Dukkan mu muna da dimbin bukatun da ba za su kirgu ba, kuma dukkan mu masu laifuffuka ne da ba mu san iyakarsu ba, don haka kada a yi sanya, yana da matukar alfanu ma’aurata su zauna su rubuta dukkan bukatunsu a takarda, ya kasance in sun yin addu’a lokacin Ramadan da kuma kafin zuwansa, sai kawai su dauko su karanta, ta haka ba za su mance da ko daya ba daga cikin bukatunsu.

Da fatan Allah Ya amsa mana addu’o’inmu, Ya kuma biya mana dukkan bukatunmu na alheri, amin.

3. Tuba ingantacce: Kamar yadda ya gabata a sama cewa, watan Ramadan watan amsar tuba ne, mun kuma san cewa ba a fafe gora ranar tafiya, don haka ma’aurata kada ku yi kuskuren cewa wai lallai sai Ramadan ya iso sannan za ku tuba ga Allah daga kurakurai da laifuffukanku.

Ya kamata ku kasance cikin tuba, neman yafiya da gafarar Ubangiji Madaukakin Sarki a kowane lokaci kuma musamman a wannan wata na Sha’aban.

Shi ingantaccen tuba yana wanke tsatsar zuciya da daudar ruhi, kuma yana kara kwararar imani cikin zuciya da dogaro ga Allah a koyaushe.

Don haka, sai bawa ya fara Ramadan dinsa cikin sauki, kuma hakan zai taimaka masa ya rika jin saukin gabatar da ibada da sauran ayyukan alheri.

4. Murna da gabatowar Ramadan: Wannan kyakkyawar Sunnah ce da ya kamata ma’aurata su dabbaka a cikin rayuwarsu, babban bako mai tsananin farin jini da kwarjini, mai cike da alherai da albarkatu iri-iri zai iso gare ku ma’aurata, watan da ake rufe kofofin wuta a bude kofofin Aljanna, yana da alfanu ma’aurata su jirace shi cikin murna da kagara da fatan samun dukkan alheran da ke cikinsa.

5. Neman ilimi: Yana daga abin da zai kara kyautata shirin ma’aurata na tarbar Ramadan neman karin ilimi game da watan Ramadan da sauran al’amuran addini, musamman wadanda suka yi kusanci da Ramadan, kamar Sallar dare da ilimin yin addu’a da ilimi game sadaka da amfaninta da ilimin daren Lailatul Kadr da sauransu.

6. Karatun Kurani: Shi ma wani kyakkyawan aiki ne da ya kamata ma’aurata su dage da yin sa a-kai-a-kai tun a cikin wannan wata na Sha’aban ba sai an shiga Ramadan sannan a fara ba.

Idan ma’aurata suka fara tun yanzu, zai yi musu sauki sosai in Ramadan ya iso in sha Allah.

Sai mako na gaba in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.