Shu’aibu Ibrahim, Gusau
Rundunan ’Yan sandan Jihar Zamfara ta samu nasarar kama wadansu da ake zargin masu garkuwa da mutane su hudu a wani samame da ta kai a karamar Hukumar Bukkuyum.Kakakin Rundunar ’Yan sandan, DSP Sanusi Amiru ya bayyana haka a lokacin da yake nuna wa manema labarai wadanda ake zargin, inda ya ce wadanda ake zargin […]
Rundunan ’Yan sandan Jihar Zamfara ta samu nasarar kama wadansu da ake zargin masu garkuwa da mutane su hudu a wani samame da ta kai a karamar Hukumar Bukkuyum.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan, DSP Sanusi Amiru ya bayyana haka a lokacin da yake nuna wa manema labarai wadanda ake zargin, inda ya ce wadanda ake zargin suna cikin mutanen da suka addabi mutane suka hana su sakat ta hanyar sace su tare da dora musu kudaden fansa.
DSP Sunusi Amiru ya bayyana cewa cikin wadanda ake zargi da sace mutanen, akwai Mai Jumma bingel da Mai Jumma Buba da Abu danmajo da kuma Dogon Malam, dukkansu daga karamar Hukumar Bukkuyum.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai jagoran wadanda ake zargi da sace mutanen, ya bayyana cewa sukan amshi Naira dubu 100 zuwa dubu 600 kan duk wanda suka yi garkuwa da shi, sai dai ya ce idan rana ta baci har Naira dubu 20 suna amsa, kafin su saki mutanen da suka yi garkuwa da su.
Wadansu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su da suka hada da Alhaji Abdullahi Fari da Alhaji Ardo Dakake, wadanda dukkansu mazauna kauyen Gwashi ne da ke karamar Hukumar Bukkuyum, sun ce masu garkuwa da su sun karbi Naira dubu 600 daga Alhaji Alhaji Abdullahi Fari, sai Alhaji Ardo Dakake wanda suka karbi Naira dubu 200 kafin a sake su.
Daga bisani Kakakin ’Yan sandan DSP Sanusi Amiru ya ce za su mika wadanda ake zargin ga kotu domin tuhumarsu da zargin aikata laifin satar mutane da yin garkuwa da su da kuma amsar kudi.
DSP Amiru ya yi kira ga jama’ar jihar su rika taimaka wa ’yan sanda da bayanan sirri, musamman mafakar batagari don su dauki mataki ciki gaggawa.