Shugaba Buhari ka kawo dauki Zamfara
Shugaba Buhari ka kawo dauki Zamfara Editan Aminiya, Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. A yau ku ba ni dama domin mika ta’azziyata ga ’yan uwa da abokan arziki , bayin Allah da barayi suka kashe ba laifin komai a garin Badarawa a karamar Hukumar Shinkafi. Da fatan Allah ya tsare gaba, kuma muna kira ga […]
Shugaba Buhari ka kawo dauki Zamfara
Editan Aminiya, Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. A yau ku ba ni dama domin mika ta’azziyata ga ’yan uwa da abokan arziki , bayin Allah da barayi suka kashe ba laifin komai a garin Badarawa a karamar Hukumar Shinkafi. Da fatan Allah ya tsare gaba, kuma muna kira ga Shugaba Buhari don girman Allah ya kawo mana daukin gaggawa, kamar yadda ya kai a Jihohin Adamawa da Barno da Yobe. Domin wallahi tallahi barayin shanu suna cin karensu babu babbaka, ganin kullum cikin kashe bayin Allah suke yi, kamar yadda ’yan Boko Haram ke yi, na kashe jama’a da kone gari, tare da satar dukiyoyinsu da mata da yara. Kuma ga shi mai daraja Gwamnan Zamfara ya nuna halin ko-in-kula. Don ba ya zama a jihar balle ya san halin da talakawansa ke ciki. Ya Mai girma Shugaba Buhari don girman Allah a taimaka, a kawo mana dauki, domin mu al’ummar Zamfara muna cikin wani mawuyacin hali na zubar da jinin al’umma. Naziru Abubakar Sabo Gusau 07033565999 [email protected]
Kuka ga Sarkin Daura
Zuwa ga Edita bayan gaisuwa mai yawa da fatan alheri, a yau ina so a ba ni dama domin in yi kuka ga mai Martaba Sarkin Daura, Alh Umar Faruk Umar. Kukan kuwa, shi ne Mai martaba muna so ka kafa wa drebobi dokar hana gudu tsakanin GRA da Gurjiya. Allah ya kara maka lafiya, na san cewa, ka fini sanin tun daga GRA zuwa Gurjiya duk cikin gari ne, amma irin yadda drebobi suke yin gudu a wannan tsakani. Wallahi sai ka yi zaton Legas mutum zai tafi saboda yawan hadarin da ake yi a wannan tsakani. Abun babu kyau. Don haka mun yi imanin kai kadai za ka iya yi mana maganin maganin wannan matsal in Allah Ya yarda. Daga Hadi Tsohon Sarki Daura 08148442241 08085127726
’Yan kasuwa a tausaya wa talaka
Assalam Edita kabani Dama in yi kira ga yan kasuwarmu na Najeriya, manya da kanana Saboda ba sa jin tausayin talaka. Idan fetir ya kara kudi su kara farashi ko da kayan bai shafi fetir ba. Idan Dala ma ta tashi su kara wa kaya kudi ko da a gida Najeriya ake yin kayan. Don Yanzu Saboda Dala ta tashi doya da manja da magi da ruwan leda “pure water,” da sauransu duk sun kara kudi. Kayan da ake shigowa da shi kuwa, ko da sun dade da shigo da su, ai ba magana. Don Allah ’yan kasuwa aji tausayin talaka. Daga Balarabe Ahmed Garba Tsiga, Apapa Legas. 08034470313
Addu’a ga kasata
Assalamu alaikum Aminiya mai tarin albarka. Don Allah ku ba ni dama in yi addu’a ga kasata Najeriya irin wannan hali da ’yan uwan mu a Arewacin Najeriya ke ciki a halin yanzu abin akwai takaici da ban tausayi. Fatan mu a kullum shi ne, Allah ya ba mu zaman lafiya mai dorewa. Amin. Daga khadija Ibrahim (YAR PROMISE) Jos, Jihar Filato. 07066032339
Kirana ga babban Bankin Najeriya Kirana ga CBN da kuma majalisar tarayya, a kan ya kamata a kirkiri dokar da za ta sa dole bankuna su riga bayar da kariya ga ababen hawan kwastomominsu, saboda sace sacen abin hawa da ake yi a bankuna. Kuma bankuna su ce bai shafe su ba. Daga Bashir Soja Dala 8103135352
Hikimar carar zakara
Gaisuwa ga Babban Edita Mannir. Hikimar wannan adabin na makon da ya wuce, shi ne, Dalar shinkafa a Najeriya nan ba da dadewa fa za ta ƙare. Ya kamata shugaban kasa ya sa majilisa ta dubi yadda za a dinke bakin zaren.’’ Ado Kano. 08039642880
A duba asibitin Tiga
Editan Aminiya ka ba ni dama in koka game da halin da asibitin Tiga ke ciki. Domin yana cikin tsofaffin asibitoci a Kano ta Kudu. Kuma tun zamanin Audu Bako, asibiti Rano ne kawai ya fi shi girma. A yau babu likitoci da malaman jinya da za su lura da marasa lafiya akan kari ko duk sa’adda bukata ta so. Ni ganau ne ba jiyau ba. A da ba haka ake yi ba, amma yanzu al’amuran sun sakwarkwarce a asibitin mu Gwamnatin Kano a duba wannan lamari. Daga Ahmad Tiga 0906938460
Addu’a ga Ado Gidan Dabino
Addu’a ga Ado Gidan Dabino a kan gudummawar da yake yi da kokari da kishi akan harshen Hausa. Ina alfahari da duk mai jajircewa irin sa akan ci gabammu. Ina yi masa fatan alheri a kan jajircewarsa da yio wa Hausa garkuwan. Na farkon ba da gudummawa Abubakar Imam marubuci Magana Jari da ta amfani daliban kasar nan, masu nazarin harshen Hausa. Allah ya saka musu da alheri. Amin. Daga Jamil Nayar Abuja 08033121619
Addu’a ce mafita
Edita.abin da ya dace mu yi, musamman mu ’yan Arewa, shi ne, kamar yadda muka dage da addu’a Allah ka bai wa Buhari kasar nan, to yanzu ma haka ya dace mu yi, ba wai fadar abubuwa na batanci ba. Shugaban kasa mutum ne kamar yadda muke ajizai, amma addu’a ita ce mafitar mu. Daga Hassan Dauda Abubakar Chiromawar Bichi, Jihar Kano 08067723391
Ta’aziyyar A’isha dankano
Salam Edita Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Ya Allah ka jikan A’isha dankano da ta rasu. Allah ka sa ta huta, amin mu kuma in tamu ta zo Allah ka sa mu cika da imani, amin. Daga Sa’adu Baffa Funtuwa 08078535480
EFCC Ya labarin Stella Oduah?
Edita wai, shin EFCC ko ta manta ne da tsohuwar Ministar Jiragen Sama Stella Oduah? Ai Irin badakalar da ta yi bai kamata akyale ta ba, tamkar an bar baya da kura ne. Domin tabargazar,da ta shuka a kasar nan, ya ci a ce, an cafko hannun ta. Daga Yahaya Ahmed Jabo Apapa Lagos 08128286038