Shugaba Buhari kunenka nawa? (4)
Ni dai ba masanin tattalin arzikin kasa ba ne, to amma abin da ke tashe yanzu a duniyar inganta tattalin arziki a duniya kamar yadda masana harkar ke bayani, shi ne a ‘tayar da komadar tattalin arzikin talakawa da sauran al’ummar kasa, ba wai tayar da komadar tattalin arzikin kamfanoni da ’yan jari-hujja ba,’ wanda […]
Ni dai ba masanin tattalin arzikin kasa ba ne, to amma abin da ke tashe yanzu a duniyar inganta tattalin arziki a duniya kamar yadda masana harkar ke bayani, shi ne a ‘tayar da komadar tattalin arzikin talakawa da sauran al’ummar kasa, ba wai tayar da komadar tattalin arzikin kamfanoni da ’yan jari-hujja ba,’ wanda shi ne gwamnatinka ta sa gaba.
Ka sani ya Shugaba Muhammadu Buhari, masana tattalin arzikin kasa tuni sun gano cewa kasashe irin Najeriya ba za su taba fita daga tarkon masassarar tattalin arziki ba, har sai sun tayar da komadar tattalin arzikin talaka da marasa karfi, ba kuma wata hanya da ta dace a bi da ta wuce a sa kasafin kudin kasa ya fuskanci al’ummuran da suka shafi talaka kai-tsaye, kamar samar da ingantaccen ilimi ga yawancin al’ummar kasa da rage radadin talauci ga yawancin talakawa da yara kanana, ba wai tsarin “Trader Moni” ko “N-Power’ ko wani adashin gata da bai fitar da mutane daga damuwa da kunci ba. Wata hanyar gyara kuma ita ce a samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya ga yawancin al’ummar kasa, shi ma mataki ne na auna ci gaba, ba wai makale wa tattalin GDP kawai ba da a takarda yake kwana da tashi, sai kuwa a asusun ’yan jari-hujja. Ke nan tsarin tattalin da muke gudanarwa a halin yanzu ya Shugaban Kasa! Ya yi ban-hannun-makafi ne da abin da ke tabbatacce da halin rayuwar talaka. Ka ga ke nan, jiya, i yau, kila ma i, gobe ko har abada, in ba gyaran kwarai aka yi ba. Allah Ya kyauta!
Saboda haka ya Shugabana! Lokaci ya yi da za ka samar da dawwamammen tsarin tattalin arzikin da zai sa talakawa farin ciki da annashuwa, kada su kasance sun yi zaben tumun-dare, sai safiya ta yi su rasa abin sa wa a bakin salati. Ka dai san irin halin kuncin da al’ummarka ke ciki, ka fada, ba sau daya ba biyu ba, amma kullum na yi nazarin tsarin da kake bi na gudanar da tattalin arzikin kasa sai in ga tamkar madubin da kake amfani da shi, na duba-rudu ne, ko mai zagi, domin ni abin da nake hangowa kai ba shi kake hangowa ba, ban sani ba, ko kai ba ka ji a jikinka ne, kamar yadda mu muke ji! Ga hujja: Da hawanka mulki ya Shugaba! Ka bayyana mana cewa za ka cire tallafin da gwamnati ke bayarwa domin samar da albarkatun man fetur arha ko cikin rahusa ga al’ummar kasa, ta haka za a samar da fetur da kananzir da gas, yanfu-yanfu a cikin kasa. Nan take ka ce ka ‘cire’ tallafin, wannan ne ya sa ka kara farashin fetur da kanazir da gas. Shi man fetur ka tada shi daga Naira 87 zuwa Naira 145, duk da cewa talakawa sun san karin farashin albarkatun man fetur zai wahalar da su, amma saboda imani da yarda da aminci da suke da shi game da kai, ga kuma dattakunka da rikon amana da suke gani game da kai, suka hakura, suka mika wuya domin a yanka, in dai wannan shi ne zai kawo karshen matsalolin da ake fuskanta. Amma, ya Shugabana Buhari! Shin me ya canja tun daga wancan lokaci zuwa yau?
Talakan Najeriya dai ya fahimci cewa shigo-shigo ba zurfi ne aka yi masa, domin kamar yadda jami’an gwamnatinka ke fada yanzu, bayan tsawon lokaci da cire tallafin, suna ikirarin wai ba a cire tallafin man fetur ba a can baya, yanzu ne ya kamata a cire. Wai, suna ce da mu abin da aka yi a baya shi ne ana dai biyan hamshakan ’yan kasuwa masu shigo da tataccen mai da Kamfanin NNPC, biliyoyin nairori na tallafi, domin a samar da albarkatun man fetur cikin sauki. Ya Shugabana! To ina amfanin karin kudin man fetur da aka yi a can baya, idan shi ba cire tallafi ba ne? Me ya sa aka kara kudin man fetur da sauransu, shi kuma me sunan wannan tsari? Shin ko dai da ma can tsarin naka shi ne a kara kudin man fetur ta wata hanya domin ta haka ne kurum za a wadatar da shi a cikin kasa, amma kuma tallafin na nan ba a fasa mika wa ’yan Jari-Hujjar da Kamfanin NNPC ba? An dai sake diba daga hannun talaka, a mika wa masu hannu da shuni? To ina amfanin badi ba rai?
Ba wannan kadai ba ya Shugaba Buhari! Shin ka taba tambayar kanka irin halin da talakawan kasar nan ke ciki dangane da tashin gwauron zabo da kayayyakin masarufi ke yi tun hawanka mulki, ba wai kawai fadar da kake yi na cewa ka san halin da ake ciki ba? Na fadi haka ne domin na san ba kasuwa kake zuwa ba, ba ka kuma zuwa mahauta, ba ka kuma ziyartar dan tireda ko gyartai da mai gyaran takalmi ko mai yankan kumba. Haka ba ka shiga motar haya ko shatar mota don daukar kaya daga gona. Haka kuma ba ka biyan kudin wutar lantarki ko sayen magani a kemis, bare uwa-uba kuma na san ba ka biyan kudin makarantar yara, bare kuma dinka musu kayan makaranta da na bukukuwan addini ko makamantan haka. Ba ka yin wadannan abubuwa a zahiri, domin wannan ai kuri’ar talaka ta raba ka da su, ta bar talakan da jangwam!
Za mu ci gaba