Shugaba Buhari! Kunnenka nawa? (1)
Kwanakin baya ne na tura sako a kafar sadarwa ta facebook cewa ina son in gana da kai, mu gaisa, domin mun dade ba mu gana ba, a tsawon zamani. Na yi kurman zance ne, wato ban fadi abin da nake so bayan gaisuwar ba, wanda ya sa wadansu ke ganin cewa kila wani mukami […]
Kwanakin baya ne na tura sako a kafar sadarwa ta facebook cewa ina son in gana da kai, mu gaisa, domin mun dade ba mu gana ba, a tsawon zamani. Na yi kurman zance ne, wato ban fadi abin da nake so bayan gaisuwar ba, wanda ya sa wadansu ke ganin cewa kila wani mukami nake nema ko wata kwangila ko wata alfarma da ganinka zai iya samarwa. Duk da cewa ban amsa wa wadancan mutane ba, na san wadansu sun riga sun yanke hukunci kan irin abin da nake son ganinka a kai, musamman kamar yadda wani ya aiko min ta akwatin sako, “Me kuma kake so da ganin Shugaba Buhari, alhali kana daga cikin kalilan da ba su zabe shi ba?”
Wannan sako shi ya sa na ga ya dace in sake bibiyar dangantakata da kai da kuma yadda nake kallonka da siyasarka da mulkinka da kuma damar da nake da ita a matsayin dan Najeriya na zabi duk wanda ya kwanta min a rai a matsayin Shugaban Najeriya.
Tabbas ban zabe ka ba, a zaben da ya wuce na kuma bayyana dalilaina na yin haka tun kafin a yi zaben, wadanda kuma ban canja su ba har ranar jefa kuri’a, kuma na tabbata ni da kai mun san cewa ba laifi ba ne idan zabin dan kasa a lokacin hada-hadar neman kuri’a ta sha bamban da ta yawancin jama’a kila ma aka jefa kuri’ar har mutum ya ci kubeji, kamar yadda na yi a zaben 2019.
Duk wannnan ba shi ne matsalar ba, zancen da ya dace a yi shi ne ko dan kasa da bai zabe ka ba, bai da hurumin da zai nemi ya ganka ku gaisa ko ya ba ka shawarar da yake ganin za ta fidda kasa ko al’ummarta? Na san ba haka tunaninka yake ba, amma duk da haka na ga ya dace in yi fashin baki na dalilaina na neman mu gana, domin mu gaisa, inda daga nan in dama ta samu, na amaye wasu abubuwa da suke damuna game da yanayin mulki da siyasar kasar nan a halin yanzu.
Abin da zan yi a wannan karo shi ne na waiwayi baya game da rayuwata da kai da kuma irin yadda muka hadu, muka rabu, muka sake haduwa a cikin tsawon zamani, wanda kila ta haka a gane me cikin jiya ya kunsa, yaya kuma nakudar yau take ciki, me za a iya haifa, ko kuma zai yi tsawon rai ko a’a. Kila daga wannan rubutu, wanda na sha yin irinsa a tsawon shekaru game da kai, wadansu za su samu amsar tambayoyin da ke susarsu, tunda na nemi in gana da kai.
Ya Shugaba Buhari! Zuwa yau na yi tsawon shekara 36 ke nan da nake hulda da kai, wani lokacin a kaikaice, wato daga nesa kurum nake ganinka ko jin labarinka, musamman lokacin da ka dare Shugabancin Kasar nan a shekarar 1983, kana soja, cikin kakin da ba wanda ya isa ya tanka maka ko ya ce ka yi ba daidai ba, don kai ne da wuka da nama. A lokacin ban kammala karatun jami’a ba, kuma lallai daga halin da kasar nan ta shiga a lokacin, na san mutane sun ji jiki, domin mu kanmu dalibai, mun ji jikin, ta fuskoki da dama da za mu iya kararwa. Abincin da ake ba mu kusan mu ce a kyauta a matsayin dalibai, wata sa’a har da rabin kaza kafin zuwan mulkinka, muka neme shi sama ko kasa, sai dai mu sanya kudi mu saya, kuma a lokacin an yi fatarar da kullum ke sa mu kokawa a zuci, wata sa’a kuma har a fili. Amma daga baya mun ji dadin gwamnatinka, musamman daga 1984 lokacin da ka fara saita lamura, zuwa shekarar 1985 da muke yin hidimar kasa, za mu iya cewa kasar nan ta fara ganin hasken da zai kai ta ga tudun-mun-tsira, duk kuwa da cewa an sha wuya, ba ga ’yan makaranta ba, har sauran al’ummar kasar baki daya, talakawa da masu tarin dukiya, balle kuma ’yan siyasa da ka rika daurewa, wadansu har tsawon shekara 100 a gidan kaso!
Duk da cewa mulkinka a wancan lokaci ya dace da yanayin kasar, domin kuwa ta lalace ta kowace fuska, amma wahalar da aka sha da rayukan da aka rasa da talaucewar da aka yi ba abin da wadansu za su manta da sauri ne ba. Ke nan zan iya cewa, bakin-farin-ciki ne ya kame al’ummarmu a lokacin. Shi ya sa har abada ban mantawa da abin da ya faru a lokacin muna kan hidimar kasa a birnin Yola, inda da asuba a wata rana a watan Agustan 1985 da kwamnandan sojan da ke kula da mu ya taso cikin muku-mukun safiya ya ce da mu ‘yau ba fareti za mu yi ba, na tashe ku ne in gaya muku cewa an kawar da gwamnatin Janar Buhari, ban san dalilin yin haka ba, kuma bai dame ni ba, kowa ya koma daki.’ Ban taba mantawa da yanayin da muka samu kanmu a ciki, har da sojojin da ke kula da mu, daga masu tsaki, sai masu tofin Allah-tsine, irinmu da suke masoyanka tun a lokacin hawaye muka rika zubarwa, domin mun yi amanna cewa abin da Janar Babangida ya yi maka, bai kyauta ba, ba kuma kai ne kadai bai kyauta wa ba, mu ne ya lalata wa tsari, kasar ce bai yi wa adalci ba, domin kuwa duk mai hankali yana da yakinin da ka dade a kan karagar mulki da kila kasar ta samu tudun dafawa domin ci gaba ta fuskoki da dama. Haka muka bar kanmu cikin alhini da damuwa.