Shugaba Buhari: Sabani tsakanin Gwamna da Sarkin Kano
An ruwaito Shugaba Buhari yana furta wasu kalamai a ranar Juma’ar makon jiya, a fadar Shugaban da ke Abuja lokacin da ya karbi wani ayarin ’ya’yan Jam’iyyar APC na Jihar Kano da suka hada har da sababbin zababbun ’yan majalisa a karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, inda yake cewa: “Na san matsayin irin rawar […]
An ruwaito Shugaba Buhari yana furta wasu kalamai a ranar Juma’ar makon jiya, a fadar Shugaban da ke Abuja lokacin da ya karbi wani ayarin ’ya’yan Jam’iyyar APC na Jihar Kano da suka hada har da sababbin zababbun ’yan majalisa a karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, inda yake cewa:
“Na san matsayin irin rawar da zan iya takawa a zamana na Shugaban Kasa. A bisa ga tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Kasar nan, Gwamnan Jihar Kano ma yana da nasa, in dai har batu yana gaban Majalisar Dokoki (kamar Kano) Shugaban Kasa ba ya da wani iko da tsarin mulki ya ba shi da zai iya tsoma baki. Tsarin mulkin ya kawo ni. Na rantse da shi kuma a kansa na tsaya. Amma bari in fada muku wani abu da na fahimta a kan rawar da tsarin mulkin yake magana, zaman lafiya da tsaro dole a tabbatar da su a duk inda aka samu barazanarsu. A nan zan iya amfani da damar da Kundin Tsarin Mulkin ya ba ni.”
Tun cikin watan Mayun bara, bayan Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kara kirkiro masautu hudu (Bichi, Rano, Karaye da Gaya) daga Masarautar Kano, dokar da ta ba Gwamna Ganduje damar nada wa wadancan masarautu sarakunan yanka masu daraja ta daya, ta bayyana karara a idon duniya cewa abin boye ya fito fili, a kan sabanin da aka dade ana rade-radinsa cewa zaman doya-da-manja a tsakanin Gwamnan da Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II. Sabanin da wadansu suka ce ya yi kamari tun daga lokacin da Gwamna ya gane cewa Sarki, Jam’iyyar PDP da dan takararta na neman Gwamnan Jihar, Injiniya Abba Kabir Yusuf a zaben bara yake goyon baya.
Kodayake Gwamna Ganduje ya yi ta kare matsayin da gwamnatinsa ta dauka a kan yi wa Masarautar Kano ayaga, wanda yake ta nanatawa daga lokaci zuwa lokaci, cewa ba don wata nufaka ko biyan bukatar kansa ya yi haka ba, illa sai don ci gaban jihar da al’ummarta. Yayin da wadansu suka amince, wadansu kuma har gobe ba su aminta ba, bisa la’akari da irin tuhume-tuhume da binciken zargin aikata laifuffukan da suka jibanci cin hanci da rashawa da Hukumar Karbar Korafe-Korafen Jama’a da Yaki da Cin hanci da Rashawa ta Jihar ke yi a kan Mai martaba Sarkin Kanon, tun kafin kirkiro sababbin masarautun har zuwa yanzu, sun san ba banza ba, akwai kuma inda gwamnatin jihar ta dosa. Ga irin wadancan mutane, kirkiro sababbin masarautun hudu bai zo musu da wani mamaki ba.
Irin wannan sabanin fahimta da ra’ayoyi da aka samu, sun sanya hatta wadansu da ake ganin za su iya yayyafa wa rashin fahimtar ruwa, suka rika daukar matakan da akasari suka zama wuta suka kara izawa ga al’amarin. Alal misali, masu zaben Sarkin Kano hudu (Makama da Sarkin Bai da Madaki da Sarkin Dawaki Mai Tuta) da Kwamitin Dattawan Jihar Kano da ke karkashin jagorancin Alhaji Bashir Othman Tofa, sun garzaya zuwa Babbar Kotun Jiha, inda dukkansu suka kalubalanci dokar kirkiro sababbin masarautun hudu, suna neman lallai kotun ta soke su ta kuma kori sarakunan.
Daga bisani kotun ta soke masarautun a kan hanzarin tsarin da aka bi aka gabatar wa Majalisar Dokokin Jihar daftarin dokar, cewa ya saba wa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar nan, kasancewar wanda ya gabatar da bukatar bai cancanci yin haka ba. Yanke wannan hukunci ke da wuya sai Gwamnatin Ganduje ta sake kakkabe daftarin dokar ta kuma sake gabatar da shi ga Majalisar Dokokin Jihar. ’Yan Majalisar ba tare da wani bata lokaci ba dukkansu 37, in ban da mutum 1, (a lokacin Jam’iyyar APC na da mambobi 25, PDP na da 12) suka amince da dokar, shi kuma Gwamna Ganduje ya sake nada sarakunan.
Ana cikin wannan dambarwa ce kwatsam, sai aka wayi gari da kafa wata sabuwar kungiya a kasarkashin jagorancin Farfesa Abdu Salihu na Jami’ar Bayaro, Kano, kungiyar da akasarin mambobinta ’yan bokon da suka fito ne daga karkarar jihar. Kungiyar da ita kuma ta yi maraba tare da jaddada goyon bayanta a kan kara kirkiro masarautun, bisa ga abin da ta kira zai kara kawo ci gaba a cikin hanzari a yankunansu, har ma da kara samun hadin kan mutanen jihar baki daya. Sabanin kungiyar su Alhaji Bashir Tofa da ke ikirarin cewa kirkiro masarautun zai kara kawo rashin hadin kan mutanen jihar baki daya.
Tunda aka fara wannan takun-saka tsakanin Gwamna da Sarki, hakimai 18 na tsohuwar Masarautar Kano suka rasa rawaninsu, bisa ga sun yi kememe, sun ki yin mubayi’a ga sababbin sarakunan masarautunsu. Daga cikinsu har da masu zaben Sarkin Kano. Wani abu kuma da kara kirkiro masarautun ke nunawa a kullum shi ne, irin yadda a duk lokacin da wani sha’ani ya taso a fadar sababbin masarautun, mutanen masarautun kan yi fitar farin dango wajen amsa kiran sarakunan, tare da nuna shauki da farin cikinsu. Hawan Sallah da nade-naden sababbin hakimai da sarakunan suka rika yi a masarautun, a ’yan kwanakin nan sun tabbatar da haka.
Bari in dawo kan bayanin da Gwamna Ganduje ya bayar ga manema labaran Fadar Shugaban Kasa, jim kadan bayan fitowarsu daga wajen Shugaba Buhari. Gwamnan na Kano ya ce sabanin da ke tsakaninsa da Sarkin Kano, batu ne da ya shafi kundin tsarin mulkin kasar nan, wanda za a iya gyarawa ta ruwan-sanyi. “Magana ce ta kundin tsarin mulki, tsakanin Gwamna da Sarki kowa yana aiki kan huruminsa, kuma za a kawo karshen rashin fahimtar cikin ruwan-sanyi da kuma bisa ga tanade-tanaden kundin tsarin mulki,” inji Gwamna Ganduje. Har ma ya kara da cewa “Hatta Kungiyar Dattawan Arewa ta zo kan wannan batu, muna kuma tattaunawa da su.”
Tunda aka shiga wannan rashin fahimta ake ta zargin cewa manyan kasa sun ki shiga don sasanta manyan biyu. Ni kuma na san manya da dama da tun al’amarin bai kazance ba, da suka rika sa baki, ta hanyar tuntubar manyan biyu da niyyar su mayar da wukakensu kube, amma al’amarin ya ci gaba har ya kawo haka. Kuma hakan bai wuce irin yadda kowannensu (Gwamna da Sarki) yake jin ya isa ba.
A ’yar fahimtata da batun tanade-tanaden kundin tsarin mulki a kan wannan batu, bai wuce ikon da kundin ya ba majalisun dokoki na jihohi a kan suna iya kirkiro masarautu da kuma ikon da Gwamnan Jiha ke da shi na ya nada ko ya tube Sarki ba. Buhari dai ya yi magana, fassarar tsarin mulki ake jira daga kotuna bisa ga kararrakin batun masarautun nan da ke gabansu.