Shugaba Buhari ya albarci bikin cikar Jihar Ogun shekara 40

Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da wasu muhimman ayyukan da Gwamnan Jihar Ogun Sanata Ibikunle Amosu ya gudanar a manyan gundumomi da ke fadin jihar.Shugaban ya fara ne da kaddamar da katafariyar kasuwar zamani ta Omida a Abekuta da gadar sama ta Itoku, wacce aka sanya wa sunan ’yar rajin kare hakkin mata, kana mace […]

Shugaba Buhari ya albarci bikin cikar Jihar Ogun shekara 40
Shugaba Buhari ya albarci bikin cikar Jihar Ogun shekara 40

Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da wasu muhimman ayyukan da Gwamnan Jihar Ogun Sanata Ibikunle Amosu ya gudanar a manyan gundumomi da ke fadin jihar.
Shugaban ya fara ne da kaddamar da katafariyar kasuwar zamani ta Omida a Abekuta da gadar sama ta Itoku, wacce aka sanya wa sunan ’yar rajin kare hakkin mata, kana mace ta farko da ta fara tuka mota a Najeriya, Olufunmilayo Ransome-Kuti. Ya kuma kaddamar da rukunin gidajen ma’aikatan jihar, wanda aka sanya wa suna Shugaba Muhammadu Buhari da kuma makarantun zamani. Hakazalika ya aza harsashin ginin rukunin gidajen alkalan jihar.
Shugaban ya yaba wa gwamnan jihar, Sanata Ibikunle Amosu bisa wannan gagaruman ayyukan.
Tuni dai gwamnan ya gabatar da manyan ayyuka arba’in da ya gudanar, wadanda aka kaddamar a makon bikin cikar jihar shekaru 40 da kafuwa. Kana Shugaba Buhari ya kaddamar da sabuwar alamar taswirar jihar a hukumance.
A cewar Babban Jojin jihar, Mai shari’a Olatokunbo Olubade, gina rukunin gidajen alkalan abin a yaba ne, domin wandanda suke amfani da su a halin yanzu an gina su ne fiye da shekaru 40 kafin kafuwar jihar.
Jihar Ogun ta yi fice  a fannoni daban-daban, ita ce jiha mafi noman rogo da samar da siminti a duk fadin Naeriya kana tana da dinbin kanfanoni da ma’adanan karkashin  kasa kuma mashiga ce ga birnin Legas, domin ko ta ina za ka Legas sai ka ratsa ta jihar.
An samar da Jihar Ogun ne a lokacin mulkin Janar Murtala Muhammed, inda wanda aka kirkire ta daga Jihar Kudu maso yamma, kana garin Abekuta ya zamo babban birnin jihar. An fitar da Ogun da Oyo da Ondo a wannan lokacin duk daga Jihar Kudu maso yamma.  Jihar ta samu sunanta ne daga sunan wani kogi da ke ciki jihar, mai suna Ogun.