Shugaba Buhari ya ba da tallafin Naira miliyan 500 ga masu kananan jari a Adamawa

Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da tallafin Naira miliyan 500 ga masu kananan karfi a Jihar Adamawa. Shugaba Buhari ya raba kudin ne daga watan Agusta bara zuwa Agustan bana don cika alkawuran da ya dauka na taimaka wa marasa karfi inda ake aika kudaden ta asusun jama’a. Shugaba mai kulawa da shigar kudin a […]

Shugaba Buhari ya ba da tallafin Naira miliyan 500 ga masu kananan jari a Adamawa

Muhammadu-Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da tallafin Naira miliyan 500 ga masu kananan karfi a Jihar Adamawa. Shugaba Buhari ya raba kudin ne daga watan Agusta bara zuwa Agustan bana don cika alkawuran da ya dauka na taimaka wa marasa karfi inda ake aika kudaden ta asusun jama’a.

Shugaba mai kulawa da shigar kudin a Jihar Adamawa, Mista Zhegun Joseph ne ya bayyana haka a zantawa da manema labarai a ranan Litinin da ta gabata.

“An fara saka kudaden a asusun bankuna na jama’a tun a watan Agustan shekarar 2017, inda  mutum 8,653 suka amfana daga kananan hukumomi shida. A kowane gida cikin wadanda suka yi rajista suna karbar Naira dubu biyar a duk wata,” inji shi.

Ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin sake yin rajistar wadansu marasa karfi da ke Jihar Adamawa. “Mun sake bayar da wani tallafin ga mutum 13,520,” inji shi.

Ya ce jama’ar da suka amfana da tallafin kudaden sun nuna farin cikinsu da kuma nuna godiya ga Shugaba Muhammadu Buhari. Ya ce bangarorin da suka amfana daga wannan tallafin sun kunshi kananan hukumomin Girei da Song da Numan da Lamurde da Madagali da kuma Michika.

 

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa