Shugaba Buhari ya ce zai sake tsayawa saura ma za su fito
“Yan Najeriya suna ta yawan kiraye-kirayen a kan ko zan tsaya ko a`a. Hakan ta sa na ga ya kamata in bara. Muna da abubuwa da dama da muke so mu maida hankali akai, kamar batun tsaro, ayyukan gona, tattalin arzikin kasa, yaki da cin hanci da rashawa da sauransu.Muna bukatar mu mayar da hankali […]
“Yan Najeriya suna ta yawan kiraye-kirayen a kan ko zan tsaya ko a`a. Hakan ta sa na ga ya kamata in bara. Muna da abubuwa da dama da muke so mu maida hankali akai, kamar batun tsaro, ayyukan gona, tattalin arzikin kasa, yaki da cin hanci da rashawa da sauransu.Muna bukatar mu mayar da hankali akansu. Siyasa kuma ba ta kamata ta zama abin da za ta kautar da mu akansu ba. Mafi yawan `yan kasa, suna yabawa da abubuwan da muke yi, wannan kuma shi ne dalilin da zai sanya in sake neman ku zabe ni. Shugaba Muhammadu Buhari ke nan yayin sake jaddada aniyarsa ta zai tsaya neman takarar shugabancin kasar nan a ranar Larabar makon jiya a birnin Landan, lokacin da yake maraba lale wajen karbar bakuncin babban limamin Cocin kasar Birtaniya Achibishop na Kantibore, wanda ya kai mai ziyarar ban girma a masaukinsa a cikin wata ziyarar kashin kai da kuma aiki da shugaba Buhari ya fara a kasar ta Birtaniya a ranar Litinin din makon jiyan.”
Kafin shugaba Buhari ya bayyana aniyarsa ta zai sake neman shugabancin kasar nan a zaben shekarar mai zuwa wato 2019, kiraye-kirayen jama`ar kasa ya yi nisa akan lallai sai ya fito ya fayyace ma `yan kasa akan zai sake tsayawa ko a`a. Gwamnonin jam`iyyarsa ta APC su 24, a ranar 22 ga watan Fabrairun da ya gabata a wata ganawa da su ka yi da shugaban kasar a fadar gwamnati a Abuja, sai da su ka neme sa akan lallai sai ya fito ya bayyana aniyarsa ta zai sake tsayawa takarar. Kai karewa ma da karau gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje sai da ya yi barazanar cewa muddin shugaban kasar ya ki amsa kiransu, to kuwa za su gurfanar da shi gaban kuliya, don kotu ta tilasta masa ya amsa wannan kira na su.
Wasu `yan kasa musamman mabiya da magoya bayan jam`iyyar APC da ma masu tsananin kaunar shugaba Buhari sun ta kiraye-kirayen lallai sai ya fito neman wannan takara a karo na biyu da kundin tsarin mulkin kasar nan ya halasta masa. Duk bayan wadancan kiraye-kiraye na bayyane, a gefe daya kuma an cewa shugaba Buhari, ya fadada shawararsa zuwa ga makusanta kuma amintattunsa da ma ba sa cikin gwamnati ko harkokin siyasa, da su ka karfafa masa gwiwar da lallai ya sake neman takarar a karo na biyu.
Mai karatu, kar ka manta, daukar wannan matsayi da shugaba Buhari ya yi cike yake da kalubale iri-iri a ciki da wajen jam`iyyarsa ta APC. Kowa dai ya ji irin kiraye-kirayen da tsofaffin shugabannin kasar nan wato Cif Olusegun Obasonjo da Janar Ibrahim Badamasi Babangida su ka rika yi wa shugaba Buhari akan kar ya sake neman wannan takara. Ta kai ma shugaba Obasanjo da ya taka gagarumar rawa wajen kawar da gwamnatin tsohuwar jam`iyyarsa ta PDP da kuma ganin nasarar shugaba Muhammadu Buhari da jam`iyyar APC a zabubbukan 2015, sai da ya kai fagen yana cewa wannan gwamnatin ta Buhari ta gaza don a fadarsa ba ta tsinanan komai ba, kamar dai yadda tarihi zuwa yanzu ya tabbatar da cewa Cif Obasanjo ya yi kaurin suna wajen ganin ya tunbuke dukan gwamnatin da ta ki taka rawar kidansa.
Shi kuwa tsohon shugaban kasa Janar Babangida, bayan shawara kamar yadda ya kirata da ya bayar ga shugaba Buhari akan kar ya sake tsayawa takarar neman shugabancin kasar nan a shekara mai zuwa, daga bisani kuma ya koma yana kamfen din lallai lokaci ya yi da tsofaffin jini za su ja baya su ba matasan kasar nan damar su mulki kasar nan. Mai karatu ka ji a yau Janar Babangida ya san da matasan kasar nan za su iya taka rawa, bayan a zamanin mulkinsa na shekaru kusan bakwai 1985 zuwa 1992, ba irin wasan kurar da bai yi ba da sabbin da tsofaffin jini na `yan siyasar kasar nan akan zai basu mulki, amma daga karshe tusa ta karewa budari ya sauka ba tare da ma iya saita alkiblar siyasar kasar nan, bare a yau a iya gane akan su wa ya karkata da aniyarsa ba don biyan bukatar kansa ya ke ba.
A duk lokacin da na ji kiraye-kiraye da soke-soken gwamnatoci musamman gwamnatin Buhari daga wadancan tsofaffin shugabannin kasa guda biyu, ko na kusa da su, na kan yi dariya, domin na san cewa kira ne na adawa ba na neman gyara ba. Shi kuwa kiran adawa, kira ne na kawar da wanda ke kan mulki don wani naka da za ka iya juya shi ya hau, ko kuma ka rika tinkahon jam`iyyarka ke mulki, wanda a tsari irin na siyasar wannan zamani yin hakan halas ne.
Tun bayan da shugaba Buhari ya bayyana aniyarsa ta zai sake tsayawa takara bayan soke-soken wadancan shugabanni wasu ‘yan adawa na ganin shugaban bai kamata ya sake neman a tsayar da shi ba bisa ga abin da suke gani babu wani aiki daya tilo da shugaban ya kirkiro ya kuma kammala a cikin shekara 3, da yake kai yanzu. Amma magoya bayansa suna ganin ya yi gagaruman ayyukan da ba wani shugaban da tunda aka fara wannan mulkin na dimukradiyya yau kusan shekara 20, da ya yi irin wanda ya yi, kasancewar shi shugaba Buhari ya yarda da cewar babbar nasarar kowace gwamnati shi ne dorawa daga kan inda ta samu kanta, tsarin da shi shugaba Buhari yake kai.
Na san cewa bayyana wannan aniya da shugaba Buhari ya yi, ba ita ce karshen magana ba akan ya samu tutar tsayawa jam’iyyarsa takarar neman shugabancin kasar, kasancewar an ji Kakakin jam’iyyar Malam Bolaji Abdullahi yana cewa kofa a bude take ga sauran masu sha’awar tsayawa jam’iyyar takara su nemi hakan. Amma ni nasan wannan magana ce ta siyasa a yau ba sai gobe ba, ba na jin jam’iyyar ta APC ta na da gwarzon dan takara da wasu ‘yan kasa ma’abota hankali suke ma kallon ya fara sanya kasar nan akan tubar farfado da kima da mutuncinta a cikin gida da waje, kamar shugaba Buhari, su kansu sauran jam’iyyun siyasun adawa sun san da haka. Uwa uba kuma har gobe zunzurutun talakawa da suke kada kuri’a a kasar nan suna nan tare da shugaba Buhari duk kuwa da kasancewar suke shan bakar wahalar matsin tattalin arzikin kasa da kasar take ciki. Ma’ana dai irin wadancan talakawa sun fara gane cewa gwamnatocin baya su ka jazawa kasar nan wadannan masifu na faduwar tattalin arzikin kasa da rikice-rikicen fulani makiyaya da manoma da na yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa da sace-sacen shanu da uwa uba rikicin Boko Haram, shi Buhari gyara kawai ya ke.
Saura da me ya rage yanzu, shi ne lallai shugaba Buhari muddin ya na so ya kai ga nasara sai ya sake takun da yake akan dangantakar bangaren Zartarwa da na Dokoki da kuma salon yakinsa na cin hanci da rashawa, da tun da aka fara shi ‘yan adawa da ma wasu ‘yan kasa suke kallon ba a taba ‘yan jam’iyyar shugaban kasar ta APC duk kuwa da irin zargin da ake masu da su ma su na da kashi a gindinsu.