Shugaba Buhari ya ci gaba da tafiya kasashen waje ko ya tsaya a gida?

Shugaban kasa Muhammad Buhari, ya zuwa yanzu da rantsar da shi ya yi tafiye-tafiye zuwa kasashe daban-daban har hudu. Wasu na ganin bai kamata ya yi ta tafiye-tafiye haka ba, ya zauna Najeriya ya gudanar da mulkinsa, a yayin da wasu kuma suke ganin ya ci gaba da tafiye-tafiyensa tun da duk aiki ne. Abin […]

Shugaba Buhari ya ci gaba da tafiya kasashen waje ko ya tsaya a gida?
Shugaba Buhari ya ci gaba da tafiya kasashen waje ko ya tsaya a gida?

Shugaban kasa Muhammad Buhari, ya zuwa yanzu da rantsar da shi ya yi tafiye-tafiye zuwa kasashe daban-daban har hudu. Wasu na ganin bai kamata ya yi ta tafiye-tafiye haka ba, ya zauna Najeriya ya gudanar da mulkinsa, a yayin da wasu kuma suke ganin ya ci gaba da tafiye-tafiyensa tun da duk aiki ne. Abin tambaya a nan shi ne, shin me ya kamata shugaban ya yi? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana:

Tafiyar na da muhimmanci – Hamza Lukman

Kabir Yayo Ali, a Ibadan

Hamzah Lukuman: “Ziyarar kasashen waje da Shugaba Muhammadu Buhari yake yi tana da muhimmancin gaske fiye da zaman dirshan a cikin gida. Idan muka tuna tun kafin ya zama shugaba yake fada wa ’yan Najeriya cewa matsalar tsaron kasa tana daga cikin muhimman abubuwan da zai fi mayar da hankali a kai. To, wadannan ziyarce-ziyarce da yake yi suna daga cikin hanyoyin da za su taimaka masa shawo kan matsalar tsaro a kasar nan. Ana shigo da makamai cikin kasar nan ta hanyoyi daban-daban wanda dole ne ya nemi hadin kan kasashe makwabta domin yin maganin hakan. Idan babu kyakkyawan tsaro, to kuwa ba zama lafiya balle a samu ci gaba.”

Ba zama gida ne kadai aiki ba -Shaikh Hassan

Hamza Aliyu, a Bauchi

Sheikh Hassan Usman Zango: “Tabbas tun lokacin da Muhammdu Buhari ya kama aiki ya je kasashen Nijar, Chadi, Jamus da kuma kasar Afirika ta Kudu. Zaman lafiya shi ne babban sinadirin da ke samar wa dan Adam natsuwa kuma idan babu shi babu abin da zai wakana a Najeriya. A fahimtata yana yin wadannan tafiye-tafiye domin ganin cewa an shawo kan masu tada kayar baya a yankin Afirika. Kuma ina tabbatar wa al’umma cewa idan bai yi tafiye-tafiyen ba, ta yaya za a magance wannan matsala ta masu tada kayar baya?
Masu cewa Buhari ya zauna a gina ya ci gaba da gudanar da aikinsa sun jahilci rayuwa kuma sun jahilci duniyar da muke rayuwa a cikinta.”

Mun fi bukatarsa a gida – Isah Moyi

John Wada, a Lafiya

Alhaji Isah Moyi: “Ba shakka tafiyar da Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ke yi zuwa kasashen waje ta da ce. Don ba wai yana yi ne don yana sha’awar yin haka ba. Yana yi ne don aikinsa ne sai dai shawarar da zan ba shi ita ce, wasu daga cikin tafiye-tafiyen da ya lura ba su da mahimmanci sosai ba, ya rika tura wakilansa su wakilce shi. Don mu a gida Najeriya mun fi bukatarsa sosai a halin yanzu. Musamman ka ga abubuwan da suke faruwa a Majalisar Dattawa a kasar nan, ya kamata ya himmatu wajen warware lamarin don ba shi damar cin nasara a wannan mulki nasa.”

Babu laifi ga tafiyar amma… – Abubakar Zubairu

Kabir Yayo Ali, a Ibadan

Abubakar Zubairu: “Wannan ziyara da Shugaba Muhammadu Buhari yake yi zuwa kasashen ketare tana da muhimmanci musamman a kasashen da ke makwabtaka da Najeriya kamar Chadi da Nijar da Kamaru, wadanda su ma ba su tsira daga matsalar Boko Haram ba. Amma ya kamata ya dakata da ziyartar kasashen Turai wadanda nake ganin ba za su iya yi mana magani cikin lokaci kamar yadda za mu yi wa kanmu ba. Ziyarar da ya kai zuwa kasar Afirika ta Kudu tana da muhimmanci domin shugabannin kasashen Afirika ne suka yi taron da za su yi maganin tabarbarewar tsaro a kasashen nasu.”

Wajibi ne yin tafiye-tafiyen – Musa Aliyu

Hamza Aliyu, a Bauchi

Malam Musa Aliyu Jahun: “Abin da zan fada a nan shi ne, ya zamo wajibi a kan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wadannan tafiye-tafiye, domin ta haka za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya da sauran kasashen makobta. Idan Najeriya ta zauna lafiya kowa zai zauna lafiya a Afirika. Kuma tafiye-tafiyen na daya daga cikin wani bangare na ayyukan raya kasa. Masu cewa ya zauna a gida ya ci gaba da aiki ina ganin watakila sun jahilci abubuwan da ke faruwa ne a duniya saboda haka suke wadannan maganganu na rashin hankali da sanin ya kamata.”

Ya ci gaba da tafiye-tafiyen – Muhammad Idasho

John Wada, a Lafiya

Malam Muhammed Idasho: “A nawa ra’ayi dai ya da ce Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ya ci gaba da halartar wadannan tarurruka don ai yana yi ne saboda amfanin kasar nan. Kamar yadda Hausawa ke cewa, tafiya da kai ya fi sako. Saboda haka ban goyi bayan cewa ya rika aika wasu su halarci tarurruka a kasashen waje ba. Don akwai wasu abubuwa da idan za a fada a wurin idan yana nan da kansa dole a fada amma idan ya aiki wani ba za yi maganar ba. Saboda haka na goyi bayan ya ci gaba da halartar tarurrukan don yana yi ne saboda mu ’yan kasar nan baki daya.