Shugaba Buhari ya dage ziyarar zuwa Imo

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dage ziyarar kaddamar da aiki ta kwana daya da zai kai jihar Imo a yau Talata. Shugaban zai kaddamar da wasu sabbin ayyuka da gwamnatin jihar Imo ta yi. Sakataren watsa labaran Gwamnan Jihar Imo Sam Onwuemeodo ne ya bayyanawa manema labaran hakan a yau, ya ce an dage ziyarar […]

Shugaba Buhari ya dage ziyarar zuwa Imo

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dage ziyarar kaddamar da aiki ta kwana daya da zai kai jihar Imo a yau Talata.

Shugaban zai kaddamar da wasu sabbin ayyuka da gwamnatin jihar Imo ta yi.

Sakataren watsa labaran Gwamnan Jihar Imo Sam Onwuemeodo ne ya bayyanawa manema labaran hakan a yau, ya ce an dage ziyarar ne saboda  shugaban kasa yana shirin dawowa daga kasar Saudiyya bayan yin Umrah.