Shugaba Buhari ya goyi bayan El-Rufai kan koran malamai
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna goyon bayansa ga Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai bisa kudurinsa na koron malamai 21,780, wadanda suka fadi jarabawar da jihar ta shirya domin gwada cancantarsu. Shugaba Buhara ya yi wannan jawabin ne a Abuja a lokacin taro na musamman da ‘yan Majalisar Zantarwa a kan […]
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna goyon bayansa ga Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai bisa kudurinsa na koron malamai 21,780, wadanda suka fadi jarabawar da jihar ta shirya domin gwada cancantarsu.
Shugaba Buhara ya yi wannan jawabin ne a Abuja a lokacin taro na musamman da ‘yan Majalisar Zantarwa a kan matsalolin da ke fusakantar bangaren ilimi a Najeriya, da kuma yadda za a magance su.
Shugaban ya kwatanta yadda ake samu a lokuta da yawa inda babu banbamci tsakanin malaman da dalibansu.
Shugaban ya nuna yadda harkan ilimi ya tabarbare a kasar, wanda yanzu haka kusan yara Miliyan 13.2 ne suke zaune ba sa zuwa makaranta.
Ministan ilimi, Malam Adamu Adamu ya ce ana bukatar Naira triliyan daya a duk shekara na tsawon shakara hudu kafin su cika alkawarin da suka dauka a bangaren.