Shugaba Buhari ya ki sa hannu kan Dokar Zabe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki sa hannu a kan kudirin Gyara Dokar Zabe na 2010, wanda ya bayar da dalilin wasu “murdaddun batutuwa” da ba a warware ba a lokacin da aka sake aiko masa da kudirin daga majalisa. Mai taimaka wa Shugaban kasa kan Harkokin Majalisar Dattawa, Ita Enag ne ya bayyana haka […]

Shugaba Buhari ya ki sa hannu kan Dokar Zabe
Shugaba Buhari ya ki sa hannu kan Dokar Zabe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki sa hannu a kan kudirin Gyara Dokar Zabe na 2010, wanda ya bayar da dalilin wasu “murdaddun batutuwa” da ba a warware ba a lokacin da aka sake aiko masa da kudirin daga majalisa.

Mai taimaka wa Shugaban kasa kan Harkokin Majalisar Dattawa, Ita Enag ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar a Abuja kamar yadda BBC ta jiyo shi yana fada.

Ya ce Shugaban kasa ya sanar da Majalisar Dattawa hakan tun a ranar 30 ga Agusta.

Shugaban kasa, ya ki sa hannu ne a kan kudirin Gyara Dokar Zabe, saboda har yanzu akwai sauran rina a kaba, domin akwai batutuwan da majalisa ba ta tabo ba a lokacin da ka gabatar da kudirin.

“Shugaban kasa ya gayyaci Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai domin su zauna a warware zare da abawar da suka hargitsa batun dokar zaben, domin shi ma ya gaggauta sa wa dokar hannu,” inji shi.

Ya ce akwai batun abin da  sashe na 87 (14) na dokar zaben ya tanada, wanda ya yi magana kan takamaimen ranakun da za a gudanar da zabubbukan fid da-gwani na jam’iyyun siyasa.

“Domin hakan yana iya kawo cikas ga INEC, yadda zai zama saura kwana tara kawai ya rage ga hukumar zaben ta kammala hada sunayen ’yan takara na jam’iyyun siyasa da dawainiyar gudanar da zaben fid da gwanin jam’iyyun siyasa har 91.”

Ya ce majalisar ta yi gaggawar aike wa Shugaban kasa kudirin dokar, ba tare da gyara sashen doka na 31 da 34 da na 85 ba.

 

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa