Shugaba Buhari ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnati
A ranar Larabar da ta gabata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Boss Mustapha fadarsa dake Abuja. Nadin tare da rantsar da sabon sakataren gwamnatin ya zo kwan guda bayan korar tsohon Sakataren Gwamnatin, Lawan Babachir bayan da kwamitin bincike karkashin Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya mika rahotansa […]
A ranar Larabar da ta gabata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Boss Mustapha fadarsa dake Abuja.
Nadin tare da rantsar da sabon sakataren gwamnatin ya zo kwan guda bayan korar tsohon Sakataren Gwamnatin, Lawan Babachir bayan da kwamitin bincike karkashin Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya mika rahotansa bisa zarge-zargen sama da fadi da Majalisar Dattawa ta bankado.
Tuni sabon sakataren ya kama aiki, har ma ya samu damar shiga zaman majalisar zartarwar kasar a ranar Larabar, inda ya zauna kusa da kujerar mataimakin shugaban kasa.
Kafin nadin nasa, Boss Mustapha shi ne Shugaban Hukumar Kula da Hanyoyin ruwa na cikin gida wato NIWA. Haka kuma lauya ne, dan siyasa kuma dan kasuwa. Shi ne kuma sakataren kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a shekarar 2015, kuma mamba ne na kwamitin amintattu na Jam’iyyar ta APC.
An bayyana Mista Mustapha a matsayin kwararre a fannin aikin gwamnati da na kamfanoni. Haifaffen Jihar Adamawa ne kuma ya yi karatunsa na sakandare a garin Hong, ya yi kwalejin kimiyya ta Maiduguri, ya yi karatun digirinsa a fannin shari’a a Jami’ar Ahmadu Bello Zaria, ya kuma tafi makarantar koyon aikin shari’a a shekarar 1980 zuwa 1981.
Bayan kammala bautar kasarsa a hedikwatar rundunar sojin Najeriya, sai ya fara aiki da wani kamfanin kasar Italiya dake Najeriya, Sotesa Nigeria Limited. A shekarar 1983 kuma ya koma aiki da kamfanin lauyoyi na Onagoruwa & Co dake Lagos.
Daga bisani kuma ya bude kamfaninsa na aikin lauya, ‘Messrs Mustapha & Associates’. Haka kuma ya taba zaman mamba na wani kwamitin gudanarwa na wucin-gadi a hukumar PTF, daga 2000 zuwa 2007. Bayan ya bar PTF ne ya zama daya daga cikin manyan masu hannun jari na kamfanin Adroit Led, ya kuma zama mamba na majalisar dokoki karkashin mulkin soja daga shekarar 1988-1989.
Ya shugabanci jam’iyyar PSP ta tsohuwar Jihar Gongola a shekarar 1989 zuwa1 990, ya kuma shugabanci jam’iyyar SDP daga shekarar 1990 zuwa 1991. Ya tsaya takarar gwamnan Adamawa a shekarar 1991. Ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar ACN na kasa daga 2010 zuwa 2013. A shekarar 2007 kuma ya zama mataimakin shugaban kungiyar yakin neman zabe na dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar ACN