Shugaba Buhari ya san na-yi a kan mukarrabansa

“Na nemi ganawa da mai girma Shugaban kasa bayan kammala taron Majalisar zartarwa ta kasa na ranar Laraba 11-10-2017, inda na sanar da mai girma da baka irin matsalolin da ke tattare da mayar da Alhaji Abdurrashid Abdullahi Maina a kan mukaminsa, musammman irin bata sunan da ya ka iya jawo wa matsayin wannan gwamnati […]

Shugaba Buhari ya san na-yi a kan mukarrabansa

“Na nemi ganawa da mai girma Shugaban kasa bayan kammala taron Majalisar zartarwa ta kasa na ranar Laraba 11-10-2017, inda na sanar da mai girma da baka irin matsalolin da ke tattare da mayar da Alhaji Abdurrashid Abdullahi Maina a kan mukaminsa, musammman irin bata sunan da ya ka iya jawo wa matsayin wannan gwamnati na yaki da cin hanci da rashawa.” Wadannan kalamai na daga cikin kalaman da Uwar- gida Winfred Oyo-Ita Ekanem shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya ta bayyana a cikin wasikar da ta mikawa ta hannun shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya bisa ga umarnin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, bayan da ta bayyana a kunnen duniya cewa an mayar da Alhaji Maina aiki tare da karin girma zuwa Darakta da ya shantake hankali.

Uwargida Oyo-Ita, ta yi cacar baka da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Alhaji Abba Kyari jim kadan kafin a fara taron Majalisar zartarwa na Larabar wancan makon wato2-11-2017, inda har aka jiyo ta, tana cewa me za ta ji tsoro yanzu, tunda ta kai magaryar tukewa akan mukamin aikin gwamnati a matsayinta na shugabar ma’aikata. 

Duk da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya tsawatar wa jami’an biyu, amma Uwargida Oyo-Ita tayi ta daga muryarta akan batun. Wannan sa’insa ita ce ta baya-bayannan da ta bayyana tsakankanin mukarraban gwamnatin sShugaba Muhammadu Buhari, tun bayan da ta bayyana gwamnatin ta dawo da Alhaji Abdurrashid Abdullahi Maina akan mukaminsa.     

Shi dai Alhaji Maina shi ne shugaban kwamitin musamman akan kudaden fensho, musamman na ‘yan sandan kasar nan da tsohon shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya nada a wannan mukamin a cikin shekarar 2010. Bayan tafiya ta yi tafiya ne ganin abubuwa sun fara sukurkurcewa akan sha’anin kudaden fenshon ‘yan sandan, a shekarar 2013, sai Rundunar ‘yan sandan ta kasa ta bayyana tana neman Alhaji Maina ruwa a jallo akan kudaden fensho da su ka kai N195b. Su ma kwamitin hadin gwuiwa na ma’aikatun gwamnati da na kula da mulkin Jihohi da kananan Hukumomi na Majalisar Dattawa da su ka bi did-dikin waccan badakalar salwantar biliyoyin Naira na kudaden fensho,  sun tabbatar da Maina na da hannu a cikin al’amarin. Ita ma hukumar yaki da ta’annati da kudaden jama’a wato EFCC, a shekarar 2015, ta bayyana tana neman Alhaji Maina ruwa a jallo akan badakalar yin sama da fadi da kudaden fenshon da su ka kai N195, kamar dai yadda `yan sandan da Majalisar Dattawan su ka yi zargi tun farko. Jin wannan nema ya yi yawa ya sanya a shekarar 2015, din su ka sanya Alhaji Maina ya arce ya bar kasar nan, a lokacin yana rike da mikamin Mataimakin Darakta. Kwatsam a `yan kwamakinnan, bisa ga kulle-kullen wasu mukarraban shugaba Buhari, irinsu Laftanar Janar Abdurrahaman Bello Danbazau Ministan Al`amurran cikin gida da Ministan Shari`a kuma babban Lauyan gwamnati Malam Abubakar Malami da shugaban ma`aikatan fadar shugaban kasa Malam Abba Kyari da Hukumar daukar ma`aikata ta tarayya, su kai kutu-kutun dawowar Alhaji Maina bakin aiki kuma a mukamin Darakta a ma’aikatar Al’amurran cikin gida inda dama daga nan ya tafi aikin musamman akan kudaden fenshon.

Duk da lokacin da shugaba Buhari ya fara samun labari Alhaji Maina ya dawo bakin aiki, wanda a lokacin ya bada umarnin lalle a gaggauta sallamar Maina daga bakin aiki kuma shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya da ta mika masa cikakken rahoton yadda aka yi Alhaji Maina ya dawo bakin aiki ta hannun Malam Abba Kyari, amma yanzu bisa ga abinda ya bayyana koda tsakanin Uwargida Oyo-Ita da Malam Abba Kyari, to kuwa ko shakka babu shugaba Buhari yana da cikakkiyar masaniyar yadda aka yi Alhaji Maina ya dawo bakin aiki. karewa ma da karau a taron da su ka yi da manema labarai a Kaduna bayan bayyanar sake koran Alhaji Maina, iyalan Alhaji Maina sun yi zargin cewa shugaban kasa Buhari ya gayyato dan uwansu don ya zo ya taimka masa cikin yaki da cin hanci da rashawa na gwamnatinsa.  Baya ga wannan abin kunya da mukarraban gwamnatin Buharin su ka jefata akan batun Alhaji Maina, akwai kuma wasu sa’insar kwancema Gwamnatin Buharin zane a kasuwa da wasu mukarraban gwamnatin Buharin suka shiga yi wa junansu, a ‘yan watannin nan. Alal misali, a kwanakin bayan an ji irin yadda karamin Ministan albarkatun man fetur Dokta Ibe Kachikwui ya aika wa shugaban kasa wata wasika, inda a ciki yake karar Manajin Daraktan Kamfanin man fetur na kasa Injiniya Maikanti Baru da yin watsi da ka’idojin bada kwangila da ma uwa uba kin bin umurnin shi Ministan cikin tafiyar da Kamfanin NNPC, zarge-zargen da Injiniya Baru ya musanta. Ita kanta Uwargidan shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari wanda acan baya an ji ta a wata hira da ta yi da sashen Hausa na BBC na kokawa da irin yadda wasu da ta kira ‘yan shan kai su su ka kankane mulkin mijin na ta, ba wadanda aka sha wahalar yakin neman zabe da su ba. To a kwanan nan ma Hajia Aisha din ta sake barawa inda ta koka akan duk da irin makudan kudaden da ake warewa wajen tafiyar da assibitin da ke fadar shugaban kasa, amma ta kai yanzu ko sirinjin yin allura bare kwayoyin Fanadol babu a asibitin. 

Haka wannan labari ya ke akan duk irin yadda shugaba Buhari ya ke son Majalisar Dattawa ta tabbatar masa da nadin Alhaji Ibrahim Magu a matsayin cikakken shugaban Hukumar EFCC, bayan mika shi da ya yi har sau biyu, amma rahotan Hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS da ta zargi Alhaji Magu cewa ba shi da kimar da zai shugabanci Hukumar ta EFCC, a haka din kuma ake zaune, shi ma Ministan Shari’a Malam Abubakar Malami su na nasu takun sakar da Magu akan wai Magun ne ya yi sanadiyyar dakatar da kasar nan daga cikin kungiyar kasashen duniya 135, da suke  yaki da cin hanci da rashawa daga nan kuma ya tilastawa Magun da lalle sai ya rinka mika ofishinsa (Minista) dukkan manyan kisa-kisan walau don hadin kai ko gurfanarwa gaban shari’a.

Akwai irin wadannan sa-in-sa da dama a tsakanin mukarraban Gwamnatin Buhari da rashin fili ba zai bari in kawo ba. Amma dai abin la’akari da shi a nan, bai wuce in ce lokaci ya yi da Shugaba Buhari zai rinka ladaftar da mukarrabansa, ta yadda za su daina gurgurta tafiyar gwamntainsa da har gobe talakawan kasar nan suke matukar kaunarta. Alal misali, yayar wannan jaridar ta ranar Lahadi 29-10-2017, ta gabatar da wata hira da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido na jam’iyyar PDP, inda yake bayyana irin abin da ya kamata talakawa su yi wa Shugaba Buhari a zaben 2019, wato ma’ana kar su zabi Buharin. Amma daga cikin makaranta jarida 30, da suka maida martani ga kiran Sule Lamido kamar yadda jaridar ta buga a ranar Lahadi 05-11-2017, mutane 8 kadai suka goyi bayan kiran Sule Lamidon sauran 22, su na tare da Buhari. Mai karatu ka ga ke nan ko yau za a je zabe talakawan kasa suna tare da shugaba Buhari.