Shugaba Buhari ya tafi Faransa (Faifan bidiyo)

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tafi kasar Faransa domin halartar taro na musamman da shugabannin kasashe 50 a kan sauyin yanayi. Shugaba Buhari ya tashi ne kai tsaye da filin sauka da tashin jiragen sama na Aminu Kano da ke Jihar Kano. A makon jiya ne dai Shugaba Buhari ya kai ziyarar aiki na kwana […]

Shugaba Buhari ya tafi Faransa (Faifan bidiyo)

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tafi kasar Faransa domin halartar taro na musamman da shugabannin kasashe 50 a kan sauyin yanayi.

Shugaba Buhari ya tashi ne kai tsaye da filin sauka da tashin jiragen sama na Aminu Kano da ke Jihar Kano.

A makon jiya ne dai Shugaba Buhari ya kai ziyarar aiki na kwana biyu Jihar Kano, sannan daga nana ya garzaya Daura, inda ya je gida. Sannan kuma daga nan yau din nan ya dawo Jihar Kano, inda ya tashi domin ya tafi Kasar ta Faransa.

Ku kalli bidiyon lokacin da Shugaba Buhari ya tashi a filin jirgin kamar yadda gidan gwamnati ta wallafa.