Shugaba Buhari ya yi alhinin rasuwar Magajin Garin Kano
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa game da rasuwar Magajin Garin Kano, Alhaji Muhammad Inuwa Wada, wanda ya rasu a ranar Larabar da ta gabata, bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.Shugaban, wanda ya aika sakon gaisuwar ta’aziyya ga iyalan mamacin, ya kuma bayyana ta bakin mai magana da yawunsa, Femi Adeshina cewa […]
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa game da rasuwar Magajin Garin Kano, Alhaji Muhammad Inuwa Wada, wanda ya rasu a ranar Larabar da ta gabata, bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Shugaban, wanda ya aika sakon gaisuwar ta’aziyya ga iyalan mamacin, ya kuma bayyana ta bakin mai magana da yawunsa, Femi Adeshina cewa yana rokon iyalan da su dauki hakurin juriya, musamman ganin cewa Magajin Kanon ya yi rayuwa mai kyau, wacce ta taimaka wa al’ummar kasa da ci gabanta baki daya. Haka kuma Shugaba Buhari ya bayyana irin ayyukan gina kasa da mamacin ya gudanar a rayuwarsa, musamman ma kasancewarsa tsohon malamin makaranta, dan siyasa, wanda kuma ya taba kasancewar minista a ma’aikatu daban-daban.
Marigayin, wanda shi ne tsohon Ministan Ayyuka, haka kuma Ministan Tsaro a lokacin Jamhuriya ta farko, ya rasu yana da shekaru 98 a duniya.
Marigayin kawu ne ga tsohon Shugaban kasa marigayi Murtala Muhammad, wanda shi ne ma ya sanya shi a aikin soja kasancewar a lokacin yana daga makusantan Firimiyan Jihar Arewa marigayi Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato.
Marigayin ya rasu ya bar matar aure daya da kuma ’ya’ya takwas da jikoki da dama. Tuni dai aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, inda Sarkin Kano Muhamamdu Sanusi II ya jagoranci Sallar jana’izar da aka gudanar a kofar kwaru, kusa da babban Masallacin Juma’a na Kano.
Jama’a da dama ne suka halarci jana’izar marigayin, wadanda suka hada da manyan ’yan majalisar sarki da hakimai da tsohon Sufeto Janar na ’yan sanda, Alhaji Ibrahim Kumasi da tsohon Shugaban Kotun daukaka kara Mai shari’a Mamamn Nasir da sauran manyan mutane daga ciki da wajen Jihar Kano.
Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana marigayin a matsayin dan kishin kasa, wanda kasancewarsa dan sarauta bai sa shi ya zama mai girman kai ko nuna son kai ba.