Shugaba Buhari yana samun sauki – Osinbajo

A ranar Talatar da ta gabata ne Muqaddashin Shugaban Qasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a birnin Landon, a daidai lokacin da ya kwashe fi ye da wata biyu yana jinya a can: Acikin wani rahoto da BBC ta ruwaito, ta bayyana cewa Shugaba Buhari ne ya buqaci da muqaddashin shugaban […]

Shugaba Buhari yana samun sauki – Osinbajo

A ranar Talatar da ta gabata ne Muqaddashin Shugaban Qasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a birnin Landon, a daidai lokacin da ya kwashe fi ye da wata biyu yana jinya a can:

Acikin wani rahoto da BBC ta ruwaito, ta bayyana cewa Shugaba Buhari ne ya buqaci da muqaddashin shugaban qasar ya je can wurinsa domin su tattauna kan wasu batutuwan da suka shafi makomar qasar. Haka kuma wannan shi ne karo na farko da mutanen biyu suka gana tun bayan da shugaban ya fice daga qasar saboda jinya.


Haka zalika kuma jim kadan bayan dawowar muqaddashin shugaban qasar ya bayyanawa manema labarai a fadar gwamnatin qasa a ranar Laraba gabannin a fara taron majalisar zartarwa cewa nan ba da jimawa ba Shugaba Buhari zai dawo gida Najeriya. Ya kuma qara da cewa Shugaba Buharin ya na samun sauqi sosai da sosai, don haka ya ce yana sa ran dawowarsa anan kusa. Sai dai kuma muqaddashin bai yi wani qarin bayani kan yadda tattaunawar ta su ta kasance da shugaba Buhari ba.


Koda yake ya yi qarin haske akan matakin rashin lafiyar shugaba Buharin, amma rahotanni sun bayyana cewa shugabannin biyu sun shafe sama da sa’a guda suna tattaunawar sirri a tsakaninsu, wacce ita ce ganawar su ta farko tun bayan tafiyarsa jinyar, sai dai ya zanta da manema labarai gab da shiga fara taron majalisar zartarwar, Ga yadda gajeriyar tattaunawar da muqadashin yay i da manema labaran fadar gwamnatin kamar haka: Inda y ace “Da farko kamar yadda ku ka sani, na je ne in duba lafiyarsa domin in san yadda yake ji. Kuma daman ina magana da shi ta waya kusan kullum, sai na ga ya dace in je in gan shi kuma in ga irin halin da yake ciki tare da ba shi labarin abubuwan da ke aukuwa a gida. Saboda haka, mun tattauna da kyau kan abubuwa da dama kuma yana cike da annashuwa. Yana samun sauki sosai.”


Ya ya jikin shugaban qasar a halin yanzu?
“E, kamar yadda na ce yana cikin annashuwa, yana samun sauqi sosai. Kuma mun yi tattaunawa ta tsawon lokaci. Mun shafe fiye da sa’a guda muna tattaunawa, kuma yana nan kamar yadda aka san shi da raharsa. Yana samun sauki sosai.”


To yaushe zai dawo?
“Ina ganin a nan gaba kadan. Nan ba da jimawa ba. Ina ganin ya kamata mu tsammanci dawowarsa. Kamar yadda na fada yana samun sauqi sosai.”


Kun tattauna kan batun sakataren gwamnatin tarayyar da shugaban hukumar leken asiri?
“Batutuwa da dama ne. Ba zan iya bayayya batutuwan da muka tattauna ba dalla-dalla.”

Amma kun tattauna batun rantsar da ministoci biyu?
“A’a. Ba mu tattauna batun rantsar da su ba.”

Shin muna tsammanin shugaban qasa zai dawo nan da kwanaki 90?
“A’a. Wa’adi ba abu ne mai kyau ba, amman kamar yadda na faxa yana samun sauqi sosai. Muna tsammanin zuwansa nan ba da jimawa ba, fiye da yadda ku ke tsammani.” Kamar yadda tattaunawar ta bayyana.