Shugaba Buhari zai ziyarci Maiduguri a yau
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a yau Laraba zai ziyarci Maiduguri babban birnin jihar Borno. Shugaban zai ziyarci jihar ne da nufin karawa dakarun sojojin kasar kwarin gwiwa akan yakar ‘yan Boko Haram da suke yi a yankin Arewa maso Gabas. Majiyarmu ta gano cewa, duk an kammala shirye-shirye na ziyarar Shugaban kasar yau Laraba, kamar […]
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a yau Laraba zai ziyarci Maiduguri babban birnin jihar Borno. Shugaban zai ziyarci jihar ne da nufin karawa dakarun sojojin kasar kwarin gwiwa akan yakar ‘yan Boko Haram da suke yi a yankin Arewa maso Gabas.
Majiyarmu ta gano cewa, duk an kammala shirye-shirye na ziyarar Shugaban kasar yau Laraba, kamar yadda mai taimaka wa shugaban kasar a harkar sabbin kafafen yada labarai Bashir Ahmed ya sanar a shafinsa na Twitter.