Shugaba Faye ya rusa Majalisar Dokokin Senegal
Rinjiyen ‘yan hamayya a majalisar ya sa yana shan wahala wajen aiwatar da “sauye-sauye masu ma’ana.
Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya rusa majalisar dokokin ƙasar da ke ƙarkashin jagorancin ’yan adawa.
Lamarin na zuwa ne a matsayin wani yunkuri na kawo ƙarshen rashin jituwar da ke tsakanin majalisar da ɓangaren zartarwa.
- Sojoji sun kashe ubangidan Bello Turji a Zamfara
- Shigowar ’yan bindigar ƙasashen waje ta gigita Sakkwato
A wani jawabi da ya yi wa ‘yan ƙasar ranar Alhami, Faye ya ce za a gudanar da zaɓen gaggawa a ranar 17 ga watan Nuwamba na bana.
Ya ce “dogaro da ikon da sashi na 87 na Kundin Tsarin Mulki ya ba ni, kuma bayan tuntuɓar Majalisar Tsarin Mulki a kan ranar da ta dace, da tuntuɓar Firayiminista da Shugaban Majalisar Dokoki, na rushe Majalisar Dokoki ta ƙasa.”
Ya ce rinjiyen da ‘yan hamayya ke da shi a majalisar ya sa yana shan wahala wajen aiwatar da “sauye-sauye masu ma’ana” da ya yi alkawari a lokacin yaƙin neman zaɓe.
Ya roƙi masu kaɗa ƙuri’a da su zaɓi ’yan jam’iyyarsa ta Patriots of Senegal for Work, Ethics and Fraternity (PASTEF).
Faye wanda ya lashe zaɓen ƙasar da aka gudanar a watan Maris na wannan shekarar, tare da faraministansa Ousmane Sonko, sun yi wa ’yan ƙasar alkawarin kawo sauyi mai ma’ana.
To sai dai gwamnatinsu na fuskantar koma baya wajen aiwatar da manufofinta, sakamon rashin rinjayen da su ke da shi a zauren majalisar.
Gwamnatin Faye dai na zargin gwamnatin magabacinsa ta Macky Sall, da kunbiya-kunbiya game da yadda gwamnatinsa ta kashe ƙudi.
Ya ce nan ba da jimawa ba za su wallafa rahoton binciken da suka gudanar game da yadda gwamnatin baya ta kashe ƙuɗaɗe, bayan da kotun ƙasar ta amince da shi.