Shugaba Jonathan A Kan Sikeli

daya daga cikin bayanan da Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya yi a watan Agustan 2012, ya nuna cewa Nijeriya ta bunkasa a cikin kankanin lokaci. Wannan bayanin dai ya janyo cece-kucen dimbin jama’a daga sassan kasar nan ganin yadda gwamnatin da ke ci gaba da shan suka daga al’ummar duniya ta samu yabo bisa […]

Shugaba Jonathan A Kan Sikeli
Shugaba Jonathan A Kan Sikeli

daya daga cikin bayanan da Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya yi a watan Agustan 2012, ya nuna cewa Nijeriya ta bunkasa a cikin kankanin lokaci. Wannan bayanin dai ya janyo cece-kucen dimbin jama’a daga sassan kasar nan ganin yadda gwamnatin da ke ci gaba da shan suka daga al’ummar duniya ta samu yabo bisa kwazo. Wannan bayani dai babu abin da ya haifar in ban da kara fusata al’umma.

Abin tambaya a nan shi ne, shin da ma kasar nan ingantattun hanyoyi ne da shi Jonathan ya shigo ya lalata? Ko kuwa dai zuwansa ne ya lalata tsayayyen lantarkin da ake da shi a can baya? Ko kuma dai shi ne ya haifar da fari gami da ambaliyar da suka lalata gonaki? A bisa la’akari da wadannan tambayoyi ne ya sa a wani lokaci Shugaba Jonathan ya yi wani jawabin mayar da martani inda aka ji shi ya ce, “A bar masu magana kowa ya ci gaba da fadin albarkacin bakinsa, amma a kwana da sanin cewa lokaci zai bayyana kansa”.
Bisa lura da bayanan Jonathan, za a fahimci cewa sun raja’a ne a kan harkokin da suka shafi bunkasa saka jari domin ci gaban kasa gami da al’umma, wanda hakan kuwa na bukatar lokaci kafin a soma cin moriyarsu. Saboda ko shakka babu cewa irin wannan ci gaba kan kama ne a hankali amma ba a cikin yini guda ba. Haka nan cewa, kasashen duniya da dama sun nuna kwadayinsu na shigowa su zuba jarinsu wanda hakan zai taimaka ga cimma kudirin da Jonthan ke da shi ga kasar nan. Sai dai wani abin lura a nan shi ne, anya kokarin Jonathan wajen cimma kudirorin da ya sanya gaba abin kwatantawa ne kuwa da na sauran kasashen duniya? Ko kuwa dai an yi gudun-ya-da-kane an baro shi baya?
Akwai bukatar kwazo matuka domin cimma inganta rayuwar kowace al’umma. Idan kuwa aka dubi Nijeriya a karkashin jogorancin Jonathan, za a ga cewa akwai burbushin himma wajen gudanar da ayyukan ci gaban kasa, sai dai matsalar ita ce ‘yan kasa ba su gamsu da ayyukan da suke gani ba sannan ita gwamnati ba ta kai matuka ba wajen wayar da kan al’ummarta ba dangane da ayyukanta.
Alal misali, gwamnati ta taka rawar gani wajen daidaita manyan hanyoyin kasar nan. Wasu hanyoyin an kammala gyaransu, an samar da wasu sabbi sannan aiki na nan na ci gaba da gudana wajen gyaran wasunsu. Kyakkyawan misali a nan shi ne, idan aka yi la’akari da hanyar Enugu zuwa Port Harcourt; hanyar Katsina zuwa Daura; sai ta Kano zuwa Maiduguri; haka ma Gombe zuwa Numan da dai sauransu. Sannan ga gyara babbar gadar nan ta Second Niger Bridge da ta yi gami da farfado da sufurin jirgin kasa bayan shekaru da dama da durkushewar fannin tare da bunkasa sufurin kan ruwa wanda hakan zai taimaka gaya wajen karfafa tattalin arzikin kasar nan. Amma ya zuwa yanzu dai bayanai sun nuna cewa layin doko da ke yammcin kasar nan wanda ya kama daga Legas zuwa Kano kuma mai nisan kilomita 1124, ya kammalu. Ta bangaren gabacin kasar kuwa, wato daga PortHarcourt zuwa Maiduguri, ana gab da kammala shi, haka ma layin da ya dauka daga Abuja zuwa Kaduna.
Bayanan sun kara da nuna cewa an samu karin kayayyakin da akan shigo da su ta ruwa daga tan milyan 2.9 a shekarar 2011 zuwa sama da tan milyan 5 a 2013 sakamakon bunkasa fannin sufurin ruwa da aka yi.
A fannin sufurin jiragen sama ma gwamnatin Jonathan ta tabuka. Domin kuwa ta yi shiga-da-fita wajen daukaka fannin duk da kalubalen da ya fuskanta. Inda ta yi nasarar yi wa wasu mnyan filayen sauka da tashin jirgin sama kwaskwarima a sassan kasar nan tare da daukaka darajar wasu kanan filayen, kana ta samar da ingantattun kayayyakin aiki baya ga kwadaita wa hamshakan ‘yan kasuwa na gida da ketare shigowa domin zuba jari a fannin.
Bugu da kari, gwamnatin Jonathan ta yi nasarar sassauta lamurra a kan iyakar kasa wajen shigowa da kayayyakin amfani. Inda ta tsaftatce fannin sarai ga barin duk wasu matsaloli da kan haifar wa fannin cikas. Da ta tabo fannin gona, gwamnatin ta yi hobbasa tare da aiwatar da ababen da suka dace wajen inganta fannin. Kama daga gyara wa gurbatattun ma’aikatan fannin zama, samar da takin zamani, samar da hanyoyin tafiyar da harkokin noma na zamani, samar da ingantattun kayayyakin noma, tallafa wa manoma da da sauransu masu yawan gaske domin bunkasa noman rani da na damina don kyautata rayuwar al’ummar kasa baki daya.
Har wa yau, domin daidaita wannan fanni mai muhimmanci ya sa gwamnatin ta saka jari mai yawa a fannin ta yadda ya zuwa shekara ta 2015, kasar nan za ta yi karfin samar da abincin da ya kai tan milyan 20 wanda ta hakan sai ya kasance Nijeriya ba za ta yi fama da matsalar karancin abinci ba tare da rage yawan kudaden da akan salwantar wajen shigowa da wasu kayayyakin abinci kasar nan. Kimanin manoma sama da milyan 10 suka samu rijista a shirin nan na ‘e-wallet’ da gwamnatin ta kirkiro domin tallafa wa harkar noma da su kansu manoman a duk fadin kasa inda tuni manoma milyan 6.5 suka samu nasarar cin gajiyar shirin ta hanyar samar musu da ingantattun kayayyakin aikin gona a kan farashi mai rahusa albarkacin wannan shiri dai gwamnati samu ragowar barnata kudi da magudi da akan samu musamman a bangaren rabon takin zamani. Kuma dimbin kudaden da akan kashe wajen shigo kayayyakin abinci kasar nan ya ragu da kimanin naira tiriliyan 2.38 a 2011, sannan tiriliyan 1.5 a shekarar 2013 sakamakon jajircewar da gwamnatin ta yi wajen bunkasa fannin.
Dadin-dadawa, kyakkyawar manufar da Jonathan ke da ita ga kasar nan ya sa bai yi kasa a gwiwa ba wajen bunkasa fannin masana’antu. Misali, gwamnatin ta maida hankali sosai wajen sarra shinkafa, sukari, inganta masaka, sarrafa siminti da sauransu, wanda sakamakon hakan a yau, Nijeriya tana daya daga jerin kasashen da ke samar da siminti don amfanin sauran kasashen duniya. An samu ci gaba wajen samar da siminti sabanin yadda lamarin yake a can baya. A shekarun baya kamar 2002, Nijeriya tana samar da siminti ne kimanin metric tonnes milyan biyu, yayin da take samar da metric tonnes milyan 28.5, wanda hakan ke nuni da babbar alamar nasara da aka samu a fanni masana’antu. Haka nan, an bai wa jihohin kasar nan da dama damar zuba jarinsu a wannan fanni don ci gabansu da ma kasa baki daya.
Kuma hasashe ya nuna cewa mai yiwuwa a samu karin adadin simintin da Nijeriya za ta rika samarwa ya kai metric tonnes milyan 39 ya zuwa shekara ta 2015. Yanayin bunkasar wannan fannin ya kwadaita wa wasu ‘yan kasuwa zuba jarin mukudan kudade a fannin sarrafa takin zamani. Alal misali, kamfanin Dorama ya saka jarin dalar Amurka bilyan 1.2 a katafariyar masana’antar takin nan da aka kashe dala milyan 250 wajen kafa ta a jihar Ogun da sauransu.
Bayanin nasarorin gwamnatin Jonathan ba zai cika ba muddin ba a ambaci fannin lantarki ba. Saboda gwamnatin ta zuba jari mai yawan gaske a wannan fannin domin daidaita lamurran lantarkin kasar nan. Tare da bai wa ‘yan kasuwa masu zaman kansu damar shigowa fannin don ci gaba da bunkasa shi yadda ya kamata. Duk da dai ya zuwa wannan lokaci gwamnatin ba ta cimma kudirinta na samar da lantarki a kowane lokaci babu kiftawa ba, amma ana sa ran nan ba da dadewa ba komai zai daidaita.

Balarabe ya rubuto daga Gwamnaja, Kano

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya