Shugaba Jonathan: Amincewa da zabe, jaruntaka ce ko tsoro?

Shugaba Goodluck Jonathan ya amince da sakamakon zabe, inda ya kira Janar Buhari ya taya shi murna. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan abu da ya yi, jaruntaka ce ko kuwa ya yi ne saboda tsoro? Wakilanmu sun tattauna da mutane kuma ga abin da suka ce: Ya yi haka don kare kansa […]

Shugaba Jonathan: Amincewa da zabe, jaruntaka ce ko tsoro?
Shugaba Jonathan: Amincewa da zabe, jaruntaka ce ko tsoro?

Shugaba Goodluck Jonathan ya amince da sakamakon zabe, inda ya kira Janar Buhari ya taya shi murna. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan abu da ya yi, jaruntaka ce ko kuwa ya yi ne saboda tsoro? Wakilanmu sun tattauna da mutane kuma ga abin da suka ce:

Ya yi haka don kare kansa ne – Malam Musa

A.A. Masagala, a Benin

Malam Musa Mayobelwa: “Ni a matsayina na cikaakken dan Najeriya, abin da na fahimta shi ne, Goodluck Ebele Jonathan ba ya yi wannan don ya amince da shan kayi da nufin alheri ga kasar nan ba, a’a ya yi ne domin ya kare kansa daga irin barna da lalata da gwamnatinsu ta PDP ta tafka, na kashe rayuka da wawashe dukiyar kasa da suka ci gaba da aikatawa ido a rufe. Akalla cikin shekaru shida da ya yi yana a kan kujerar mulki, inda ya yi wa al’ummar Najeriya jagoranci na bakin duhu. ”Don haka za a tabbatar da ce wa ya rigaya ya karaya har da mukarrabansa kuma ya tsorata gaba daya, domin ya gane duk dabarunsa sun kure, shi da kansa ya tabbatar ba ya da wani katabus ko dabara ko hanyar tsira a wannan lokaci.”

Abin da ya yi saboda tsoro ne – Muntari Nepa

Ahmad Kabir, a Katsina

Alhaji Muntari Nepa: “Jonathan tsoro ya ji saboda kada Buhari ya bincike shi a kan abubuwan da ya yi wa Najeriya, wadanda ba su kirguwa sai dai a bayar da misali. Kamar satar kudin kasa, halatta cin hanci da rashawa, rashin iya aiki, uwa uba kisan jama’ar da ba a san manufar abin ba. Ga kuma sayar da kadarorin talakawan Najeriya da ya yi. Saboda tunanin irin abin da ka iya biyowa baya a kan faduwar da ya gani, shi ya sa ya ji tsoro.”

Dola ce ta sa Jonatha ya mika wuya
– Abubakar dandada

Hamza Aliyu, a Bauchi

Malam Abubakar dandada: “Idan za a iya tunawa, tun kafin a gudanar da babban zaben kowa ya sa hannu tsakanin Shugaba Jonathan da Janar Muhammadu Buhari, cewa duk wanda ya yi nasara zai amince da sakamakon zaben saboda haka abin da Jonathan ya yi ba jarunta ba ce dole ce ta sa ya taya sabon shugaban kasa murna.
“Babu abin da Jonathan ya yi wanda za a jinjina masa kamar yadda wasu ke fada ta kafofin watsa labarai. barnar da ya yi a Najeriya ta fi alherin da ya yi. Sama da shekaru shida ana kashe mutane a jihohin Arewa maso gabas.”

Bai nuna jaruntaka ba – Baba Ali

A.A. Masagala, a Benin

Baba Ali Usman: “Ban yarda da cewa wai Goodluck Jonathan ya nuna halin dattaku ko jarunta ba a cikin wannan ihu bayan hari, domin ya san irin muguntar da ya aikata, wanda ko da an ce an yafe masa wasu ba za a iya a yafe masa wasu ba daga nan har lahira. Don haka ku tuna irin kisan kiyashi da aka ci gaba da yi a kasar nan a cikin wannan bakin mulknisa da wulakantar da dokokin kasa. Da ya tabbatar wannan karon ta bare masa da sauran jami’ansa gaba daya, wannan ya sa yake wannan kamun kafa da nufin za a kyale shi da barnarsa ta shekaru shida da ya yi yana sheke ayarsa tare da gasa wa mutanen wasu bangaren tsakuwa a tafi, ba tare da ko ya yi wani tunani ba.

Tsoro ne ba bajinta ba – Hajiya Hurera

Ahmad Kabir, a Katsina

Hajiya Hurera Tashar NARTO: “Gaskiya Jonathan tsorata ya yi ba bajinta ba. Dalilina shi ne, ya ga canjin da jama’a ke nema ya taho babu makawa Allah Ya kawo shi. Sannan kuma ya ga gaskiya ta fito fili babu wata hanyar boye ta. Yana kuma tsoron idon duniya saboda an zura masa ido a kan zaben. Tsoron kada Majalisar dinkin Duniya ko dai ta tuhume shi koma ta kama shi baki daya a kan irin yadda ya jefa Najeriya da al’ummarta ta wajen rashin tsaro, ga yawaitar asarar rayuka da dukiyoyi wadanda an rasa gane abin da shi da gwamnatinsa suke nufi a kan wannan. Akwai abubuwa da yawa da ya lura da su suka sa ya ji tsoron.”

Shugaba Jonathan jarunta ya nuna
– Ibrahim Hassan

Hamza Aliyu, a Bauchi

Malam Ibrahim Hassan Jahun: “Ya kamata shugabannin nahiyar Afirika su yi koyi da Shugaba Jonathan, domin tun da aka dawo mulkin dimokuradiyya a 1999 ba a taba samun wanda ya fadi a zabe kuma ya amince da sakamakon zaben ba sai Jonathan. Saboda haka a fahimta ta, abin da ya yi ba tsoro ba ne. Kuma lokaci ya yi da ya kamata shugabanni su fahimci cewa duk lokacin da aka fito takara akwai wanda zai yi nasara, akwai wanda kuma zai fadi warwas. Abin da mutum ya yi na alheri shi zai girba a ranar gobe kiyama.”