Shugaba Jonathan ba ya kaunar al’ummar Jihar Filato – Nuhu Gagara

Mista Nuhu Gagara daya ne daga cikin tsofaffin kwamishinonin Gwamnan Jihar Filato Mista Jonah Jang bakwai da suka fice daga Jam’iyyar PDP zuwa koma babbar jam’iyyar adawa ta APC, a tattaunawarsa da wakilinmu, ya zargi Shugaban kasa Goodluck Jonathan da nuna rashin kauna ga al’ummar Jihar Filato. Ya zarge shi da daure wa Gwamna Jang […]

Shugaba Jonathan ba ya kaunar al’ummar Jihar Filato – Nuhu Gagara
Shugaba Jonathan ba ya kaunar al’ummar Jihar Filato – Nuhu Gagara

Mista Nuhu Gagara daya ne daga cikin tsofaffin kwamishinonin Gwamnan Jihar Filato Mista Jonah Jang bakwai da suka fice daga Jam’iyyar PDP zuwa koma babbar jam’iyyar adawa ta APC, a tattaunawarsa da wakilinmu, ya zargi Shugaban kasa Goodluck Jonathan da nuna rashin kauna ga al’ummar Jihar Filato. Ya zarge shi da daure wa Gwamna Jang gindi ya sake dora dan kabilarsa ta Berom a matsayin dan takarar Gwamna na Jam’iyyar PDP, tare da watsar da sauran kabilun jihar. Har ila yau ya ce a yanzu babu Jam’iyyar PDP a jihar saboda duk manyan ’yan siyasar jihar sun fice daga cikinta tare da magoya bayansu, sun koma Jam’iyyar APC saboda rashin adalcin da aka yi musu:

Aminiya: Wadanne dalilai ne suka sanya kuka fice daga Jam’iyyar PDP kuka koma Jam’iyyar APC?
Nuhu Gagara: Akwai dalilai da dama da suka sanya muka fice daga PDP zuwa APC. Da farko ina son mutane su gane cewa mu da mu aka kafa Jam’iyyar PDP, bayan haka mun yi ruwa mun yi tsaki wajen kafa gwamnatin PDP a Jihar Filato a shekarar 2007. Kuma mun ci gaba da yi wa wannan jam’iyya aiki a jihar. Amma a shekara biyu da suka wuce sai muka gano cewa rashin gaskiya da yaudara da mugunta da danniya sun shiga cikin wannan jam’iyya a jihar nan da Najeriya baki daya. A nan Filato kowa ya san irin abubuwan da suke faruwa. Mun kafa gwamnati tsakani da Allah, muka ce za a yi wa jama’a aiki kowa ya ci moriyar gwamnati, amma sai aka wayigari gwamnati ta zama ta kabila daya wato kabilar Berom.
Idan kai ba dan kabilar Berom ba ne ba wanda zai saurare ka a gwamnatin Filato, kudin talakawa na jihar da ake turowa daga tarayya ana yin ayyuka da su ne kawai a yankin kabilar Berom. Bayan haka da aka wayigari ana son a samu wadanda za su tsaya takarar Gwamnan Jihar a Jam’iyyar PDP a bana, sai Gwamnan Jang ya nace cewa dole sai dan kabilarsa ta Berom ne zai tsaya. Kuma da ya tashi daukowa sai ya kara take kowa ya dauko dan dan uwansa ya ba shi wannan takara a Jam’iyyar PDP. Mun yi ta kuka da baki da rubuce-rubuce a kan wannan al’amari, mun je Abuja mun kai kukanmu ga Shugaban kasa da sakatariyar Jam’iyyar PDP ta kasa, amma ba mu samu biyan bukata ba. Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu ya karbi kukanmu ya yi gyara, amma daga baya Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kira shugabannin PDP na Jihar Filato ya ce su bar duk wani gyara a Jam’iyyar PDP reshen jihar a bar wa kabilar Berom. Wannan ya nuna mana cewa Shugaban kasa ba ya kaunar al’ummar jihar su kusan mutum miliyan hudu, sai mutanen da b asu kai miliyan daya ba da suke bugun kirgin wai su ne suke da Jihar Filato. Shi ne muka ce wannan cin mutunci ya isa haka, siyasa ra’ayi ce tunda yake ba a bukatarmu a PDP bari mu koma Jam’iyyar APC.
Bayan haka wani babban dalili kuma shi ne ganin yadda aka yi gaskiya ba tare da wani magudi ba a zaben fadda-gwani na dan takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar APC. Domin a cikin wadanda suka yi takarar Janar Buhari shi ne wanda ba ya da komai, amma wakilan da suka yi zaben suka ki karbar miliyoyin kudin da aka yi masu tayi suka zabi Janar Buhari, kuma a cikin ’yan takarar babu wanda ya daga hankalinsa, wannan ya nuna mana cewa ana yin adalci a cikin Jam’iyyar APC. A yanzu idon kowa ya bude a Najeriya, an gane cewa babu wanda zai ceto kasar nan ya magance cin hanci da rashawa da yaki da rashin zaman lafiya da kawo ci gaba sai Janar Buhari. Wadannan ne dalilan da suka sanya muka dawo Jam’iyyar APC don mu taimaka mu ga Janar Buhari ya zama Shugaban kasar nan, kuma mu ga dan takarar Gwamnan Jihar Filato karkashin Jam’iyyar APC, Simon Lalong ya lashe zaben Gwamnan Jihar Filato, kuma in Allah Ya yarda za mu samu nasara.
Aminiya: Ana cewa wannan jiha ta Filato jiha ce ta PDP, ba ka ganin wannan zai kawo maku cikas ga wannan buri naku?
Nuhu Gagara: A kwanakin baya babu shakka Jihar Filato jiha ce ta PDP, amma a yanzu al’ummar jihar sun kaurace mata. Domin a maganar da muke yi da kai wadanda suka yi takarar Gwamnan Jihar Filato a karkashin Jam’iyyar PDP su 16 sun bar ta sun dawo APC. Tsohuwar Mataimakiyar Gwamnan Jihar Misis
Pauline Tallen ta bar PDP ta dawo APC mu tsofaffin kwamishinonin Gwamna Jang mu bakwai da masu ba shi shawara su biyu duk mun dawo APC. A cikin gwamnatin Jang ina tabbatar maka akwai mutane da dama da muke aiki da su ga wannan jam’iyya ta APC, don haka ina PDP take a Jihar Filato?
Aminiya: To, me za ka ce kan dage zabe da Hukumar INEC ta yi?
Nuhu Gagara: Wannan dage zabe da aka yi babban abin kunya ne ga Shugaban kasa da al’ummar Najeriya baki daya. Wai a ce Shugaban kasa yana kan mulki amma kuma yana jin tsoron a yi zabe, wannan babban abin kunya ne da ba a taba yin irin sa ba a Najeriya. Ni ban ga laifin Hukumar Zabe ba kan dage zaben, domin shugaban hukumar Farfesa Attahiru Jega ya ce ba zai yarda a yi amfani da shi a yi magudi ba, don haka ya ce zai tsaya tsakani da Allah duk wanda ya ci zabe za a ba shi, Shugaban kasa bai ji dadin wannan mataki da Farfesa Jega ya ce zai dauka ba. Shugaban kasa na son ya yi amfani da shugaba da Hukumar Zabe ne domin ya yi masa murdiya. Amma da ya ga ba za ta yiwu ba, kuma ya ga cewa za a yi zabe, shi ya sa ya nace sai dai a dage zaben. Don haka ya zagaya ya sa shugabannin sojoji su ce saboda tashe-tashen hankulan da ake yi a jihohin Barno da Yobe da Adamawa ba za a iya yin zabe ba, don haka a kara mako shida. Wannan magana ko yaro karami ba zai yarda da ita ba, domin Shugaban kasa ya yi shekara shida yana fama da matsalar Boko Haram bai iya magance ta ba, a cikin mako shida ne zai magance matsalar? Kuma maganar cewa ana tashe-tashen hankula a jihohin don haka aka dage zabe, shin Shugaban kasa bai je yakin neman zabe a jihohi ba? Ya je jihohin ya yi yakin neman zabe, babu wanda ya rasa ransa, sai a lokacin zabe ne za a karkashe mutane? A kasashen Afirka, Najeriya ce ta daya a bangaren soja, amma abin mamaki kasar Chadi wadda ba ta kai Jihar Filato ba, sojojinta ne suka shigo Najeriya suke ta korar ’yan Boko Haram. Ya kamata Shugaba Jonathan da shugabannin sojojin Najeriya su sauka daga kan mukamansu saboda wannan abin kunya da ake tafkawa a Najeriya.
Aminiya: To, kana ganin wannan mataki da aka dauka zai iya ba PDP nasara idan aka zo yin zaben?
Nuhu Gagara: A tunaninsu suna ganin idan suka yi haka PDP za ta samu nasara, amma Allah a cikin ikonSa, mutanen Najeriya da yake sun gaji da wannan gwamnati ta mugunta da sharri da kashe kasa, ba za su zabe ta ba. Kuma ko sun ki ko sun so, zaben nan sai an yi shi.
Aminiya: Mene ne sakonka ga al’ummar Najeriya kan wadannan abubuwa da suke faruwa?
Nuhu Gagara: Sakona ga al’ummar Najeriya shi ne mu yi hakuri da wannan cuta da aka yi mana na dage zabe, kuma mu yi amfani da wannan lokaci kowa ya tabbatar ya karbi katin zabensa, domin mu fito mu kawar da wannan gwamnati a lokacin zabe mai zuwa.