Shugaba Jonathan na shakkun satar ’yan matan Chibok

Yau kwanaki 25, daidai da ‘Yan Kungiyar JamaatulAhlisSunnah Lidaawati Wal JIhad, suka kutsa kai cikin makarantar `yan mata ta garin Chibok, kudancin jihar Barno, suka sace `yan mata sama da 200, a lokacin da suke rubuta jarrabar kammala karatunsu na Sakandare ta Hukumar shirya jarrabawa ta Afirka ta yamma wato WAEC da ake ciki a […]

Shugaba Jonathan na shakkun satar ’yan matan Chibok
Shugaba Jonathan na shakkun satar ’yan matan Chibok

Yau kwanaki 25, daidai da ‘Yan Kungiyar JamaatulAhlisSunnah Lidaawati Wal JIhad, suka kutsa kai cikin makarantar `yan mata ta garin Chibok, kudancin jihar Barno, suka sace `yan mata sama da 200, a lokacin da suke rubuta jarrabar kammala karatunsu na Sakandare ta Hukumar shirya jarrabawa ta Afirka ta yamma wato WAEC da ake ciki a duk fadin kasashen ta Afirka ta yamma. Zuwa yanzu Shugaban kungiyar, AbubakarShekau ya tabbatar wa Duniya cewa su suka yi, kuma za su cigaba.   Tun waccan lokacin zuwa yanzu saboda rashin tsari na kasar nan, Mahukuntar makarantar da jami`an tsaro da ita kanta gwamnatin tarayya sun kasa tantance hakikanin yawan `yan mata da aka sace, da kuma inda suke, bare a iya ceto su. Da farko Mahukuntan makarantar da ita kanta Gwamnatin JiharBarno, sun ce dalibai 129, aka sace daga bisani kuma bayan iyayen yara sun yi ta kururuwar batan `ya`yan nasu Mahukuntar jihar suka ce dalibai 236, ne, sai kuma ga shi kwatsam a wani taron hadin guiwa da suka gudanar a Maiduguri a cikin makon jiya manyan jami`an tsaron kasa biyu daga jihar, Kwamishinan’yan sanda, Alhaji Lawan Tanko da takwaransa na jami`an tsaron  farin kaya (SSS), Alhaji Ahmed Abdullahi sun  sanar da duniya cewa dalibai 276, aka sace zuwa wancan makon, kuma dalibai 53 kadai suka samu kubutowa, saura 223, har yanzu ba a san inda suke ba. Sun kara da cewa sun samu wadannan alkalumma ne daga irin shaidar  da suka samu daga iyayen daliban, kuma adadin na iya karuwa muddin wasu iyayen suka bijiro da kwakkwarar shaida.
 Sace `yan matan ke da wuya Gwamnan Jihar Barno, Alhaji Kassim Shettima da sauram makarrabansa suka yi ta kai komo tsakanin  Chibok da Maiduguri da Abuja duk a yunkurin ganin ya ya za a iya ceto daliban. A gefe daya kamar yadda ya saba Shugaban kasa, Dokta Goodluck Jonathan ya yi ta babatun da ya saba yi na cewa za a gano wadanda suka aikata ta`asar da aniyar ganin an hukunta su a duk inda suka shiga, a duk lokacin da aka samu annobar hare-hare irin na `yan kungiyar Jama`atu Ahlis Sunnah Lid Da`awati Wal jihad da ake wa lkabin BokoHaram.
A gefe daya, bayan wasu iyayen daliban, sun yi yunkurin shiga dajin Sambisa, dajin da ake zargin an kai ’yan matan, da zummar ceto su, amma suka guji kar a yi biyu babu, don haka a dolen su suka dawo. Wannan ta sa kungiyoyin mata hade da iyayen `yan mata suka fara zanga-zangar neman  mahukuntan da suke da alhakin ceto ’ya’yansu, su ceto su, zanga-zangar da suka fara daga garin na Chibok zuwa Maiduguri babban birnin jihar, sannan suka fadadata zuwa Abuja fadar gwamnatin tarayya da manyan birane irinsu Kaduna da Legas da Kano da Badun.
  Duk da wannan danbarwa da jimami da dimauta da kasa take ciki akan sace `yan matan, babu wani kwakkwaran sabon yunkuri, ko wata magana mai gamsarwa a zaman karfafa guiwa daga Shugaba Jonathan ko makarrabansa na ceto daliban, sai ma nuna shakkun an sace `yan mata da aka rika ji daga bakin shugaban kasar da wasu makarbansa. Tsohuwar Ministar kula da zirga-zigar jiragen sama Misis Kema Chekwu, kuma shugabar mata ta jam`iyyar PDP ta kasa baki daya, ita ta fara nuna wanna shakku, a lokacin da take jawabi a wajen wani taron addu`a da ta hada da mata Musulmi da Kirista a Hedkwtar jam’iyyarsu ta kasa da ke Abuja a Larabar makon da ya gabata.
 Tambayoyin da ta rika yi sun hada da yaya aka yi lamarin ya faru? Wane ne ya gani? Wane ne bai gani ba? Wane ne ya aikata wannan danyen aiki? A fadarta, batun sace `yan matan wata makarkashiya ce aka shirya wa gwamnatinsu ta PDP.
A gefe daya ita ma uwargidan shugaban kasa Dame Patience Jonathan a wani taro da ta kira da ya kunshi matan gwamnonin jihohi da mata Ministoci da mata `yan Majalisun Dokoki na kasa da matar Sanata da ta dan Majalisar Wakilai ta tarayya daga yankin da kungiyoyin mata da matar Shugaban karamar Hukumar  Chibok, sannan kuma ta kafa wani Kwamiti da ke karkashin jagorancin Gwamnan Jihar ta Barno, kwamitin da ta dora wa alhakin  gano `yan matan, wadda dama a cikin jawabinta na bude ta fadi karara cewar alhakin gano `yan mata ya rataya ne kacokan akan Gwamnan Jihar Barno, kasancewar sa babban jami`in tsaron jihar.
 A daidai lokacin da uwargidan shugaban kasar take nata taron, a gefe daya  shi ma Shugaba Jonathan a lokacin ya yi taro da manyan dakarun tsaron kasar nan akan batun `yan matan da harin kunar bakin wake na baya-bayan nan da aka sake kaiwa kusa da tashar mota ta Nyanya, inda kusan mutane 20, suka mutu. A wajen wancan taron Shugaba Jonathan ya kafa wani Kwamiti da ke karkashin jagoranci Birgediya Janar Ibrahim A Sabo (mai ritaya) da ya dora wa ayyukan ya iya tantance me ya kawo lokacin da makarantun kwana suke rufe a dukkan fadin jihar, amma ta Chibok tana bude? Kwamitin ya kuma tattauna da iyayen yaran da aka sacen da shugabannin al`umma na yankin da jami`an tsaron jihar da aniyar ya iya tantance `yan matan da aka sace da yawansu da yawan wadanda suka samu kubutowa? Kwamitin ya kuma wayar da kan iyaye da sauran masu ruwa da tsaki a yankin na Chibok akan irin muhammancisn da ke akwai na su taimaka wa jami`an tsaro wajen  kubutar da `yan matan.
Mai karatu daga bayanan da na dan iya kawowa a sama, bisaga danbarwar da ake ciki ta gano wadancan `yan mata da na kawo karshen rashin tsaron da ake fama da shi a Arewa, za ka iya fahimtar cewa Shugaba Jonathan da gwamantinsa ko dai sun rude ko kuma sun gaza kwata-kwata cikin tafiyar da mulkin kasar nan, ko kuma ya bari abubuwa suna ta tabarbarewa ne da nufin ya cimma nasa bukatun na shekarar 2015.
Da irin wannan hali ka iya cewa takardar da Gwamnan Jihar Adamawa Murtala Nyako ya rubata wa takwarorinsa na jihohin Arewa a kwanakin baya, inda yake zargin Shugaba Jonatahan da shirya kisan kare dangi akan `yan Arewacin kasar nan don ya cimma burinsa na siyasa akwai kanshin gaskiya a cikinsa. Allah mun tuba ka ba mu ikon canja shugabannin da ba su da niyyar ganin kyautatuwar rayuwa da zaman lafiyarmu amin summa amin.