Shugaba Jonathan ne butulu ba Lamido ko Obasanjo ba – Musari

dan takarar Shugaban karamar Hukumar Guri da ke Jihar Jigawa Alhaji Usman Abdulllahi Musari ya ce Shugaba Jonathan ne ya yi butulci ga Cif Obasanjo da Gwamna Sule Lamido da kuma Jam’iyyar PDP inda yake kokarin wargaza ta saboda bukatar kashin kansa.Alhaji Usman Musari ya bayyana haka ne lokacin da yake mayar da martani ga […]

Shugaba Jonathan ne butulu ba Lamido ko Obasanjo ba – Musari
Shugaba Jonathan ne butulu ba Lamido ko Obasanjo ba – Musari

dan takarar Shugaban karamar Hukumar Guri da ke Jihar Jigawa Alhaji Usman Abdulllahi Musari ya ce Shugaba Jonathan ne ya yi butulci ga Cif Obasanjo da Gwamna Sule Lamido da kuma Jam’iyyar PDP inda yake kokarin wargaza ta saboda bukatar kashin kansa.
Alhaji Usman Musari ya bayyana haka ne lokacin da yake mayar da martani ga tsohon dan Majalisar Tarayya daga Jihar Jigawa Alhaji Abba Anas Adamu wanda ya ce Gwamna Lamido da Obasanjo sun yi wa Shugaba Jonathan butulci a tat taunawarsa da Aminiya a makon jiya.
Ya kara da cewa duk Najeriya babu butulu kamar Shugaba Jonathan saboda yadda ya yi wa al’ummar Najeriya kuma ya yi wa Obasanjo da Gwamna Lamido butulci duk da irin taimakon da suka yi masa a baya har ya zama Shugaban kasa.
Alhaj Usman Musari ya ce Obasanjo ne ya sa Shugaba Jonathan ya zama wani abu a cikin Jam’iyyar PDP, kuma aka yi masa alfamar zama Gwamnan jiharsa. “Kada Abba Anas ya manta Obasanjo ne ya sa Alhaji Umaru Musa ’Yar’aduwa ya dauki Jonathan a matsayyin mataimakinsa a zaben 2007, kuma bayan rasuwarsa Obasanjo ya sake shiga rigar arziki aka ba shi shugabancin kasar nan,” inji Musari.
Amma saboda butulci da ganain karfinsa ya kawo yake tunanin ba ya da abokin gaba da ya fi Obasanjo. “Idan ana maganar Gwamna Lamido, gudunmawar da ya ba Jonathan shi da su Murtala Nyako da sauransu, a kasar nan babu sunan batanci da ba a kira Gwamna Lamido da shi ba har arne da fasto an ce masa saboda Jonathan, kuma jin dadin haka ne ya sa har alkawari ya yi cewa in ya hau karagar mulkin kasar nan zai gina wa Jihar Jigawa filin jirgin sama na zamani tare da gyara hanyoyin
Gwamnatin Tarayya da sauran alkawura da dama amma ko alkawari daya bai cika wa Lamido ba.
Ya ce saboda Gwamna Lamido ya bukaci Shugaba Jonathan kan ya hakura da batun sake tsayawa
takarar shugabancin kasar nan a 2015 ne ake yi masa sharri da bata shi, ake wa iyalansa kalaman batanci da turo jami’in Hukumar EFCC don cin zarafinsa.
Musari ya ce da Abba Anas yana da kishin Arewa kuma ya san me yake yi a siyasa ba zai sake komawa bayan Jonathan ba mutumin da ya yi masa kazafi ya bata shi a baya ya raba shi da majalisa kuma ya nemi ya gurgunta masa harkokin siyasarsa.