Shugaba Jonathan ne ko mutanen boye ke juya kasar nan?
A Shekarar 1959 ne wani marubuci dan kasar Amukra a birnin New York, mai suna Richard Thomas Condon ya rubuta wani littafi mai suna THE MANCHURIAN CANDIDATE. A kuma shekarar na ya fitar da wani littafin mai suna THE OLDEST CONFESSOIN. Wadannan littafai guda biyu sun sa marubucin ya yi suna nan da wadannan littafai […]
A Shekarar 1959 ne wani marubuci dan kasar Amukra a birnin New York, mai suna Richard Thomas Condon ya rubuta wani littafi mai suna THE MANCHURIAN CANDIDATE. A kuma shekarar na ya fitar da wani littafin mai suna THE OLDEST CONFESSOIN. Wadannan littafai guda biyu sun sa marubucin ya yi suna nan da wadannan littafai guda biyu. Nan da nan sunansa ya shiga cikin shararrun marubutan duniya. Sauran littafan da ya rubuta guda 24 suka samu karbuwa.
Tarihi ya nuna an haifi Ricahard a shekarar 1915, ya yi rayuwarsa a tsakanin NEW York da Hollywood. A shekarar 1962 wani kamfanin shirya fina-finai a Hollywood ya mayar da wannan littafin nasa mai suna THE MANCHURIAN CANDIDITE fim. Kuma fim din ya samu gagarumar karbuwa. an yi canje -canje daga abin da marubucin ya rubuta, amma a kalla an isar da sakon da yake son isarwa.
A shekarar 2004, wani kamfani ya sake ma wancan film na Manchurian candidate fasali ya sake gabatar da shi, inda a sabon film din ya dauko wasu abubuwan da ke cikin littafin da kuma wadanda ke cikin film din 1962 ya yi nasa , wanda ya fito a shekarar 2004. An kuma kashe Dala miliyan 80 wajen shirya film din. Nan da nan film din ya maida kudinsa har da gagarumar riba.
A littafin Manchurian candidate labari ne. na wani dan takarar shugaban kasa, wanda wata kungiyar sirri ta horas, ta kuma wanke ma kwakwalwa lamarin bai tsaya a haka ba, ta kuma yi masa tiyata a kwala ta makala masa wata naura.
Duk lokacin da suke bukata za su yi abin da suke so bisa tarbiyyar da suka ba shi. Suka sa masa wazirai, wadanda suka kewaye shi suna tabbatar da cewa ya yi daidai abin da suke bukata.
A labarin sun tabbatar da sun dora shi bisa wannan shugabancin, amma yana da majalisa guda biyu, wadda aka zaba ta kasa, wadda jama’a ke gani. Sai kuma ta boye, wadda waccan kungiyar suka nada masa. Kome za a zartar a waccan majalisar sai wannan majalisar ta kungiyar sirri ta tabbatar kafin a yi aiki da shi, wadannan ’yan majalisarsa na kungiyar sirri . su ne farko da zai fara gani a kullum. kuma su ne zai gani ya tattauna da su kafin karshen rata. Daga su baya kara ganin wasu.
A labarin na littafin idan da shugaban kasa zai yi tawaye ya ki yi yi ma waziransa na kungiyar sirri tawaye.idan suka kai kararsa wajen Babbansu. to daga inda yake akwai naurar da zai danna sai kwakwalwarsa ta juye a rika sarrafa shi yadda ake so. Da babban ya danna wannan na’ura sai kawai shugaba ya zama kama “zombie” sai yadda aka yi da shi. Don haka sai shugaban ya zama wani irin mumu ga shi nan, a matsayin shi ne shugaba, amma bashi ke mulki ba.
Marubucin ya littafin Manchurian candidate ya rubuta labarin sa ne. da duk salon da fasalin da kuma inda yace abin ya faru da kasar Amurka. A labarin ya ce kasar ta Amurka ta rikice. Aka rasa inda aka sanya gaba majalisar wakilai da ta sanatoci suka rasa gane kan shugaban.
kasa ta yamu tse aka rasa ina ne wajen kamawa, ba wanda yasan me ake ciki sai abin da aka kaga an aiwatar kai tsaye.a littafin hukumomin tsaro na sirri na wanda hakkinsu ne kariya da tabbatuwar kasar abin ya ishe su. suka fara shiri na daukar mataki wanda suka fara aiki, ba dare, ba rana, kuma suka yi nasarar gano, inda matsalar take su kai maganinta.
A littafin na Manchurian candidate jaridu.na amurka kullum suna buga wani labari na wata tabargaza da shugaban kasa yayi , don ha ka ana kwana da tashin jin me kuma ya aikata? Daga cikin labaran da aka buga wanda ya jawo duk kasar Amurka ta rika gun guni shine yadda a jawabinsa ya da wata karamar hukuma ya sanya a wata jaha.daga wata jahar.kamar yadda muka ji ance shugabanmu na Najeriya yayi, Inda rahotanni suka ruwaito yana tambayar shin a ina Garin Goza yake a jahar barno ne ko adamawa
A littafin akwai .shugaban wata hukuma a kasar ta amurka da yayi wani laifi.yan majalisa suka fara bincike.shi kuma yayi sa a.yana auren diyar daya daga cikin yan kungiyar sirrin dake juya shugaban kasa .da wannan daurin gindi da yake dashi.ya sanya. Majalisa ta nuna ma shugaban kasa illar a kyale mutumin nan yaci gaba da rike hukumar amma ya kasa komai. Suka kafa wa hukumar takunkumi, amma ya ki cire shi. Kusan kwatankwacin abin da ya faru a kasar nan, inda shugabar fataucin hannayen jari ta kasa, ta yi laifi yau shekaru hudu ke nan majalisar ba ta ba ta ko kwabo a kasafin kudi ba. Shugaban kasar mu ya ki cire ta, duk da kuwa an ce zaman ta a matsayin ya haifar wa da kasar nan asara ta sama da Dala miliyan 20; an yi asarar Dala miliyan 20, amma ga shi ana neman rancen Dala miliyan daya a sa yi makamai, an nemi majalisa ta bada iko, kuma ta bayar.
A littafin an ce kullum shugaban sai ya rika magana akan ya manta da abin da ya fada jiya, ko kuma dazun. An ce kullum maganarsa na karo da dazun da kuma ta jiya, da ta shekaran jiya. Wannan yasa har wasu jaridu suka buga wani sharhi mai suna tukfa da warwara, tare da tunakuli a zantukan shugaban kasa.
Irin wannan an sha rubuta su a jaridun kasar mu akan shugaban kasa. Wasu mujjallu ma har babban labari suka yi akan lamarin. A littafin an kawo yadda rai ba a ba shi muhimmaci a kasar Amurka lokacin wannan shugaba na cikin littafin.
Suka ce ana kashe-kashe ko’ina, har ma akwai lokacin da wani hadari ya hada da wasu ’yan wata kasa makwabciyar Amurka, wato Mekzico, amma shugaban sai bayan kwana biyar ya nuna jajantawarsa duk kuwa da yadda lamarin ke da sammatsi.
Lamari ya kwabe komai ya rikice a kasar Amurka ta labarin wannan littafin. Idan zai yi magana sai ya caba, kamar yadda shugaban kasar mu ya je Bauchi ya ce, “duk jihohin PDP ana zaman lafiya, jihar APC kawai ake tashin hankali.” Da kuma yadda ya je Sakkwato, ya ce “da nan aka haife shi ya tashi da almajiri zai rayu.” Wata jarida har kalubale ta sanya na shugaban ya fito ba tare da wani shiri ba, ya tsaya gaban jama’a inda aka yi hira da shi a kasar Amurka. kalubalen da aka yi ta maimaitawa, amma shugaban ya kasa kare kansa.
Bayan da na karanta littafin a tsanake, na kuma kalli fim din da aka yi na 1962, da kuma na 2004, da wanda wata tasha a Indiya ta dauka ta gyara, ta mayar da shi Indiyanci, sai na fara tunanin anya ba Manchurian Candidate” ake yi a Najeriya ba? Shin wai Jonatan ke mulkin mu ko ko Ebele ne? Duk wanda ya yi nazarin me ke faruwa a kasar nan sai ya rude, zai zama kamar wata karin magana da ke cikin littafin, wadda ke cewa.’’’ Ilmi yana zama haske ne da wayar da kai, amma a kasa ta yawan abin da ka sani girman rudewarka.’’ Marubucin ya rubuta wani littafin kamar yadda na kawo da farko, wanda shi ma zubin sa ya yi kama da abin da ke faruwa a Najeriya. Littafin an yi masa taken The Oldest Confession, wanda film din da aka tashi yi, sai aka yi masa taken: THE HAPPY THIEbES.,” ma’ana FARIN CIKIN bARAYI..