Shugaba Jonathan ya haramta kungiyar Boko Haram da ta Ansaru

A ranar talatar da ta gabata ne Shugaba Goodluck Jonathan ya haramta kungiyar Boko Haram, ya kuma yi alla-wadai da ayyukan kungiyar.Tun a watannin baya ne ake ta kokarin samar da dokar haramta ayyukan ta’addanci wanda ake kira ‘Terrorism (prebention) (Proscription order). A yanzu dai an samar da dokar kuma ta shafi kungiyoyin da suka […]

Shugaba Jonathan ya haramta kungiyar Boko Haram da ta Ansaru
Shugaba Jonathan ya haramta kungiyar Boko Haram da ta Ansaru

A ranar talatar da ta gabata ne Shugaba Goodluck Jonathan ya haramta kungiyar Boko Haram, ya kuma yi alla-wadai da ayyukan kungiyar.
Tun a watannin baya ne ake ta kokarin samar da dokar haramta ayyukan ta’addanci wanda ake kira ‘Terrorism (prebention) (Proscription order). A yanzu dai an samar da dokar kuma ta shafi kungiyoyin da suka hada da Jama’atu Ahlis Sunnah Lid Da’awati Lid Jihad (Boko Haram) da kuma Jama’atu Ansarul Muslimina Fi Baladis Sudan (Ansaru).
Dokar ta bayyana, duk wanda aka kama da laifin ta’addanci ko kuma da hannu wurin taimaka wa ta’addanci ko ya hada kai da kungiyoyin ta’addanci za a daure shi a gidan yari har tsawon shekara 20.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Reuben Abati ne ya bayyana hakan a Abuja.
Ya ce: “Sashi na 5 (1) na dokar haramta ta’addanci ta bayyana za a yanke wa duk mutumin da aka samu da laifi ko hannu wurin aikata ta’addanci daurin shekara 20 a gidan yari.
“Sakin layi na daya (1) na dokar ya ce: (a) Duk wanda ya yi kalamai ta hanyar intanet ko na’urorin sadarwa- kamar rediyo ko jaridu ko mujallu ko kuma ya yada bayanan da za su haifar da ta’addanci.
“(b) Ya karba ko bayar taimakon muggan makamai masu guba ko masu linzami ko bama-bamai, ko bayar da horo ko zirga-zirga da yin takardun bogi ko shaidar bogi ga dan ta’adda ko kungiyar ‘yan ta’adda.
(c) Bayar ko karbar bayanai ko taimako ko kuma amsa gayyatar dan ta’adda ko kuma kungiyar ta’addanci.
Har ilau yau Shugaba Jonathan ya goyi bayan ladan Naira biliyan 1.1 da kasar Amurka ta dora a kan Shugaban kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah Lid Da’awati Wal Jihad wadda aka fi sani da Boko Haram, Abubakar Shekau.
Shugaban kasar ya ce wannan ladan da Amurka ta sanya ya tabbatar ta’addanci ya shafi duniya gaba daya ba wai wani yanki ba.
Ya ce: “Wannan ladan da Amurka ta dora kan ’yan ta’adda abin a yaba ne, za mu yi maraba da duk kasashen da za su taimaka mana wurin yaki da ’yan ta’adda da kuma masu rurar wutar ta’addanci. Hakan ya nuna ta’addanci kalubale ne ga duniya wanda kuma ke bukatar gudunmuwar duniya don a kawo karshensa.”  
Idan ba za a manta ba dai a ranar Litinin da ta gabata ne Amurka ta sanya ladan Dala miliyan 23 kan shugabannin kungiyoyin ’yan ta’adda a kasashen Afrika.
Amurka ta sanya ladan Naira biliyan 1.1 (Dala miliyan 7) a kan Shekau, sannan ta sanya Dala miliyan 5 kan manyan shugabannin Al-kaeda Mokhtar Belmokhtar da Yahya Abou Al-Hamma.